ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Iran Ta Zargi Amurka Da Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wutar Da Ke Tsakaninsu

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago

Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninsu, bayan da mahukuntan birnin Washington suka bayar da umarnin kai farmakin kan cibiyar harba makamai masu linzami da kuma jiragen ruwan yaƙin Iran a cikin daren da ya gabata.

Mai magana da yawun rundunar sojin Amurka Tim Hawkins, ya ce sun kai farmakin ne domin kare kai daga duk wata barzana da za ta iya fitowa daga dakarun Iran musamman ma a ɓangaren kudancin ƙasar.

Sanarwar ta ƙara da cewa an kai hare-haren ne kan cibiyoyin da Iran ke amfani da su domin harba makamai masu linzami, da kuma jiragen sojin ruwan ƙasar da ke ƙoƙarin dasa nakiyoyi a teku. Kuma wannan shi ne karon farko bayan share makonnin 7 babu tsokana a tsakaninsu.

ADVERTISEMENT

Makomar yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakanin amurka da iran?

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da ke ziyara a ƙasar Indiya, ya ce duk da farmakin da dakarunsu suka kai, yarjejeniyar tsagaita wutar na nan daram, kazalika tataunawar da ɓangarorin biyu ke yi a Ƙatar za  ta ci gaba, yana mai cewa ga alama ana ma dab da cimma yarjejeniya.

LABARAI MASU NASABA

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

Sai dai ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana harin da Amurka ta kai a yankin Bandar Abas mai tsahar jiragen ruwa a matsayin karya yarjejeniyar tsagaita wuta da ke tsakaninsu, yayin da Rundunar Sojin Iran ɗin ke cewa ta harbo wani jirgi maras matuƙi mallakin Amurka lokacin da ya shiga sararin samaniyar ƙasar.

Inda tattaunawar Amurka da Iran ta fi karkata

Bayanai na nuni da cewa, Amurka da Iran na tattaunawa ne wannan karo kan abubuwa 14 a maimakon 20, amma batun sako wa Iran bilyoyin kuɗaɗe da Amurka ta riƙe a sassan duniya, da janyewar dakarun Amurka daga Gabas ta Tsakiya, da tabbatar da cewa ba wani jami’in sojin Amurka a Hormuz, da kawo ƙarshen duk wasu hare-hare da Isra’ila ke kai wa ƙasar Lebanon da dai sauransu, su ne suka fi ɗaukar hankula a zaman da ake yi a birnin Doha ƙasar Ƙatar.

Tasirin harin Amurka kan Iran a kasuwannin Duniya

Tasirin da wannan mataki ya yi shi ne, haifar da fargaba a tsakanin al’ummomin ƙasashen Yankin Gulf da kuma su kansu al’ummar ƙasar Iran, bayan share makwanni na tsagaita wuta, daga nan kuma an ɗan samu hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya saboda fargaba.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Kasashen Ketare

Nijar Da Canada Sun Ƙulla Yarjejeniyar Gina Sabuwar Matatar Mai A Jihar Dosso

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Kotun ICC Ta Yi Watsi Da Sabbin Takunkuman Amurka Kan Jami’anta

August 23, 2026
Kasashen Ketare

Rasha Da Ukraine Sun Zafafa Hare-hare Kan Juna Bayan Yaƙinsu Ya Ɗauki Sabon Salo

August 22, 2026
Next Post
Dambazau Ya Karɓi Aiki A Matsayin Jakadan Nijeriya A China

Dambazau Ya Karɓi Aiki A Matsayin Jakadan Nijeriya A China

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.