Tsohon mai neman takarar gwamnan Jihar Bauchi a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Captain Muhammad Bala Jibrin, fice daga cikin jam’iyyar, yana mai bayyana rashin adalci da kuma zargin yin ɗauki-ɗora na ‘yan takara a matsayin dalilan ficewarsa.
Jibrin ya bayyana murabus ɗin sa ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 31 ga watan Agusta, 2026, wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na mazaɓar Nasarawa/Bakin Kasuwa da ke Azare, a ƙaramar hukumar Katagum ta jihar.A cikin wasiƙar, ya ce murabus ɗinsa da kuma janye goyon bayansa ga APC zai fara aiki nan take.
Ya ce matakin nasa ya samo asali ne musamman daga abin da ya ƙira “rashin adalci tsantsa” da kuma ɗauki-ɗoran ‘yan takara a zaɓukan cikin gida na jam’iyyar, ba tare da la’akari da ra’ayoyin ‘ya’yan jam’iyyar ba.Ya ce, “Na yanke wannan shawarar ne musamman saboda rashin adalci tsantsa da kuma ɗauki-doran ‘yan takara a zaɓukan fitar da gwani, ba tare da la’akari da ‘yan jam’iyya a Jihar Bauchi ba”.
Tsohon ɗan takarar ya ce ya yanke shawarar ne bayan tattaunawa da magoya bayansa, da abokan hulɗarsa, waɗanda ya ce sun amince da matakin da ya ɗauka na ficewa daga jam’iyyar.Jibrin ya kuma bayyana ficewarsa a matsayin “mataki mafi daraja,” maimakon ci gaba da kasancewa a jam’iyyar da yake ganin ana raina ‘yan cikinta.
Jibrin ya kasance mai yawan sukar matakin APC na tsayar da tsohon gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar SAN, wanda aka fi sani da M.A. Abubakar, a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na jam’iyyar a zaben 2027.Kafin gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar, Jibrin ya yi adawa da shirin tsayar da tsohon gwamnan, yana mai cewa bai dace ya wakilci jam’iyyar a babban zaɓen 2027 ba.
Daga bisani ya yi zargin cewa Abubakar ya samu tikitin jam’iyyar ne ta hanyar ɗoki-dora da wasu tsirarun mutane suka yi. A wani taron manema labarai da ya gudanar gabanin zaɓen fidda gwani na APC, Jibrin ya gargaɗi masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da kada su “cutar da al’ummar Bauchi ta hanyar tursasa da tilasta musu ɗan takarar da ba sa so.”
A cewarsa, mazauna Bauchi za su yi adawa da duk wani yunƙurin na dawo da Barr. Mohammed Abdullahi Abubakar kan karagar mulki, yana mai cewa tsohon gwamnan an riga an “Gwada shi, an tantance shi, sannan aka yi watsi da shi a zaɓen shekarar 2019.”
Ya ce, “Ya kamata su nisanci duk wani shiri na tilasta wa al’umma wani shugaba mara kwarewa, maras tausayi kuma mai son kai, wanda ya samu damar yin wa jama’a hidima amma ya Ka-sa-ka-sau.”
Ya kuma gargaɗi Farfesa Ali Pate da kada ya goyi bayan abin da ya kira yunƙurin tsohon gwamnan na dawowa kan mulki, yana mai cewa hakan ba zai amfani al’ummar Bauchi ba.
Da yake magana ta wayar tarho da wakilinmu kan dalilin ficewarsa daga jam’iyyar, Captain Bala Jibrin ya ce bai ga wata hujja mai karfi da za ta sa ya ci gaba da kasancewa a APC ba, wadda ya zarga da rashin ba da fifiko ga muradun talakawa.
Jibrin ya bayyana cewa ba zai goyi bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko Muhammad Abdullahi Abubakar a zaɓen ba, yana mai cewa a ganinsa, babu ɗaya daga cikinsu da ya nuna cikakkiyar himma wajen hidimta wa al’umma.
Ya kuma zargi shugabannin APC da gaza tabbatar da adalci, tare da nuna rashin cikakkiyar niyyar inganta rayuwar talakawa, yana mai cewa son kai ne ke jagorantar wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar, saɓanin yadda suka haɗa kansu wajen kafa APC tun da farko.Ya ce wadannan dalilai ne suka tabbatar masa da cewa ficewa daga jam’iyyar shi ne matakin da ya dace ya dauka.














