Hukumomi a Kasar Turkiyya sun sanar da cewa za a yi bikin karamar sallar Idi a kasar a ranar Juma’a 21 ga watan Afrilun 2023 hakan na nuni da cewa za su ajiye Azumi a wannan ranar.
Hukumar kula da harkokin Addini ta kasar Turkiyya ce ta sanar da hakan, ta ce, al’ummar kasar sun azumci watan Ramadana na tsawon kwanaki 29 da suka fara daga ranar 23 ga watan Maris zuwa 20 ga watan Afrilu.
- Kasashen Yamma Na Shafawa Sin Bakin Fenti Bisa Fakewa Da Karuwar Jama’ar Indiya
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kwaso Daliban Nijeriya Bayan Barkewar Rikici A Sudan
Kamar yadda kafar Morocco World News ta nakalta, inda musulmai za su kasance cikin farin ciki domin shaida bikin Idi na sallah karama.
Kana bikin na kasancewa dama wajen nuna godiya ga Allah bisa kammala gudanar da ibadar Azumi da al’ummar musulmai suka yi.
Kasar Tukiya ta maida hankali wajen jawo hankalin masu hannu da shuni da su taimaki marasa karfi a cikin al’umma da nuna soyayya da kauna ga wadanda aka raunata sakamakon matsaloli daban-daban da suka riske su.
A ranar 6 ga Fabrairu, 2023, wata mummunar girgizar kasa ta afku a kudanci da tsakiyar Turkiya, da arewaci da yammacin Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 50,000
Babban malamin addinin musulunci a Turkiyya Kuma shugaban Majalisar ta harkokin addinin musulunci, Ali Erbas, ya ce, taken watan Ramadan na bana shi ne nuna goyon baya ga wadanda suka jikkata domin samun damar taimaka musu.
Shi dai bikin Eid Al Fitr Rana ce ta farko da al’ummar musulmai ke bude baki bayan watan Ramadana su na azumi. Lamarin da ke bayar da dama wajen ziyarce-ziyarce da gaishe-gaishen juna.