ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Nijeriya Na Iya Samun Nasara A Fannin Sufuri Kamar Ƙasar Chana —Shettima

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago
Nijeriya

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da wani kamfanin ƙasar China mai suna New Power Technology (NPT) sun ƙulla wata muhimmiyar haɗin gwiwa domin farawa ƙera da haɗa kayan aikin motocin CNG da motocin lantarki (EƁ) a cikin Nijeriya.

Gwamnatin ta ce haɗin gwiwar, wanda gwamnatin China ke mara wa baya gaba ɗaya, zai mayar da hankali kan ƙira da haɗa injinan cika iskar CNG, tashoshin cika mai da kuma wuraren cajin motocin lantarki a cikin gida, a wani ɓangare na ƙoƙarin Nijeriya na ƙarfafa amfani da kayayyakin cikin gida, rage dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje da kuma bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta wajen sufuri.

Hakan ya fito ne bayan wata ganawa tsakanin tawagar kamfanin NPT ƙarƙashin jagorancin Liu Shihua da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a Abuja.

ADVERTISEMENT

Mataimakin shugaban ƙasar, wanda mataimakin shugaban ma’aikata na shugaban ƙasa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia ya wakilta, ya ce wannan mataki ya yi daidai da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na wajabta amfani da motocin CNG a dukkan hukumomin gwamnati, kuma hakan zai taimaka wajen magance matsalolin sufuri.

Sanata Shettima ya ce shirin horas da ƴan Nijeriya 100,000 aƙalla mutum 1,000 daga kowace jiha tare da ɗaukar nauyin mutum 100 zuwa ƙasar China domin samun horo, wani ɓangare ne na manufar haɗa kowa da kowa cikin tsarin “Renewed Hope Agenda” na shugaban ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

Ya bayyana cewa duk da cewa Nijeriya tana daga cikin manyan kasuwanni masu tasowa a duniya, inda matsakaicin shekarun jama’a ke kusan 21.4, yanayin kasuwarta ya yi kama da na China a shekarun 1980, wanda hakan ke nuna yiwuwar maimaita nasarar da China ta samu wajen amfani da motocin lantarki.

“Ana iya cimma sauyin sufuri mai tsafta da kare muhalli ta hanyar amfani da sabbin fasahohin muhalli na China. Inganta ƙwarewar cikin gida da horaswa su ne mabuɗin samun nasara da jawo hankalin masu zuba jari,” in ji shi.

Sanata Shettima ya kuma yaba wa gwamnatin China bisa tayin tallafin manufofi da kuɗi domin gina motocin lantarki da wuraren cajinsu. Ya ce ziyarce-ziyarcen da aka kai masana’antun China sun taimaka wajen samun rangwamen farashin motocin lantarki, tashoshin caji da sauran kayan aiki.

Ya yaba wa kamfanin NPT bisa ƙoƙarinsa wajen bunƙasa jarin ɗan’Adam na gwamnatin Tinubu ta hanyar “haɓaka kusan ayyukan injiniyan chips guda 10 cikin shekaru uku, tare da gina masana’antar chips ta lantarki, musamman ta hanyar horas da matasa, mata da masu rauni a al’umma.”

Tun da farko, shugaban tawagar NPT, Liu Shihua, ya shaida wa mataimakin shugaban ƙasar cewa manufarsu ita ce gina cikakken tsarin motocin lantarki, ciki har da sauya motocin man fetur zuwa lantarki, cibiyoyin musayar batir da kuma tsarin kula da ayyuka ta hanyar fasahar zamani.

Nijeriya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu
Manyan Labarai

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Next Post
Amirul Hajj Na Kano Ya Caccaki NAHCON Kan Halin Da Alhazai Suka Fuskanta A Saudiyya

Amirul Hajj Na Kano Ya Caccaki NAHCON Kan Halin Da Alhazai Suka Fuskanta A Saudiyya

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Yusuf Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Gano Waɗanda Suka Kashe Danshagamu

September 10, 2026
Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.