ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Muna Kan Ƙoƙarin Rage Farashin Takin Zamani — Ƙungiyar FEPSAN

by Abubakar Abba
9 months ago
Farashin

Shugaban kungiyar masu sarrafa takin zamani da rabar da shi na kasa (FEPSAN), Injiya Olusegun Falade ya bayyana cewa; kungiyar na kan koarin ganin an rage tsadar farashinsa.

Ya sanar da haka ne a Jihar Kaduna, a taron wayar da kai na tababatar da sahihancin takin zamanin na samarin NPK da cibiyar kasa da bunkasa samar da takin zamni (IFDC), ta dauki nauyi na 2025.

  • Farashin Kayan Abinci Na Cigaba Da Sauka A Jihohin Arewa Maso Gabas
  • Matatar Dangote Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa Naira 699

“Na kasance daga cikin wadanda suke kan gaba wajen ganin shirin ya dore, hakan zai bayar da dama domin ganin kowa ya samu alkaluman da ake bukata a bangaren samar da bayanai, musamman a fannin masana’antar sarrafa takin zamani,” a cewar shugaban.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa, ba wai taki ba ne kadai farashinsa ya tashi, hatta kusan komai farashinsa ya karu a Nijeriya, musamman a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban ya ci gaba da cewa, manyan dalilai biyu ne kusan suka sanya farashin ya tashi a kasar nan, musamman sabbin sauye-sauyen da gwamnatin tarayya ta kirkiro da kuma rashin samun tabbacin farashin kaya a kasuwannin kasar, wanda hakan ya jawo mutane suke daukar matakan da ba su dace ba.

LABARAI MASU NASABA

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ya yi nuni da cewa, sakamakon yakin da ake ci gaba da gabzawa a tsakanin Kasahen Russia da Ukraine, tun a 2022, hakan ya haifar da tashin farashinsa a daukacin fadin duniya.

Shugaban ya kara da cewa, hatta farashin sinadarin hada takin na MOP, wato Potash ya tashi, haka farashin sinadarin DAP, wato Diammonium Phosphate shi ma ya tashin zuwa sama da dala 900 kan tan ko sama da dala 1,000, a wasu lokutan, inda a yanzu ya kai dala 700 kowane tan daya.

Ya sanar da cewa, idan mutane sun koka kan tashin farashinsa, mu ma muna jaddada musu cewa, mun saye shi da tsada, wanda kuma idan farashin dala ya tashi a duniya, hakan na shafar farashin naira.

Sai dai, ya bayyana cewa; kungiyar na ci gaba da gudanar da rabon takin, ba tare da an kara masa wani farashi mai tsada ba, inda yayi nuni da cewa, ba don samar da wannan dauki ba, da yanzu farashinsa ya karu.

A cewarsa, mun tattauna da kwamitin da ke samar da daidaiton farashinsa tare da hadaka da hukumar zuba jari ta kasa (NSIA) da kuma taimakawar sashen kudi MOFI, na ma’aikatar kudi ta tarayya, wadanda ya sanar da cewa; suna kan kokarinsu wajen ganin an samar da sauki kan farashinsa.

Ko da yake, ba a lokaci guda za a wanzar da hakan ba, amma muna sa ran a 2026, farashin zai ragu.

Ya kara da cewa, ana kuma ci gaba da samun raguwar farashin kayan da ake hada takin zamanin da su.

Ya ci gada cewa, gwamnatin tarayya na ci gaba da kokarin daidaita farashin kayan da ake sarrafa takin zamani, wanda hakan zai bayar da damar gudanar da gasa a kasuwar da ake sayar da shi, wanda kuma har yanzu, ana ci gaba da yin wannan tsari.

Ya sanar da cewa, har zuwa yanzu, muna ci gaba da tabbatar da cewa; farashin nasa ya ragu.

Kan batun baragurbin da ke gurbata takin, shugaban ya sanar da cewa; kasancewarmu a kan gaba wajen sarrafa takin a kasar nan, gurbata takin na daga cikin matsalar da ke shafar mu.

A cewarsa, irin wadannan bata gari na kwaikwayar buhunhunan da muke zuba taki tare da sayar wa jama’a.

“Idan mun gano, muna kama irin wadannan bata gari ko kuma mu kore su daga kasuwar, a yanzu muna yin amfani da kimiyyar fasahar zamani wajen yakar masu gurbata takin, in ji shugaban.

Farashin
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Tun Ina Karama Marigayi Tumbuleke Ke Sa Ni Dariya —Hannatu Musawa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    NPA Ta Bayyana Cewa Kirkiro Da Sabuwar Hukumar NPERA Ba Zai Zame Mata Tarnaki Ba
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Yadda Bikin Girke-girke Ya Karfafa Alaka Tsakanin Musulmai Da Kiristoci A Kaduna
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari Kan Wasu Dalilan Da Ke Haddasa Sabanin Abotakar Jarumi Ko Jaruma A Kannywood

MASU ALAKA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Farashin

Matakan Dauda Lawal Na Samar Da Tsaro A Zamfara: An Bankado Ayyukan Masu Zagon Ƙasa

LABARAI MASU NASABA

Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.