Shugaban rundunar tsaro ta NSCDC Farfesa Ahmad Abubakar Audi ya bada umarnin a jibge jami’an su mutum 10,210 na musamman domin ƙara ƙarfafa tsaro da kula wajen gudanar da zaɓen jihar Osun
Bayanin haka yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwa na jami’in hulɗa da jama’a na rundunar NSCDC na ƙasa Babanwale Afolabi ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Afolabi ya ce jibge jami’an ya fara ne daga ranar Litinin domin tabbatar da cewa masu zaɓe da jami’an zaɓe da masu sanya ido da ƴan jarida da sauran al’umma sun gudanar da zaɓen su ba tare da tashin hankali ko tsoro ba
A cewar sanarwar, jami’ai masu sanye da kaki da kuma farin kaya daga jihohin Oyo da Ondo da Ekiti da Ogun da Lagos da Kwara da Edo da Kogi da Delta da tare da birnin tarayya Abuja tuni an jibge su a jihar Osun.
Sanarwar ta cigaba da bayanin cewa a ɗauko jami’ai 1,000 daga kowane runduna 10 domin ƙarfafa tsaro a jihar baki ɗaya kuma za su yi aiki tare da sauran jami’an tsaro a lokacin zaɓen.
Afolabi ya ƙara da cewa jigbe jami’an na daga cikin tsarin inganta tsaro kafin da bayan an kammala zaɓe, ya hanyar bayar tsaro da yanayi mai kyau domin kowa ya gudanar da zaɓe na da cikin kwanciyar hankali.
Haka kuma shugaban rundunar na ƙara ya bada umarnin a ƙara jigbe wasu jami’an na musamman da za su tabbatar da komi yana tafiya yadda aka tsara da suka haɗa da mataimakin shugaba da sashen tattara bayanan sirri da sashen mata ba musanman da kuma sashen ko ta kwana tare da ɓangaren K9
Shugaban rundunar NSCDC ya yi alƙawarin yin aiki bisa doka ta hanyar girmama ƴancin kowa lokacin gudanar da zaɓen tare da tabbatarwa da al’umma an ba su tsaro yadda ya kamata
Sai dai kwamandan ya bayyana cewa ba zai lamunci duk wani jami’in tsaro da za a haɗa kai da shi ba wajen yi wa tsare-tsaren zaɓe karan tsaye ba, musamman ƴan bangar siyasa da ake amfani da su domin lalata tsarin gudanar da zaɓe, duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci kamar yadda yake a dokokin zaɓe.
Haka kuma ya yi kira ga ƴan siyasa da magoya baya da al’umma da su tsarawa kan su bin doka domin baiwa dimokuraɗiyya daman wanzuwa.
Ya ƙara da cewa jami’an su za su yi aiki kafaɗa-da kafaɗa da jami’an ƴan sanda ƙarƙashin wani tsari da hukumomin tsaro domin tabbatar da komi ya tafi yadda aka tsara a faɗin ƙananan hukumomi 30 na jihar Osun.
Farfesa Abubakar ya roƙi ruwa da tsaki da suka haɗa da ƴan siyasa da ƴan takara da magoya baya da sauran al’umma da su tattauna bada haɗin kai ga jami’an tsaro da dokokin da hukumar zaɓe ta gindaya.
Sai dai ya ja kunnen al’umma kan duk yunkuri na tada zaune tsaye, wanda ya ce jami’an da na nan cikin shirin ko ta kwana za su aiki a dokance domin tabbatar da doka da oda.
Kazalika ya roƙi al’umma da su zauna lafiya sannan su zama masu lura da sanya ido a lokacin zaɓen, da ƙarfafa jama’a da su riƙa bayar da bayanan ta jami’an tsaro akan duk wani abinda ba su amince da shi ba.














