ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Ɗan Wasan Man-United Baleba Zai Shafe Makonni Uku Yana Jinya

by Rabilu Sanusi Bena
1 week ago

Sabon ɗan wasan tsakiyar Manchester United, Carlos Baleba, zai iya shafe makonni biyu zuwa uku yana jinya sakamakon raunin da ya samu a idon sawunsa. Kocin ƙungiyar, Michael Carrick, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa raunin ba wani babban abu ba ne, amma zai hana Baleba fara buga wa United wasa nan take.

Baleba ya koma Old Trafford kan kuɗi har fam miliyan 70, a matsayin ɗaya daga cikin manyan sabbin ‘yan wasan da United ta ɗauka domin ƙarfafa tsakiyar fili. Shi ne ɗan wasa na uku a wannan matsayi da ƙungiyar ta ɗauka a kakar bana, bayan Andrey Santos da Youri Tielemans. Sai dai raunin da ya samu na nufin magoya bayan ƙungiyar za su iya jira har zuwa watan Oktoba kafin su gan shi cikin fili.

Carrick ya ce Baleba na fama da ƙaramar matsala a idon sawunsa, amma ana sa ran zai murmure cikin makonni biyu zuwa uku. “Yana fama da ɗan matsala a idon sawunsa, don haka watakila ya shafe makonni biyu zuwa uku. Ba matsala ba ce,” in ji Carrick yayin taron manema labarai gabanin wasan da Manchester United za ta yi da Ipswich Town ranar Lahadi.

ADVERTISEMENT

Carrick ya ci gaba da jagorantar United ne bayan ya taimaka wa ƙungiyar kammala gasar Premier League a matsayi na uku a kakar da ta gabata, lamarin da ya ba ta damar komawa gasar Zakarun Turai. Sai dai United ta fara kakar bana da rashin nasara, bayan da Hull City ta doke ta da ci 2-0 a makon da ya gabata, abin da ya ƙara matsa wa ƙungiyar lamba ta farfaɗo da sakamakonta.

Manchester United na fatan dawowar Baleba da sauran sabbin ‘yan wasan za ta taimaka wajen ƙarfafa ƙungiyar a tsakiyar fili da kuma dawo da ita kan hanyar samun sakamako mai kyau.

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

Rabilu Sanusi Bena
+ postsBio
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Za’a Dakatar Da Wasa A Farkon Minti 10 Na Kowane Wasa A Kasar Argentina Saboda Girmama Messi
  • Rabilu Sanusi Bena
    https://hausa.leadership.ng/author/rabilu-sanusi-bena/
    Chelsea Ta Kammala Ɗaukar Ahanor Kan Fam Miliyan 40

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana
Wasanni

Ƙungiyoyi 5 Da Ke Takarar Gwarzuwar Ƙungiya Ta Bana

September 8, 2026
Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain
Wasanni

Kofin Duniya: Yau Falconets Za Su Kece Raini Da Spain

September 7, 2026
Next Post
Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

Tsakanin Yanayin Sanyi Da Na Zafi Wanne Ya Fi Maka Dadi?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.