ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 15, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rayukan Mutanen Kenya Na Da Muhimmanci Daidai Da Na ‘Yan Amurka

by Sulaiman and CGTN Hausa
4 months ago
Kenya

Amurka ta sake cusa matsalolinta ga wasu.

Bisa rahotannin da aka bayar, an ce, gwamnatin Amurka na shirin gina wurin kula da marasa lafiya mai gadaje 50 a sansanin sojin sama na Laikipia dake kasar Kenya, domin a ajiye ‘yan Amurkan da ke cikin hadarin kamuwa da cutar Ebola, maimakon mayar da su Amurka kamar yadda aka saba. Har ma sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya fadi karara cewa: “Ba za mu bari ko da mutum daya da ya harbu da cutar Ebola ya shiga Amurka ba.” Wato ke nan ba za a bari Amurkawa su fuskanci hadarin ba, amma al’ummar Afirka za su iya fuskantar shi.

Duk da cewa Amurka tana da mafi kyawun hanyoyin kiwon lafiya da karfin tattalin arziki, maimakon ta yi aikin da ya dace da matsayinta na kasa mai girma, sai ta nuna tsananin son kai, ta jefa matsaloli da annoba ga Afirka don neman kare kanta daga hadarin cutar. Yayin da suka fuskanci wannan rashin adalci, al’ummar Kenya ba su yi shiru ba. Babbar kotun Kenya a ranar 29 ga watan Mayu ta dakatar da wannan shiri, saboda kasancewarsa “Mai barazana ga rayuka”, kuma za ta saurari karar a gobe Talata 2 ga watan nan. Cibiyar Katiba da ta shigar da karar a madadin ‘yan Kenya, ta ce “Babban abin da ke cikin wannan shari’a shi ne tabbatar da bin tsarin mulki, da kare lafiyar jama’a, da kuma tabbatar da cewa babu wata gwamnati da za ta iya fifita son zuciya a kan rayuka da tsaron al’ummar Kenya.” Babban sakataren kungiyar likitocin Kenya, Dr. Davji Bhimji Atellah, ya fada cikin bacin rai cewa, “Ba za mu zauna kallo muna barin Kenya ta zama ‘kebabben tsibiri’ na wadannan cututtuka masu hadari ba. Abin da yake da hadari ga Amurka hadari ne ga Kenya.” Har wa yau, Lauya Miguna Miguna ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa, “Kawo Amurkawa da suka yi cudanya da masu cutar Ebola zuwa Kenya, ko da wane dalili cin amanar kasa ne”. Shi ma wani mazaunin birnin Nairobi, mai suna Robert Kiberenge, ya yi tambayar cewa “Me ya sa Amurka take ganin rayukan Amurkawa sun fi na ‘yan Kenya muhimmanci, har za ta kafa wurin kula da Amurkawa a Kenya?

ADVERTISEMENT

“Hakika, Amurka ta saba da cusa matsalolinta ga kasashen Afirka – duk lokacin da Washington ta ga wani abu mai hadari da ba za ta iya ajiyewa a cikin yankunanta ba, sai ta sami wata kasa ta Afirka da za ta mikawa. A shekarun baya, Amurka ta ci gaba da korar bakin haure, da masu laifi da ba ta son karba, inda ta rika tura su zuwa kasashen Eswatini, da Saliyo da sauran wasu kasashen Afirka. Wadannan mutane masu manyan laifuka barazana ne ga al’umma, ana sanya su a cikin kasashen Afirka masu rauni da rashin wadataccen tsarin lafiya, wanda hakan ke sa al’ummar Afirka shan wahalar matsalolin Amurka, kuma ana take hakkin kasashen na Afirka da rayukan al’ummarsu. Wannan nuna bambanci ya shaida yadda Amurka ke nuna fin karfi, da dorawa kasashen Afirka nauyin da ya wuce na su.

A yanzu, mutane sama da dubu daya ake zaton sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Demokuradiyyar Cango, cutar da tuni ta halaka sama da mutane 200, kuma nahiyar Afirka na bukatar gudummawar kasashen duniya. Babban abin da ake bukata don yakar annoba shi ne sassan kasa da kasa su hada kawunansu, su dauki nauyin tare, a maimakon jefa matsalar ga wasu. Amurka na neman kauracewa daukar nauyin da ke wuyanta, da nuna bambanci game da hakkin dan Adam, bisa yadda ta sha jefa matsalolinta ga nahiyar Afirka. Kamata ya yi sassan kasa da kasa su nuna adawa da irin wannan mataki na nuna fin karfi. Tabbas za a kai ga inganta tsaron al’ummomin duniya, muddin aka daina nuna bambanci, tare da tsayawa kan warware matsalolin da duniya ke fuskanta tare.

