ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Naɗin Yari Daraktan Kamfen Ya Tsorata Kwankwaso – APC

by Abubakar Sulaiman
2 weeks ago

Wata ƙungiyar wayar da kan jama’a ta jam’iyyar APC a yankin Arewa maso Yamma, ta ce kalaman tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kan naɗin Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC, na nuna cewa naɗin ya tayar da hankalin ‘yan adawa.

A cikin wata sanarwa da Mai Gudanar da Ƙungiyar na Ƙasa, Comrade Jaafar Hassan, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce abin lura ne yadda daga cikin dukkan naɗe-naɗen da aka yi a tsarin yaƙin neman zaɓen APC, Kwankwaso ya zaɓi ya roƙi Yari da ya sake tunani kan karɓar muƙamin. Ta ce ba kasafai ‘yan siyasa ke shawartar abokan hamayyarsu su bar muƙamin da suke ganin ba shi da muhimmanci ba.

Ƙungiyar ta bayyana Yari a matsayin tsohon gwamna da yayi wa’adi biyu, kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya, Sanata mai ci kuma gogaggen ɗan siyasar da ya ƙware wajen tattara magoya baya. Ta ce gogewarsa da kuma alaƙar da ya gina a Arewacin Nijeriya, musamman Arewa maso Yamma, ne suka sa naɗinsa ya zama abin damuwa ga ‘yan adawa.

ADVERTISEMENT

Ta kuma soki Kwankwaso kan ƙoƙarin tambayar zaɓin siyasar Yari, tana mai cewa shi kansa yana dogaro da haɗin gwiwarsa da Peter Obi domin faɗaɗa tasirinsa a wajen sansanin siyasarsa na gargajiya.

Ƙungiyar ta ce Yari ba ya buƙatar wani ya ƙirƙira masa suna a siyasar ƙasa, domin tarihinsa da alaƙar da ya gina a siyasa sun isa su bayyana matsayinsa.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

Ƙungiyar ta ƙara cewa idan Yari ba shi da muhimmanci a siyasa, da Kwankwaso bai damu da naɗinsa ba har ya nemi ya janye. Ta bukaci Yari da ya yi watsi da abin da ta kira “shawarar abokan hamayya”, ya mai da hankali kan aikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabancin APC suka ɗora masa, tana mai cewa ta yi imanin zai iya jagorantar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar zuwa nasara.

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Next Post
Hukumar Kula Da Ci Gaban Kasa Da Gyare-gyare Ta Sin Ta Kebe Yuan Miliyan 50 Don Tallafa Wa Farfadowa Bayan Abkuwar Ibtila’o’i A Guangxi

Hukumar Kula Da Ci Gaban Kasa Da Gyare-gyare Ta Sin Ta Kebe Yuan Miliyan 50 Don Tallafa Wa Farfadowa Bayan Abkuwar Ibtila’o’i A Guangxi

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.