Sabon rikicin shugabanci ya dabaibaye ƙungiyar ‘OK Moɓement’, wani dandali na siyasa da aka kafa don tattara goyon baya ga takarar haɗin gwiwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, da tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso, bayan wani taƙƙamar shugabanci mai tsanani da ya haifar da zargin juna, mayar da martanin zargi da kuma iƙirarin shugabanci daban-daban ga ƙungiyar.
Rikicin ya ƙaru ne bayan da ƙungiyar ta sanar da naɗin tsohon shugaban kwamitin shawara kan haɗakar jam’iyyun siyasa, Peter Ameh, a matsayin darakta janar na ƙasa a wata sanarwa da Jackie Wayas ta sanya hannu a kai.
Wayas, wadda ta bayyana kanta a matsayin babban mai jagorantar wannan ƙungiya, ta ce an ɗauki wannan mataki ne biyo bayan taron kwamitin gudanarwa na ƙungiyar.
Tsohowar mataimakiyar sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC ta ƙara da cewa amincewar da aka yi da naɗin Ameh ta zo ne a haɗin kai saboda ƙwarewarsa a siyasa da jajircewarsa ga ƙa’idodin wannan ƙungiya.
Sai dai, cikin ƴan sa’o’i bayan sanarwar, kalaman sun haddasa cece-kuce bayan wasu mambobin sun tambayi ikon Wayas na kiran kanta a matsayin jagorar a wannan ƙungiya.
Yunƙurin jin bayani daga Wayas kan lokaci da yadda ta karɓi muƙamin bai samu nasara ba, saboda kiran waya da saƙonnin da aka aika mata ba ta amsa ba har zuwa kammala wannan rahoto.
Sabon rikicin ta bayyana batun rashin jituwa na shugabanci a cikin ƙungiyar.
Yayin da yake magana da manema labarai, tsohon sakatare yaɗa labarai na wannan ƙungiya, Justin Ijeh, ya amince cewa akwai rashin jituwa amma ya dage cewa ya kamata a warware su a cikin gida maimakon ta hanyar kafofin watsa labarai.
A yayin da yake mayar da martani ga iƙirarin cewa akwai rikici tsakanin ƙungiyoyin yaƙin nema Obi da Kwankwaso, Tanko ya dage cewa babu wani rikici a tsakani.
Lokacin da aka tambaye shi ya ƙara fayyace rashin jituwar da ke tsakanin ƙungiyoyin ‘Obidients da na OK, Tanko ya yi watsi da lamarin, yana jaddada cewa babu wata rikici ko rashin jituwa a cikin ƙungiyoyin.
“Da gaske babu wani rikici tsakanimmu. Muna ƙoƙarin yin aiki tare. Muna ƙoƙarin tabbatar da cewa muna aiki tare a matsayin ƙungiya ne kawai,” in ji shi.
Bayan ƴan wani lokaci daga bayanin Tanko, mai taimaka wa Obi kan kafofin watsa labarai, Idris Zekeri, ya saki wani bayani yana ƙaryata rahotannin a matsayin ƙarya.