LABARAI MASU NASABA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

Kenya
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Xi Ya Bukaci ‘Yan Sandan Sin Su Ci Gaba Da Dukufa Ga Hidimta Wa Jama’a Tare Da Sauke Nauyi Da Nuna Sadaukarwa
  • Sulaiman
    Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya
  • Sulaiman
    Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari
  • Sulaiman
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
Kenya
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Xi Ya Bukaci ‘Yan Sandan Sin Su Ci Gaba Da Dukufa Ga Hidimta Wa Jama’a Tare Da Sauke Nauyi Da Nuna Sadaukarwa
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Tsohon Firaminsitan Jordan: Kasar Sin Tana Kan Gaba Wajen Gudanar Da Fasahar AI A Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Hadin Gwiwar BRICS Na Jagorantar Hadin Kan Kasashe Masu Tasowa Da Dogaro Da Karfin Kansu
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Na Shirin Fadada Samar Da Hidimomin Reno Da Na Kiwon Lafiyar Yara Masu Rahusa

MASU ALAKA

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka
Ra'ayi Riga

Ra’ayin Kasar Sin Kan Fasahar AI Yana Samar Da Damammaki Ga Afirka

September 14, 2026
Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta
Ra'ayi Riga

Taswirar Duniya Mai Adalci: Afirka Ta Ki A Sake “Rage” Girmanta

September 8, 2026
Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin
Ra'ayi Riga

Duk Runtsi, Akwai Mai Ba Da Kulawa Ta Musamman A Kasar Sin

September 4, 2026
Next Post
Babachir Lawal Ya Fice Daga ADC, Ya Zargi Atiku Da Murɗe Zaben Fidda Gwani

Babachir Lawal Ya Fice Daga ADC, Ya Zargi Atiku Da Murɗe Zaben Fidda Gwani

LABARAI MASU NASABA

Xi Ya Bukaci ‘Yan Sandan Sin Su Ci Gaba Da Dukufa Ga Hidimta Wa Jama’a Tare Da Sauke Nauyi Da Nuna Sadaukarwa

Xi Ya Bukaci ‘Yan Sandan Sin Su Ci Gaba Da Dukufa Ga Hidimta Wa Jama’a Tare Da Sauke Nauyi Da Nuna Sadaukarwa

September 15, 2026
NSCDC Ta Kama Ɓarayin Mota, Ta Ƙwato AK-47 A Abuja

NSCDC Ta Kama Ɓarayin Mota, Ta Ƙwato AK-47 A Abuja

September 15, 2026
Gwamnatin Zamfara Za Ta Mayar Da Yara 453,602 Makaranta

Gwamnatin Zamfara Za Ta Mayar Da Yara 453,602 Makaranta

September 15, 2026
’Yan Ta’adda Sun Kai Wa Ƙauyuka 2 Hari A Adamawa

Boko Haram Sun Kashe Mutane 4 Tare Da Ƙone Gidaje A Adamawa

September 15, 2026
Wani Mutum Ya Kashe Kishiyar Mahaifiyarsa A Kogi

’Yan Ta’adda Na Shirin Kai Hare-Hare Makarantu, Wuraren Ibada Da Sansanonin NYSC – ’Yansanda

September 15, 2026
Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Lukuwa Bayan Harin Da Aka Kai Masa

Gwamnatin Sakkwato Ta Rufe Masallacin Sheikh Lukuwa Bayan Harin Da Aka Kai Masa

September 15, 2026
Hannun Jari: Dangote Ya Yi Wa ’Yan Nijeriya Alƙawarin Samun Gaggwaɓar Riba

Hannun Jari: Dangote Ya Yi Wa ’Yan Nijeriya Alƙawarin Samun Gaggwaɓar Riba

September 15, 2026
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12

Arziƙin Dangote Ya Haura Dala Biliyan 50 Bayan Fara Sayar Da Hannun Jarin Matatarsa – Forbes

September 15, 2026
Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

Jawabin Xi A Taron BRICS, Mafita Ce Ga Matsalolin Duniya

September 14, 2026
Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

Duk Wani Yunkuri Na Karfafa Burin Japan Na Fadada Karfin Soji Zai Jefa Yankin Cikin Hadari

September 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.