ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Na Ƙi Amincewa Da Tinubu A Matsayin Mataimakina Saboda Tikitin Muslim-Muslim – Atiku

by Sulaiman
3 weeks ago
Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana yadda ya ƙi amincewa da yunƙurin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na zama mataimakinsa, yana mai cewa ya yi hakan ne saboda yana adawa da tikitin Muslim-Muslim domin kare muradun ƙasar.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka yi da shi da harshen Hausa, wadda aka wallafa a shafin X, inda ya bayyana cewa wasu dattawan siyasa sun tuntube shi bayan ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa, domin sanar da shi cewa Tinubu na son zama mataimakinsa.

A cewarsa, Tinubu ya tura wasu dattawa biyar domin su tattauna batun da shi, ciki har da Tom Ikimi, Bisi Akande da wasu mutum uku.

ADVERTISEMENT

Atiku yace, “Ya ce zai mara mini baya wajen samun tikitin takara. Bayan na samu tikitin, sai ya tura dattawa biyar, daga cikinsu akwai Tom Ikimi, Bisi Akande da wasu uku. Sun gaya mini cewa Tinubu yana son ya zama mataimakina. Na gaya musu cewa, a matsayinsu na Kiristoci, ya kamata su fahimci cewa bai dace in zaɓi Musulmi ya zama mataimakina ba.

“Har na tambaye su dalilin da ya sa ba za su iya gaya masa hakan ba. Na gaya musu cewa ba zan iya amincewa da tikitin Muslim-Muslim ba, saboda hakan ba zai kasance cikin muradun ƙasarmu ba. Daga nan ya rabu da mu, ya mara wa marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua baya, Allah ya jiƙansa.”

LABARAI MASU NASABA

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

Atiku ya ce tun daga wannan lokaci suka rabu da Tinubu, kuma ba su sake kasancewa a sansanin siyasa guda ba har sai a shekarar 2014, lokacin da ya shiga yakin neman zaɓen marigayi Muhammadu Buhari.

Atiku
Sulaiman
+ postsBio
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki
  • Sulaiman
    Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna
  • Sulaiman
    Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba
  • Sulaiman
    Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

MASU ALAKA

Atiku
Labarai

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Atiku
Labarai

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato
Manyan Labarai

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
Next Post
An Yi Jana’izar Kone Gawar Tsohon Firaministan Kasar Sin Zhu Rongji A Birnin Beijing

An Yi Jana'izar Kone Gawar Tsohon Firaministan Kasar Sin Zhu Rongji A Birnin Beijing

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

Xi Ya Bukaci A Kara Azamar Dakile Aukuwar Muggan Hadurra Sakamakon Aukuwar Gobara A Wani Jirgin Ruwan Dakon Kayayyaki

September 10, 2026
Atiku

Jerin Bankuna 32 Da Aka Amince Su Sayar Da Hannun Jarin Matatar Dangote

September 10, 2026
Atiku

Uganda Za Ta Fara Fitar Da Man Fetur Zuwa Ƙasashen Waje

September 10, 2026
Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Kano, Katsina Da Filato

Mashaƙo: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Sun Kai 27 A Filato

September 10, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

Wane Ne Dan Shagamu: Su Wane Ne Suka Kashe Shi A Kano?

September 10, 2026
Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

Al’umma Sun Yaba Wa Sojoji Kan Yaƙar ’Yan Bindiga A Zamfara

September 10, 2026
Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

Ambaliyar Ruwa Ta Tafi Da Ɗalibai 2 A Abuja Da Abia

September 10, 2026
’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

’Yansanda Sun Kama Wadda Ta Yaɗa Labarin OPay Zai Daina Aiki A Nijeriya

September 10, 2026
2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

2027: ’Yansanda Sun Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa Kan Haifar Da Rikici A Sakkwato

September 10, 2026
Zabe: Gwamnatin Kano Ta Taƙaita Zirga-zirgar Mutane Da Ababen Hawa

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.