ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano

by El-Zaharadeen Umar
5 days ago
Mashako

Duk mutum 2 zuwa 3 na masu dauke da cutar mashako da ke kwance a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Katsina na iya mutuwa saboda cutar, gargadin wani kwararen likita.

Wannan gargadi dai ya zo daga bakin shugaban kungiyar likitoci na kasa reshen jihar Katsina akan cututtuka a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya Dakta Mohammed Abubakar

Da yake magana dangane da yaduwar cutar mashako a Jihar Katsina Dakta Mohammed Abubakar ya ce asibitin na cikin halin matsatsi saboda karuwar masu cutar mashako musamman kananan yara.

ADVERTISEMENT

A cewar sa, tsakanin kashi 70 zuwa 80 na wuraren da ake ajiye marasa lafiya sun cika makil da masu dauke da cutar mashako inda ya ce gadaje 20 cikin 25 da cibiyar take da su sun cika.

Ya kara da cewa fiye da kashi 80 na marasa lafiya yara ne kanana sannan asibitin na amsar mutane 20 zuwa 25 na masu dauke da cutar mashako inda acikin mako guda suna kaiwa har mutum 50

LABARAI MASU NASABA

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

“Fiye da marasa lafiya 10 daga cikin wadanda ake kwantawa mutum 2 zuwa 3 na iya rasa ransu sakamakon cutar mashako” inji Abubakar.

Kazalika ya dora alhakin yawatar rasa rayuka da ake yi sakamakon cutar mashako saboda karancin maganganun da ake amfani da su wajen magance kwayoyin halittar.

Shugaban kungiyar likitoci ya ce allurar antitodin ta yi karancin tsawon watanni, amma yanzu an samu ta hanyar gwamnati da kuma abokan hulda na kasashen waje.

“Ba wai ba da maganin kwayoyin cuta (antibiotics) kadai ake yi ba. Maganin yana kawar da gubar mashako da yin aiki cikin sauri wajen dakatar da gubar cutar daga ci gaba da lalata jiki,” in ji shi.

Dakta Abubakar ya ce asibitin na aiki da cikakken karfin ta fiye da wata daya. Ya kara da cewa yanayin ya canza so sai a satin da ya gabata, lokacin da cibiyoyin killace masu dauke da cutar mashako suka cike asibitin, wanda ya tilasta ma’aikatan lafiya yin amfani da wuri na wucin gadi domin kula da marasa lafiya na gaggawa.

A ziyarar gani da ido a wurin killace masu dauke da cutar na Hajiya Murja da cikin asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya ya nuna irin yadda abubuwa suka rintsabe inda yara da iyayensu suka cika wurin babu masaka tsinke. Inda zaka ga wasu yaran suna kuka tare da nuna alamun kamuwa da cutar mashako.

Wani ma’aikacin asibitin da ya ce a boye sunansa saboda ba shi ke da ikon yin magana ba, ya ce ma’aikatar asibitin har sun gaji da yawan cinkoson marasa lafiya

Ya kara da cewa fiye da marasa lafiya 40 ne aka yi wa magani a baban dakin da ake amfani da shi a matsayin wajen killace masu dauke da cutar mashako, sannan gini mai sunan Hajiya Murja an yi amfani da shi dakin wucin gadi domin kula da marasa lafiya

Suma hukumomin asibitin sun dauki matakan rage raduwar wannan cuta ta hanyar tsare duk wanda ake zargi yana dauke da ita, sannan wanda aka tabbatar yana dauke cutar ana ajiye shi a cibiyar killace masu cutar tare umartar ma’aikatan lafiya su yi amfani dubarun kariya da kashin kan su.

A cewar Dakta Abubakar mafiyawanci masu dauke da lalurar yara ne ‘yan kasa da shekaru 10 inda ya ce shekarun su daga 3 ne zuwa 8 duk da cewa wasu matasa ne da kuma manyan mutane da aka gano suna dauke da cutar

Ya kara da cewa da yawan marasa lafiya an turo su ne asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya daga cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko daidai lokacin da yanayin ya kazance ga kuma cinkoson da yake karuwa

“Da yawa wadanda marasa lafiya  da kuke gani, an kawo su ne daga wasu asibitoci, kuma na san wasu ma na zuwa, ko dai ka gansu  cikin tsananin rashin lafiya ko kuma ka same su suna da wahalar sha’ani” inji shi.

Kwararen likitan ya gano cewa an samu tazara a lokacin allurar rigakafin a matsayin daya daga cikin manyan dalilin da suka dawo da wannan cuta ta mashako inda ya ce akwai yara da yawa da masu sami allurar ba, sannan ba a kammala zagayen rigakafin ba wanda ya ce hakan na iya zama babbar barazana.

Sannan ya yi kira da a kara yawan allurar rigakafin a tsakanin alummomi tare da wayar da kan su, inda ya yi kira ga iyaye da masu kula da marasa lafiya da shugabannin al’umma su tabbatar yaran su sun samu allurar.

Dakta Abubakar ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da samar da magunguna cikin sauri da sauran kayayyakin aiki inda ya nuna bukatar cewa allura kadai ba zata wadatar ba lokacin marasa lafiya ke bukatar kulawa.

Kazalika Dakta Abubakar ya yi kira da kafa cibiyoyin kula da masu dauke da wannan cuta tare da samar da kayayyakin aikin a fadin jihar Katsina domin a rage karuwar marasa lafiya a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya wanda ya bayyana a matsayin hanyar kwara daya da a magance matsalar.

“Muna bukatar wuraren killace masu dauke da wannan cuta akalla guda 3 zuwa 4 wanda hakan zai rage karancin gadaje da ake fama da su a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Katsina” inji shi

Shugaban ya yi kira da a cigaba da kawo magunguna da alluran cutar mashako domin samar da kariya ta hanyar kayayyakin aiki da za a kula da marasa lafiya.

Dakta Mohammed Abubakar ya ce ma’aikatar lafiya ta tarayya ta fara daukar matakai biyo bayan karuwar wannan cuta ta mashako a jihohin Katsina da kuma Kano.

Haka kuma ya roki hukumomi su tabbatar sun taimaka cikin sauri wajen ganin an samar da magunguna ga asibitoci

Shugaban kungiyar likitoci ya bada shawara da iyaye da masu lura da marasa lafiya da su rika neman kulawar likitoci ga yaran da suka kamu da ciwon makogwaro da zazzabi da wahalar hadiyar miyo saboda sune alamun cutar mashako

Haka kuma, ya yi gargadin jinkirin daukar matakan magance cutar, inda ya nuna cewa; samar da allurai da magunguna matsayin wata hanyar ta rage yawan mace-mace.

Har ila yau, Jihohin Filato da Nasarawa, su ma an samu rahoton bullar cutar, inda hukumomi suka bayyana cewa; suna iya bakin kokarinsu, wajen ganin shawo kan al’amarin.

A daidai lokacin hada wannan rahoto, babu wani tsayayyen adadi na yaran da suka kamu da wannan cuta ta mashako a wadannan jihohi bayan barkewar cutar.

Mashako
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    NSCDC Ta Tura Jami’ai 10,210 Da Za Su Sanya Ido A Zaɓen Gwamnan Jihar Osun

MASU ALAKA

Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Next Post
Mashako

Babu Wanda Zai Ƙara Tsorata Mu - Peter Obi

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.