ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rikicin Masarautar Kano: Sai Shekara Mai Zuwa Kotun Koli Za Ta Yanke Hukunci

by Sani Anwar
5 months ago
Kano

Kotun koli ta sanya ranar 17 ga Afrilun 2027, domin ci gaba da sauraren shari’ar masarautar Kano.

Kwamitin alkalai, karkashin jagorancin mai shari’a Adamu Jauro, ya dage ci gaba da shari’ar, sakamakon jinkirin da aka samu daga bangaran mai kara a ranakun 14 da 15 ga watan Afrilu, maimakon ya sanar tun kafin lokacin.

Wannan kara dai, ta biyo bayan umarnin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta bayar na a mika lamarin ga babbar kotun Jihar Kano, saboda rashin ikon da babbar kotun tarayya ke da shi na sauraren lamarin.

ADVERTISEMENT

Sai dai, hukuncin da aka yanke a kan sabbin kararrakin da ka shigar masu lambobin CA/KN/27M/2025 da CA/KN/28M/2025, kotun daukaka kara ta amince da cewa; bukatar dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke a baya da ke jiran daukaka kara a gaban kotun koli ya cancanta.

Kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa, tun da ya kasance rikicin na sarauta ne, kamata ya yi wata babbar kotun jiha ta yanke hukunci, maimakon babbar kotun tarayya, wadda ta bayyana yin hakan a matsayin wani babban kuskure.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano, a karkashin mai shari’a Abubakar Liman, a ranar 20 ga watan Yunin 2024, ta soke dokar masarautar Kano ta 2024, wadda ta mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16.

Hukuncin farko da babbar kotun tarayya ta yanke, na kallon karar da wani mai ruwa da tsaki a kan lamarin, Aminu Baba-Dan’Agundi ya gabatar, a matsayin wani muhimmin lamari na tabbatar da hakkin bil’adama, sannan kuma ya umarci bangarorin da suka hada da majalisar dokokin Jihar Kano, da su ci gaba da kasancewa da irin wannan matsayi irin na zamanin Sarki Ado Bayero.

Sai dai, kotun daukaka kara a hukuncin da ta yanke, ta bayar da misali da sashe na 251 na kundin tsarin mulkin Nijeriya da kuma sashe na 22(2) na dokar babban kotun tarayya, inda ta ce; batun na sarauta ne da rikicin ‘yan majalisar jiha, don haka ba batun hakki ba ne, ya kamata a gurfanar da shi gaban babbar kotun Jihar Kano ko kuma babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kano
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Katafariyar Kasuwar Kasar Sin Na Samar Da Karin Damammaki Ga Duniya

Katafariyar Kasuwar Kasar Sin Na Samar Da Karin Damammaki Ga Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.