Jami’an Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) sun kama wani sabon ango mai shekara 25, mai suna Lovely Chukwulobelu, a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Akanu Ibiam da ke Enugu, bayan ya haɗiye ƙunshin hodar iblis guda 72 da nufin yin safararsu zuwa ƙasar Portugal.
Wanda ake zargin ya bayyana wa masu bincike cewa ya shiga safarar miyagun ƙwayoyin ne domin biyan basussukan da suka taru a kansa sakamakon bikin aurensa. Ya ƙara da cewa ya taɓa yin sana’ar ƙawata motoci a yankin Ojo da ke Jihar Legas kafin ya ƙaura zuwa Portugal a watan Mayun 2023, inda ya dawo Nijeriya a kwanan nan tare da yin aure a ranar 13 ga Satumba, 2026.
A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, an tare Chukwulobelu ne a filin jirgin a ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2026, yayin da yake ƙoƙarin shiga jirgin Ethiopian Airlines domin zuwa Portugal ta birnin Addis Ababa.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’an hukumar sun killace matashin tare da sanya shi a ƙarƙashin kulawa ta musamman bayan an gano ƙwayoyin a cikinsa, inda daga bisani ya fitar da dukkan ƙunshin hodar iblis ɗin guda 72 ta hanyar bayan-gida.
A ƙarshe, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da aikin a filin jirgin na Enugu da sauran sassan ƙasar, yana mai buƙatar su ci gaba da tsayin daka wajen daƙile safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin Nijeriya.














