ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hanyoyin Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuradiyyar Nijeriya

by Alhaji Adamu Rabiu and Sulaiman
4 months ago
Dimokuradiyya

Lokacin da matasan Najeriya za su hallara a zauren babban taron matasa na kasa, daga 7 zuwa 21 ga Yulin 2025 a birnin Abuja, tambaya guda daya ce za ta mamaye tattaunawar a karkashin jigo mai taken “Gudanar da Mulki Da Shiga Harkokin Siyasa”.

Ta yaya za mu dora siyasarmu a kan turba madaidaiciya, sannan kuma mu ceto dimokuradiyya daga hannun azzalumai a Nijeriya? A matsayina na mai gabatar da wannan kasidar tsarin manufofi zuwa kwamitin shirya taron, ban tsaya kan bayyana matsaloli kadai ba, na zo da cikakken shiri na ceto dimokuradiyyar wannan kasa.

Nijeriya na fama da mummunar matsalar rashin kyakkyawan fasilin siyasa, inda masu kudin haram ke karbe jam’iyyun siyasa, fagen siyasa ya zama cike da hadura da dungu, zabe ya koma yaudara, inda wanda ya ci zabe shi kadai ke cin moriyarta, ’yan gudun hijira sun rasa damar kada kuri’arsu, sannan hukumomin zabe na jihohi, sun zama karen farautar masu rike da madafun iko a jihohi, sannan suna yi wa gaskiya da rikon amana rikon sakainar-kashi.

ADVERTISEMENT

Wadannan matsaloli da wasu ma, na bukatar matasa su yi karatun ta-nutsu, su kuma  dauki matakin gaggawa; domin ceto Nijeriya daga hannun azzalumai, kana su kuma dora ta a kan turba madaidaiciya.

Matsalolin Da Muke Fuskanta:                    

LABARAI MASU NASABA

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

Bayan shekar 22 da kubutar da Nijeriya daga mulkin soja, dimokuradiyya na ci gaba da fama da rauni mai tsanani. Alamun cutar sun bayyana ne a cinikin baragurbin wakilai (delegates), amfani da kudin kasa da aka wawure ta hanyar haram wajen gudanar da yakin neman zabe, makudan kudin da ake ware wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), karancin yawan masu kada kuri’a, sayen kuri’u a bainar jama’a, tashin hankali yayin zabe, da kuma yaduwar fargaba, musamman a tsakanin matasa, cin amana na ’yan siyasa, canja sheka da zababbu ke yi, da dai sauran makamantansu.                                      

Asalin matsalar ita ce, rashin shiga cikin gudanar da gwamnati a siyasance (edclusion) na masu gaskiya da rikon amana, matasa, mata, masu fama da nakasa, ‘yan gudun hijira da jam’iyyun da ke da karamin karfi, duk sun kasance a wajen filin.

Wannan ba kawai rashin adalci ba ne, har ma ya saba wa kundin tsarin mulki, kuma barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban kasa. Idan ka duba, za ka fahimci cewa; dimokuradiyyarmu na hannun wasu tsirarun mutane da shugabannin jam’iyyu masu karfi, wadanda suka killace matasa da sauran ‘yan Nijeriya daga samun damar shiga siyasa ko a saurare su ko la’akari da tasu gudunmawar. Dimokuradiyyar cikin gida a jam’iyyu, abin dariya ne kawai, domin an mayar da zabe na cikin gida zuwa ciniki, wato ba ni kudi ga kuri’a. Inda a wani bangaren kuma, INEC na fuskantar kalubalen rashin ’yanci da rashin kwarin guiwar aiwatar da dokokinta.

Har ila yau, ‘yan gudun hijira da sauran al’umma masu rinjaye ana ci gaba da ware su daga zabe. Haka nan, hukumar zaben jihohi, musamman yadda aka gani a zaben kananan hukumomi a Kaduna da Bauchi, sun zama wani kwafi da ya ci mutuncin dimokuradiyya. Wannan ya saba wa sassa da dama na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (Sashe 14(2)(a), 15(1), 40, 153(1)(f), 221, 318(1), da Jadawali na Bakwai), da Dokokin Kungiyar Tarayyar Afirka da kuma Majalisar Dinkin Duniya.  

Yadda Wannan Tsari Na Matasa Zai Taimaka Wajen Ceto Siyasarmu:

1-Yarjejeniya Ta kasa Don Siyasa Mai Inganci (National Charter for Inclusion): A samar da wata Yarjejeniya ta hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Matasa ta Kasa, Kungiyar Gamayyan Jamíyyun Siyasa (IPAC), Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Kungiyoyin Fararen Hula da Majalisar Matasa ta Nijeriya. Wannan yarjejeniya za ta kafa ka’idoji da dokokin da za su tilasta dimokuradiyya a cikin jam’iyyu, tabbatar da adalci wajen zabubbuka da kuma bai wa dukkannin jam’iyyun da suka shiga zabe damar ba da gudunmuwa wajen shugabanci a kowane mataki da kuma bai wa matasa, mata, ‘yan gudun hijira da kowa da kowa damar ’yancin tsayawa takara cikin adalci. 

2- Sauyi Mai Zurfi Ga Jam’iyyu da Tsarin Zabe: Ya zama wajibi jam’iyyu su bude kofa. A kafa dokar da za ta tilasta duk mai son tsayawa takara gabatar da “Tsarin Ayyuka” (Project Plans) kafin hawa kujera, sannan ya fitar da “Rahoton Karshe” (End-of-Term Reports), bayan barin gado ko da kuwa zai koma kuwa. A dakile kudin da ake nema marasa tushe daga masu neman takara, musamman na hukumomin zaben jihohi, (Misalin KAD-SIECOM). A tabbatar da cikakken amfani da Sashe na 7 na Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zabe ta 2022.  

