Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Bauchi sun samu nasarar taso ƙeyar wani tsoho mai shekara 70 a duniya, Usman Abubakar, bisa zargin yin fyaɗe da cin zarafin wata ƙaramar yarinya ‘yar shekara takwas a yankin Tsakanin Bayara da ke cikin garin Bauchi.
An kai rahoton faruwar lamarin ne ga canji ofis ɗin ‘yansanda na ‘E’ Division da ke Yelwa a ranar Laraba, inda mahaifin yarinyar, mai shekaru 48, ya shigar da koke, yana zargin cewa a ranar Lahadi, 24 ga watan Agusta, Usman Abubakar, wanda ke zaune a unguwa guda tare da su, ya yaudari ‘yarsa zuwa wani ginin da ba a kammala ba, inda ake zargin ya aikata lalata da ita.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar ranar Lahadi, ya ce cafke wanda ake zargin na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka a ci gaba da yaƙi da laifukan cin zarafin mata da yara.Nafiu ya ce bayan samun rahoton, jami’an sashen sun gaggauta ɗaukar mataki tare da cafke wanda ake zargin.
Sanarwar ta ce, “A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin.” An garzaya da yarinyar zuwa asibitin ‘yansanda domin gudanar da gwaje-gwajen lafiya da kuma ba ta kulawar da ta dace.
Kwamishinan ‘Yansandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da lamarin, tare da tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta gudanar da cikakken bincike kan lamarin.Ya kuma ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bisa tanadin doka.
A halin yanzu, an mayar da kes ɗin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar (SCID), Bauchi, domin gudanar da bincike cikin sirri da kuma gurfanar da wanda ake zargin.
Rundunar ta sake jaddada cewa ba za ta yi sako-sako kan laifukan cin zarafin mata da yara ba, tare da yin kira ga iyaye, masu kula da yara da sauran al’umma da su kasance cikin taka-tsantsan tare da gaggauta kai rahoton duk wani abin da ake zargi ga ofishin ‘yansanda mafi kusa.














