ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴan Majalisar Dokokin Ƙasa 54 Sun Rasa Tikitin Takara A Zaɓen Fidda Gwanin APC

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Majalisa

Aƙalla ƴan majalisar dokokin ƙasa 54 masu ci ne suka rasa tikitin sake neman zaɓe a majalisar dokoki ta ƙasa a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC.

Jam’iyyar APC ta gudanar da zaɓen fidda gwani na majalisar wakilai a ranar Asabar, 16 ga Mayu, yayin da na sanatoci ya gudana ranar Litinin, 18 ga Mayu, 2026.

Daga cikin waɗanda suka sha kaye akwai fitattun ƴan majalisa da suka kwashe shekaru masu yawa a majalisar dokoki ta ƙasa, yayin da wasu kuma manyan jami’ai ne a majalisar wakilai da majalisar dattawa.

ADVERTISEMENT

A majalisar wakilai, waɗanda suka rasa tikitin sun haɗa da Hon. Nicholas Mutu mai wakiltar mazaɓar Bomadi/Patani ta Jihar Delta; shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Farfesa Julius Ihonɓbere mai wakiltar mazaɓar Owan ta Jihar Edo; Ibrahim Isiaka mai wakiltar Ifo/Ewekoro a Jihar Ogun; da Mike Etaba mai wakiltar Obubra/Etung a Jihar Cross Riɓer.

Sauran sun haɗa da Ngozi Lawrence Okolie (Aniocha/Oshimili, Delta); Daɓid Zachariya (Igalamela/Idah, Kogi); Tijani Ahmed Ozigi (Okene/Ogori-Magongo, Kogi); Eseosa Iyawe (Oredo, Edo); Matthew Nwogu (Aboh Mbaise/Ngor Okpala, Imo); Miriam Onuoha (Okigwe North, Imo); da Chike Okafor (Okigwe South, Imo).

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

Waɗanda su ma suka rasa tikitinsu kuma ba za su dawo majalisar dokoki ta ƙasa ba sun haɗa da; Harrison Nwadike (Isu/Njaba/Nkwerre/Nwangele, Imo); Emeka Martins Chinedu (Ahiazu/Ezinihitte, Imo); Ismail Kayode (Ifelodun/Oyun/Offa, Kwara); Mansur Musa Jega (Jega/Gwandu/Aleiro, Kebbi); Muktar Muhammad (Kazaure/Roni/Gwiwa Yankwashi, Jigawa); da Ibrahim Usman Auyo (Hadejia/Auyo/Kafin Hausa, Jigawa).

Hakazalika, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Ringim/Taura ta Jihar Jigawa, Hon. Sa’adu Wada Taura, ya rasa tikitin tsayawa takara a zaɓen 2027 bayan da Yushau Muhammad ya samu tikitin ta hanyar maslaha.

Sauran da ba za su koma majalisar wakilai ba sun haɗa da Yusif Sa’idu Miga (Jahun/Miga, Jigawa); Dickson Tarkighir (Makurdi/Guma, Benuwe); Terseer Ugbor (Kwande/Ushongo, Benuwe); Sesoo Ikpagher (Ɓandeikya/Konshisha, Benuwe); Asema Achado (Gwer East/Gwer West, Benuwe); Sekaɓ Iortyom (Buruku, Benuwe); Daɓid Ogewu (Oju/Obi, Benuwe); Bassey Akiba (Odukpani/Calabar Municipality, Cross Riɓer); da Daniel Asama (Jos North/Bassa, Plateau).

A zaɓen fidda gwani mai zafi, Ɓincent Bulus (Langtang, Filato); John Dafaan (Ƙua’anpan/Shendam/Mikang, Plateau); Ajang Iliya (Jos South/Jos East, Plateau); Jeremiah Umaru (Wamba/Akwanga/Nasarawa Eggon); Ari Mohamed Abdul-Mumin (Nasarawa/Toto); Abiodun Akinlade (Ipokia/Yewa South, Ogun); da Tunji Akinosi (Ado-Odo/Ota, Ogun) su ma sun sha kaye.

Haka kuma, Femi Ogunbanwo (Odogbolu/Ijebu Ode/Ijebu North East, Ogun); Adesola Elegbeji (Remo, Ogun); da Jimi Odimayo (Okitipupa/Irele, Ondo) sababbin ƴan takara sun kayar da su a zaɓen fidda gwani.

Donatus Mathew, tsohon direban babur kasuwanci wanda ya lashe kujerar majalisar wakilai ta mazaɓar Kaura a Jihar Kaduna a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party a 2023 amma ya koma APC a Disambar 2024, ya rasa ƙoƙarinsa na komawa majalisar ta sabuwar jam’iyyarsa.

Haka kuma waɗanda aka kayar sun haɗa da Timilehin Adelegbe (Owo/Ose, Ondo); Bashiru Dawodu (Oshodi-Isolo, Lagos); Kafilat Ogbara (Kosofe, Lagos); da ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ekiti North II, Akinlayo Kolawole, wanda ya rasa tikitin ga tsohon ɗan majalisar tarayya, Ibrahim Olarewaju.

A majalisar dattawa kuwa, waɗanda suka sha kaye sun haɗa da Ned Nwoko (Delta North), wanda tsohon gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya kayar; Neda Imasuen; Jibrin Isah mai wakiltar Kogi East wanda aka fi sani da Echocho; Sanata Muhammad Danjuma Goje wanda ya wakilci Gombe Central har sau huɗu a jere; da Sanata Adeniyi Adegbonmire (Ondo Central).

Sauran sun haɗa da Sanata Olajide Ipinsagba (Ondo North); Sanata Gbenga Daniel (Ogun East); Sanata Diket Plang (Plateau Central); Sanata Lola Ashiru (Kwara South); Sanata Emmanuel Udende wanda ya rasa tikitin Benuwe North East ga tsohon gwamnan Jihar, Sanata Gabriel Suswam; Sanata Titus Zam (Benuwe North West); da Sanata Olubiyi Fadeyi (Osun Central).

Majalisa
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Sanata Sani Ya Nemi Tinubu Ya Saki Masu Zanga-zanga Da Ke Tsare

Bayan Shehu Sani Ya Ƙalubalanci Zailani, Rikicin APC Ya Ƙara Zafi A Kaduna

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.