ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekaru 8 Cikin Raɗaɗi: Wani Bawan Allah Ya Samu Tiyata Kyauta Daga Gidauniyar Mangal

by El-Zaharadeen Umar
3 weeks ago
Allah

Wani majinyaci daga ƙaramar hukumar Ɗanmusa ta Jihar Katsina, Yusuf Umaru, ya samu tiyatar kyauta ta kimanin naira miliyan ɗaya, bayan shafe shekaru takwas yana fama da ciwo da matsalar yin fitsari.

Umaru, wanda ya bayyana haka bayan an yi masa tiyatar a asibitin ƙashi na Amadi Rimi da ke Katsina, ya ce matsalar ta jefa shi cikin raɗaɗii tare da kawo cikas ga ayyukansa na yau da kullum tsawon shekaru.

Ya ce ya daɗe yana neman magani a wasu asibitoci, amma an buƙaci ya biya kimanin naira 700,000 kuɗin tiyatar kaɗai, yayin da sauran kuɗaɗe da suka haɗa da magunguna, wasu hanyoyin jinya da kuɗin kwanciya a asibiti suka kai kimanin naira 300,000.

ADVERTISEMENT

A cewarsa, matsalar yin fitsarin cikin sauki ta ƙara tsananta masa rayuwa, yayin da kuɗin samun kulawar likitoci ƙwararru suka gagari ƙarfinsa.

Ya ce halin da yake ciki ya sauya ne bayan an gano shi a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su amfana da shirin bayar da tallafin lafiya kyauta da gidauniyar Mangal ta ɗauki nauyi a Katsina.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Umaru ya bayyana jin daɗinsa da godiyarsa ga gidauniyar, yana mai cewa tallafin ya dawo masa da fata bayan shafe shekaru yana rayuwa cikin raɗaɗi.

Ya ce tallafin ba wai kawai ya rage masa nauyin biyan kuɗin tiyata ba ne, har ma ya ba shi damar samun kulawar ƙwararrun likitocin da ya daɗe yana buƙata.

Haka kuma, wata wadda ta amfana da shirin, Khadija Abdullahi, ta ce ɗiyarta ƴar shekara biyu ta yi fama da cutar Hydrocele, wato kumburin da ke tattare da ruwa a kusa da gabanta, na tsawon kusan shekara guda.

Ta ce rashin ƙarfin tattalin arziki ya hana iyalinta samun damar biyan kuɗin tiyatar, tana mai bayyana fatan cewa shirin zai taimaka wajen dawo da lafiyar ɗiyarta.

Wata mahaifiya da ta yi magana a madadin ɗanta, Isma’il Bishir, mai shekaru 15, ta ce yaron ya daɗe yana fama da raɗaɗin matsalar duwatsun ƙoda.

Ta ce iyalinsu ba su da ƙarfin biyan kuɗin magani saboda halin da suke ciki na rashin kuɗi, lamarin da ya sa matsalar ta ƙara tsananta kafin a shawarce su da su tuntuɓi gidauniyar Mangal.

A cewarta, bayan tuntuɓar gidauniyar, an sanya wa ɗanta lokacin gudanar da tiyata.

Ta yaba wa gidauniyar bisa samar da maganin kyauta, tana mai cewa tallafin ya kawo sauki ga iyalinta bayan dogon lokaci na fama da matsalar.

Allah
El-Zaharadeen Umar
+ postsBio
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Cutar Mashako:Yadda Yara Ke Mutuwar Bazata A Jihohin Katsina Da Kano
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Mauludin Annabi (SAW): Shugaba Tinubu Ya Nemi A Yi Addu’o’in Nasara Kan Matsalar Tsaro
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    Tinubu Ya Nemi Malamai Su Taimaka Wajen Yaƙi Da Ƴan Ta’adda
  • El-Zaharadeen Umar
    https://hausa.leadership.ng/author/el-zaharadeen-umar/
    NSCDC Ta Tura Jami’ai 10,210 Da Za Su Sanya Ido A Zaɓen Gwamnan Jihar Osun

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Ghana Na Neman Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Yammacin Afrika Domin Bunkasa Kiwon Lafiya A Yankin

Ghana Na Neman Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Kasashen Yammacin Afrika Domin Bunkasa Kiwon Lafiya A Yankin

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.