3- Runguman Dimokuradiyyar Dijital Hannu Biyu (Digital Democracy): A kafa “Cibiyar Dimokuradiyyar Dijital ta Kasa (NDDH)” da za ta sa ido, bayar da rahoto kai tsaye, sa ido kan kudin yakin neman zabe da tantance tsarin jam’iyyu. Za ta kuma ba da damar samun ilimin siyasa ta hanyar wasanni da fasahar zamani domin kara fahimta, rage rashin sha’awa daga matasa, da bunkasa ilimi da rikon amana.

4- Karfafa IPAC Youth da Shirye-shiryen Fadakarwa: A karfafa Bangaren Matasa na IPAC (IPAC Youth Directorate) daga matakin kasa har zuwa jihohi, ta hanyar samar da doka, kasafin kudi da kuma tsarin aiki. Sannan, a dora musu alhakin wayar da kan jama’a a fadin kasar nan, musamman a tsakanin wadanda aka ware daga siyasa.

Me Za Mu Samu Idan An Bi Wannan Hanya? Za mu samu dimokuradiyya mai inganci da kuma tsabta, inda matasa, mata, masu fama da nakasa (PWDs) da ‘yan gudun hijira (IDPs) za su samu bakin fada kuma a ji a cikin siyasa da shugabanci. Za a samu karancin tashin hankali a lokacin zabe, raguwar sayen kuri’a da ingantaccen ilimi da wayewa a tsakanin jama’a.  Za kuma a samu jam’iyyu masu gaskiya da amana da kuma shugabanci na kwarai da ci gaban kasarmu Nijeriya.

Matakan Aiwanar Da Wannan Tsari:

Mataki na 1: Rubuta NSPPC tare da dukkan masu ruwa da tsaki.

Mataki na 2: Kafa tsarin dubawa tsakanin INEC, IPAC da CSO.

Mataki na 3: Kaddamar da NDDH da kayan aikin ilmantarwa.

Mataki na 4: Gyaran Dokar Zabe, domin shigar da wadanan al‘amura da muka gabatar a sama da sauran bukatu.

Kafin Mu Kammala: Makomar dimokuradiyyar Nijeriya na cikin hadari. Ba za mu iya ci gaba da kallon halin da ake ciki ba na rashin adalci, cin amana, zangon kasa ga kasa da al’úmarta.

Yazama wajibi mu yi amfani da karfin matasa, domin ceto Nijeriya daga bakin kuraye. Kirkire-kirkire da bukatar rikon amana, su ne maganin cutar da dimokuradiyyarmu ke fama da ita.

Wannan tsari nawa na zuwa ne daga gwanancewa da aiki da IPAC, shirye-shiyen fitar da sakwanni ta ‘Bakondare Speaks’, wallafa rubuce-rubuce a manyan jaridu kamar su Premium Times, Daily Trust, Guardian, Punch, Banguard, Thisday , Leadership (A hausance da turanci)) da kuma shiga ayyukan siyasa masu tsafta da kuma alaka da kungiyoyi masu muhimmanci na siyasa.  

Yanzu ne lokacin sauyi! Muryar matasa ya kamata ta koma tsakiya wajen tsara manufofi da aiwatar da su. Yakamata dimokuradiyyar Nijeriya ta amfani kowa da kowa ba wasu ba kawai!

Kafin rahoton karshe na wannan taro ya isa ofishin Shugaban Kasa ranar 12 ga Agusta, 2025 (Ranar Matasa ta Duniya), ina kira da babbar murya da fatan alheri ga duk dan Nijeriya da kuma dukkan wakilai da su rungumi wannan tsari. Ina kuma kira ga ’yan majalisa da masu zartarwa da su aiwatar da shi, domin ci gaban Nijeriya da kuma amfanin masu zuwa nan gaba. Yanzu ne lokacin daukar mataki na hakika da Jarumta! Allah ya yi mana albarka, ameen.

Dimokuradiyya
Alhaji Adamu Rabiu
+ posts Bio
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    Rashin Tsaro A Nijeriya: Gazawar Masu Mulki Ce Da Cin Amanar Ƙasa
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    ADA/ADC, APC Da PDP: Jam ’iyyun Siyasa Da Ke Shan Jinin ’Yan Nijeriya
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
  • Alhaji Adamu Rabiu
    https://hausa.leadership.ng/author/alhaji-adamu-rabiu/
    WAEC Na Buƙatar Kwaskwarima
Dimokuradiyya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Zanga-Zanga: Gwamnatin Yobe Ta Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Jihar
Bakon Marubuci

Buni Ya Nuna Kwarewarsa Ta Diflomasiyya

August 28, 2026
An Kusa Ceto Ɗaliban Neja Da Aka Sace – Ribadu
Bakon Marubuci

Shin Tinubu Ya Tabbatar Da Sauke Ribadu Daga Mukaminsa?

August 28, 2026
Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya
Bakon Marubuci

Kwairanga Ya Kafa Tarihi A Shugabancin Hukumar Kula Da Kasuwar Hannun Jari Ta Nijeriya

July 24, 2026
Next Post
Amfanin Man Kwakwa Guda 12

Amfanin Man Kwakwa Guda 12

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.