ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matakan Dauda Lawal Na Samar Da Tsaro A Zamfara: An Bankado Ayyukan Masu Zagon Ƙasa

by Bello Hamza
7 months ago
Dauda

Adaidai lokacin da matsalar tsaro ke kara rinchabewa a wasu sassan kaasar nan, wasu jihohi na matukar kokarin su na ganin an shawo kan matsalar a yankunan su. Masu lura da al’amurran yau da kullum sun tabbatar da cewa, an samu nasarori masu yawa a kokarin da Gwamnan Jihar Zamfara yake yi domin ganin jihar ta kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga, kuma daga dukkan alamu ana samu nasara. Matakan Gwamna Dauda Lawal suna haifar da da mai ido.

Sai dai kuma abin takaici a daidai wannan lokacin shi ne yadda wasu marasa kishin kasa wadanda basu yi wa al’umma Jihar Zamfara da Nijeriya fatan alhairi suke amfani da wasu kungiyoyin boyi wajen yada labarun kanzon kurege don yin zagon kasa ga kokarin da Gwamna Lawal ke yi.

  • Tinubu Na Ɗaukar Ƙwararan Matakai Don Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – Shettima
  • Binciken CGTN: Ya Kamata A Dauki Matakai Don Kula Da Yanayin Duniya

An gano cewa zargin da ake yadawa cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi afuwa tare da sakin ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci ba shi da tushe kwata-kwata, bayan cikakken bincike da jaridar PremiumTimes ta gudanar kan batun da ya tayar da kura a kafafen yada labarai.

ADVERTISEMENT

A ranar 28 ga Nuwamban 2025, wata kungiya mai suna ‘Human Rights Watchdog in Africa’ (HRWA) ta fitar da wata sanarwa da aka ce daraktanta, Samson Adamu, ne ya sanya wa hannu, inda ta bukaci Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya ayyana dokar ta-baci a Zamfara, bisa zargin cewa Gwamna Lawal ya yi afuwa tare da sakin ’yan bindiga 69 ta sirri, karkashin wani shiri da ta kira ‘Religious Amnesty.’

Sai dai binciken da aka gudanar ya nuna cewa ba a samu asalin wannan sanarwa daga kowace sahihiyar majiya ba. Kokarin samun kungiyar HRWA da shugabanta Samson Adamu ya ci tura, domin babu wani ofishinta, lambar waya, shafin yanar gizo ko kuma rajistarta da aka samu a Hukumar Kula da Kamfanoni da Kungiyoyi ta Kasa. Haka nan, babu wani sahihin bayani ko sahihiyar shaidar da ke nuna wanzuwar kungiyar ko wannan mutum kafin karshen Nuwamban 2025.

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

Bincike ya kuma tabbatar da cewa abin da ya faru a zahiri shi ne Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Zamfara ta taimaka wajen biyan basussukan fursunonin da aka yanke wa hukunci a shari’o’in farar hula, wanda hakan ya taimaka wajen sakin mutum 909 daga 2024 zuwa 2025. Wannan bayani ya fito ne daga bakin Sakataren Zartarwa na hukumar, Habib Muhammad Balarabe, a wani taron karshen shekara da aka gudanar a Gusau.

A cewarsa, a 2024 kadai, an biya basussukan fursunoni 473, yayin da a 2025 aka kashe Naira miliyan 67.2 domin biyan basussukan mutum 436, wanda adadin gaba daya ya kai 909 cikin shekaru biyu. Hukumar ta kuma bayar da tallafin jari ga mata 200 kanana ‘yan kasuwa da Naira dubu 50-50, tare da bai wa wasu mata 100 kayan fara sana’a bayan kammala horarwar kiwon kaji na makonni uku.

Jami’an hukumar Zakka sun bayyana cewa ayyukansu na jinkai ba su taba shafar ‘yan bindiga da aka yanke wa hukunci kan laifukan ta’addanci ba. Wani jami’i da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, abin dariya ne ace gwamnan da ya sha bayyana a fili cewa ba ya sulhu da ‘yan bindiga shi ne zai koma ya sake su bayan an yanke musu hukunci.

Haka kuma, an tabbatar da cewa Gwamna Lawal bai taba sauya matsayarsa kan batun ‘yan bindiga ba. A ranar 29 ga Oktoban 2025, yayin da yake jawabi a gaban daliban kwas din tsaro a ‘National Institute for Security Studies’ da ke Abuja, gwamnan ya bayyana adawarsa ga yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga da ake yi a wasu jihohin Arewa maso Yamma, yana mai cewa sulhu ba tare da kwace makamai ba hanya ce ta jinkirta tashin hankali.

Kakakin gwamnan, Suleman Bala Idris, ya musanta zargin baki daya, yana mai cewa labarin kirkirarre ne da wasu ‘yan siyasa da ke cikin matsin lamba suka tsara domin bata sunan gwamnatin Zamfara.

Ya jaddada cewa babu wani lokaci da Gwamna Lawal ya yi afuwa ko ya saki kowane dan bindiga daga kurkuku.

Bayan kammala bincike mai zurfi, an tabbatar da cewa kungiyar HRWA da shugaban nata kamar fatalwa ne, kuma zargin da aka yi cewa Gwamna Lawal ya saki ‘yan bindiga karya ne tsagwaron gaske.

Dauda
Bello Hamza
+ postsBio
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Shugaban Miyetti Allah, Bodejo Ya Karyata Zargin Halatta Kudin Haram A Zaman Kotu
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Kafa Cibiyar NIPHID: NCDC Ta Yi Kuskuren Fahimtar Ƙudirin Dokar
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Ƙaddamar Da Muhimman Ayyukan Ci Gaba A Jihar Jigawa
  • Bello Hamza
    https://hausa.leadership.ng/author/bello-hamza/
    Ƙungiyar Kansilolin APC Ta Yi Barazanar Janye Goyon Bayanta Idan Ba A Daina Zargin Sanata Yari Ba

MASU ALAKA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Manyan Labarai

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga
Manyan Labarai

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026
Next Post
EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta’addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

EU Ta Koka Da Yadda Yaduwar Ta'addanci A Sahel Ke Barazana Ga Tsaron Turai

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026
Katsina: Kotu Ta Yanke Wa Hauwa’u Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Kan Taimaka Wa ’Yan Bindiga

Kotu Ta Tsare Shugaban Makaranta Da Malami Kan Zargin Lalata Da Ɗaliba Mai Shekara 6 A Gombe

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.