Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tunibu ya yi kira ga malaman addini da shugabanin Afrika da sauran ƙasashe da su yi amfani da muryoyin su wajen yaƙi da ƴan ta’adda da masu garkuwa da mutane tare da masu amfani da addini wajen tada zaune tsaye inda ya ce babu wani aikin Allah da sai an haɗa da tada hankali.
Shugaba Tunibu ya yi wannan kira a ranar Lahadi a wani sakon fatan alheri da ya aike a Kano wajen taron Mauludin Sheikh Ahmad Al-Tijjani RTA wanda sakataren gwamnatin tarayya Sanata George Akume ya wakilta.
Da yake jawabi ga Khalifan Tijjaniyya na duniya, malamai, shugabannin addini da mabiya daga Nijeriya da wasu ƙasashe, shugaban ƙasa ya buƙaci cibiyoyin addini da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma game da ilimin zaman lafiya, fahimtar addini, neman ilimi da kuma tarbiyyantar da matasa bisa ƙyawawan ɗabi’u.
Dole ne ku yi amfani da muryoyin ku a kowane lokaci domin ƙalubalentar kisan mutanen da ba su ji, ba su gani ba da ƴan ta’adda ke yi da masu garkuwa da mutane da masu amfani da addini wajen biyan buƙatar kan su. Alaƙar wannan damdala ta ku dole ta ƙara karfi wajen kawo zaman lafiya da ilimin addini tare da bunƙasa jama’ar ku maza da mata” inji shi
“Haka kuma dole ne ku tunawa shugabannin siyasa irin nauyin da ya rataya akan su, sannan ku faɗawa ƴan ƙasa cewa jin haushin abu ba shi zai bada damar yin abinda mutum ya ga dama ba. Dukkan waɗannan abubuwan jagororin mu ya kamata su cigaba da faɗakar da al’umma yadda ake bautar Allah ba ta hanyar kashe -kashen al’umma.” Inji shugaban ƙasa
Shugaba Tunibu ya bayyana cewa wannan taro ya zo a daidai lokacin da al’umma ke fuskantar ƙalubale da faɗace-faɗace da barazanar canjin yanayi da ƙarancin abinci da hare-haren ƴan bindiga da juya al’umma ta wata hanyar da bai daidai ba.
Da yake ambaton wani rahoto na hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalisar ɗinkin duniya Tunibu ya ce mutane miliyan 117.8 ne aka tilasta musu barin gidajensu a faɗin duniya zuwa wasu ƙarshen a shekarar 2025, lamarin da ke ƙara nuna muhimmancin shugabannin addini wajen taimakawa a riƙa ba zuciya hakuri ta hanyar sauraran korafe-korafe da yaƙi da ƙiyayya.
Bola Tunibu ya ce al’umma magoya bayan Tijjaniya suna da wani irin tsari haɗuwa a ƙasashen Afrika da Afrika ta Arewa da za su iya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa zaman lafiya tare da tunkarar duk wani ƙalubalen tsaro da baiwa matasa kyakkyawar kulawa da nuna kauna.














