ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, July 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Tsaro A Nijeriya: Gazawar Masu Mulki Ce Da Cin Amanar Ƙasa

by Alhaji Adamu Rabiu
6 months ago
Nijeriya

Taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya, musamman a yankunan Kaduna, Katsina, Zamfara, Abuja da sauran wasu ɓangarorin; na ƙara ƙamari fiye da sauran lokuta a baya. Yayin da al’ummar ƙasar ke fama da ɗimbin ƙalubalen da ba a taɓa ganin irin sa a baya ba, kama daga yawaitar ƴan fashi da garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da sauran ƙalubalen tsaron da ya mamaye su.

Har ila yau, al’ummar wannan ƙasa sun shaida yadda aka yi asarar dubban rayuka da miliyoyin mutanen da suka rasa muhallinsu da durƙushewar harkokin tattalin arziƙi da kuma tauye ikon gwamnati.

  • Ɓata-gari Sun Kashe Matar Aure Da ’Ya’yanta 3 A Kano
  • ’Yansanda Sun Kama Mutane 2 Kan Sace Matan Aure A Kaduna

Wannan tashin hankali, na nuna gazawar shugabanci da rashin aiwatar da ayyuka da kishin ƙasa daga ɓangaren zartarwa, majalisar dokoki ta ƙasa, hukumomin tsaro da sauran hukumomi.

ADVERTISEMENT

Kudin Fansa Da Masu Amfana Da Shi

A cewar wani rahoto da kamfanin nazarin al’amuran yau da kullun da siyasa a Najeriya (SBM Intelligence) ya gabatar, tsakanin shekara ta 2011 zuwa 2020, an biya aƙalla dala miliyan 18.34, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 23; ga masu garkuwa da mutane a matsayin kuɗin fansa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

Ko shakka babu, garkuwa da mutane ya fi aikin gwamnati ko siyasa riba. Sannan, shin su wa ke amfani da kuɗaɗen fansar da ake biya ga masu garkuwa da mutanen?  Hasashe ya nuna cewa, mai yiwuwa a yi amfani da kuɗaɗen don ƙara sayen bindigogi da sauran makamantansu.

Tambayoyin Da Ke Bukatar Amsa Da Matsalolin Da Ke Buƙatar Warwarewa

A cikin wannan ruɗani, ka da mu manta da irin yadda gwamnati ta yi biris da ƙoƙarin ganin an magance matsalar rashin tsaron da ke addabar al’ummar wannan ƙasa, tun daga ɓangaren zartarwa zuwa na majalisa da kuma na na tsaro. Har wa yau, babban maƙasudin aikin waɗannan mutane shi ne samar da ingantaccen shugabanci tare da tsare rayukan mutane da dukiyoyinsu ba wani abu daban ba.

Bugu da ƙari, wane ƙoƙari kamfanonin sadarwa ke yi don taimakawa wajen daƙile wannan matsala? Mene ne tasirin bin diddigin masu aikata laifukan? Gano kuɗaɗen haram da kuma sa ido a kan zirga-zirgar ababen more rayuwa kamar babura da wayoyin hannu, waɗanda masu aikata laifuka ke amfani da su? Duk waɗannan na nuna babbar gazawar tattara bayanan sirri da kuma amfani da fasaha ne.

Shin mene ne amfanin katin shedar zama ɗan ƙasa (NIN), da kuma lambar tantancewa ta banki (BƁN)? Ko amfaninsu shi ne buɗe asusun banki ko samun lasisin tuƙi da fasfo na ƙasashen waje kaɗai?

Rashin Adalci Da Tausayi

Dangane da irin wannan ta’asa, ƴan ƙasa ne waɗanda ba su ji ba; ba su gani ba ke ɗaukar nauyin wannan sakaci, waɗanda laifinsu kawai shi ne na zama ƴan Nijeriya, ke fama da wahalhalu da cin zarafin da ba zai iya misaltuwa ba a hannun miyagu marasa tausayi da kuma gwamnatin da ta yi biris da haƙƙinsu da ke kanta.

Duk da irin wahalhalu da rashi da kuma asarar da aka yi musu, halin da suke ciki ya ta’azzara; sakamakon rashin ingantattun dokoki ko hanyoyin da za a bi don daƙile ko hukunta waɗannan masu laifi ko kuma samun diyya da tallafi daga gwamnati. A yayin da kukansu na neman adalci da taimako ya faɗa a kunnen uwar shegu tare da ci gaba da zaman ɗar-ɗar, kazalika su kuma masu aikata wannan aika-aika na nan suna yawo cikin walwala, su kuma waɗanda haƙƙinsu ne kama masu aikata waɗannan laifuka, sun shagaltu da neman ƙarin albashi tare da yin sharholiya da kuɗaɗen gwamnati.

