Yau Talata ne aka yi jana’izar kone gawar tsohon firaministan kasar Sin Zhu Rongji a birnin Bejing, fadar mulkin kasar Sin.A yau da safe, manyan shugabannin kasar Sin da suka hada da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da firaministan kasar na yanzu Li Qiang da sauran manyan shugabannin kasar, sun yi ban kwana da Zhu Rongji a kaburburan jama’a na Babaoshan.
A yayin da ake kidin nuna juyayi, wadannan shugabanni sun zo gaban gawar Zhu Rongji, inda suka yi shiru domin nuna alhini, sa’an nan, sun duka sau da uku a gaban gawar Zhu Rongji, daga bisani kuma, suka gaisa hannu da hannu da iyalan Zhu Rongji daya bayan daya. Kana, tsohon shugaban kasar Sin Hu Jintao ya mika furannin jana’iza domin nuna ta’aziyya.
Tsohon firaministan kasar Sin, Zhu Rongji, ya rasu sakamakon rashin lafiya yana da shekaru 98 a duniya.Zhu ya taba zama mamba a zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitocin koli na 14 da 15 na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS).
Wata sanarwa game da rasuwarsa da aka fitar, ta yaba wa Zhu a matsayin nagartaccen dan jam’iyyar JKS, kuma gogaggen dan gwagwarmayar gurguzu mai biyayya, kana fitaccen dan juyin-juya-halin ’yan kwadago kuma dan siyasa, sannan jagoran jam’iyya da kasa baki daya.
Bugu da kari, a yau Talata, kasar Sin ta saukar da tuta zuwa rabin sanda a filin Tian’anmen dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, domin nuna juyayin rasuwar tsohon firaministan na kasar Sin Zhu Rongji. (Mai Fassara: Maryam Yang)