Gazawar Gwamnati Da Hukumomi

Shugabannin Nijeriya, na fuskantar wata muhimmiyar jarrabawa; wanna kuwa ita ce gazawarsu. Ƴan majalisar dokokin ƙasar da aka ɗora wa alhakin wakilcin jama’a, sun yi biris ko kunnen uwar shegu da haƙƙoƙin jama’a da ke kansu. Yayin da hukumomin tsaron da suka haɗa da ma’aikatar tsaron ƙasar, ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro da kuma rundunar ƴan sanda; ga dukkanin alamu ba za su iya tinkarar barazanar da ke ƙara ƙamarin matsalar tsaron ba.

Har ila yau, an kwashe shekaru da dama ana gudanar da shugabanci na rashin adalci a Nijeriya, wanda wannan alama ce da za a iya gani ko a wannan gwamnati, domin kuwa ɓangaren zartarwa a halin yanzu na ci gaba da sayen motocin hawa, gina sabbin ɗakunan zama na shugaban ƙasa a filin jirgin sama na Abuja da gyaran gidajen gwamnati da ke Legas da Abuja, yayin da kuma sauran ƴan Nijeriya da dama ba su da matsugunan da za su sanya ɗuwawunsu. Wannan hali na rashin ko in kula na gwamnati, babu shakka ya bar ƴan ƙasa a cikin wani mawuyacin hali.

A wannan halin da ake ciki, su kuma ýan majalisun maimakon su kafa dokoki masu tsauri don magance rashin tsaro; sai suka ɓuge da neman a saya musu motocin alfarma ƙirar ‘Prado jeeps’ kowace ɗaya a kan kuɗi har Naira miliyan160, motocin da ba za su iya kare su daga sharrin waɗannan ƴan ta’adda masu garkuwa da mutane ba. Yayin da su kuma jami’an tsaro suka kasa samo bakin zaren. Babu shakka, wannan babban abin takaici ne ƙwarai da gaske.

Ƙin Amfani Da Na’urorin Fasaha

Gwamnatoci da majalisu daban-daban da suka haɗa da na yanzu, sun yi ta faman farfaganda a kan batun tsaro tare da buƙatar ƙarin kuɗaɗen tsaron da kuma batun sayen jiragen ‘Tucano’ da sauran makamantansu, maimakon ƙalubalen tsaron da ake fuskanta ya ragu, sai ci gaba aka samu ta fuskar ta’adanci, wanda a zahiri ya nuna cewa a gaskiyar magana Nijeriya ta shafe shekaru masu yawa ta na gudanar da shugabanci maras kan-gado da adalci, wanda shi ne ya haifar da wannan yanayi na rashin tsaro da ake fama da shi a halin yanzu.

Shin zai iya yiwuwa gwamnati da sauran hukumomin tabbatar da doka da oda a ce ba su da masaniya game da sahihancin sa ido tare da samar da na’urorin bin diddigin da ka iya taimakawa wajen kawo ƙarshen wannan ta’adanci? Ko kuwa sun yi tsada ne ko kuma Nijeriya ba ta da ma’aikatan da za su tunkari wannan aikin ne?

A Ƙarshe

Taɓarɓarewar rashin tsaro, wata alama ce ta gazawar gwamnati da hukomomi. Don haka, ya kamata waɗanda ke kan madafun iko su amince da gazawarsu tare da gyarawa ko kuma su yi murabus daga muƙamansu. Yanzu lokaci ya yi da ya kamata jama’a su fara bin kadin yadda ake gudanar da mulki a kansu. Domin kuwa, jin daɗin al’umma da tsaron lafiyarsu shi ne a kan gaba cikin Kudin Tsarin Mulkin Nijeriya, ba siyasa mara ma’ana irin ta wannan ƙasa ba.

Alhaji Adamu Rabiu ya rubuto daga Kaduna

Nijeriya
Alhaji Adamu Rabiu
+ postsBio
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    Hanyoyin Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuradiyyar Nijeriya
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima

MASU ALAKA

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makaranta, Jami’in NECO Da Ɗalibai A Kogi

July 15, 2026
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya
Manyan Labarai

Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan SDP A Gombe Ya Koma PDP, Ya Mara Wa Pantami Baya

July 15, 2026
Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221
Labarai

Zazzaɓin Lassa: Mutum 31 Sun Kamu Da Cutar A Jihohi 4, Waɗanda Suka Rasu Sun Kai 221

July 15, 2026
Next Post
Sojojin Sama Sun Hallaka Fiye da Ƴan Ta’adda 40 A Borno

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

‘Yansanda Sun Kama Shugaban PFIPC, Adeyemi

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

‘Yansanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yi Wa ‘Yan Bindiga Safarar Makamai A Kano

July 15, 2026
Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya

July 14, 2026
Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026

July 14, 2026
An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

An Yi Tir Da Kalaman Wasu Sassan Ketare Game Da Yayata Batun Cika Shekaru Goma Da Fitar Da Abin Da Aka Kira “Hukuncin Tekun Kudancin Sin”

July 14, 2026
Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

Nijeriya Za Ta Zama Ƙasa Mai Zaman Lafiya, Ba Za A Ƙara Samun Kashe-kashen Jama’a Ba – Oluremi Tinubu

July 14, 2026
Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Tsara Bunkasa Darajar Cinikayyar Kayayyaki Zuwa Yuan Tiriliyan 60 Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.