ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabuwar Manufar Sufuri Ta ‘Dangote Cement’ Na Haifar Da Sakamako Mai Kyau —FRSC

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa ta yaba wa sashen sufuri na Dangote Cement bisa gagarumin ci gaba da sauye-sauye masu anfani da ya samu wajen inganta tsaron hanya, tana mai cewa an samu raguwar haɗurran manyan motocin dakon kaya a faɗin Nijeriya bayan ƙaddamar da sabbin manufofin tsaron sufuri da gyare-gyaren gudanarwa.

Hukumar ta bayyana Dangote Cement a matsayin abin koyi wajen kula da harkokin sufuri da bin ƙa’idojin tsaron hanya, ba kawai a Nijeriya ba har ma a faɗin nahiyar Afirka.

Da yake jawabi yayin wata ziyarar da Dangote Cement ya kai hedikwatar Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa  ranar Talata, shugaban hukumar, Shehu Mohammed, ya yaba wa kamfanin bisa kafa sabbin ma’auni wajen kula da tsaron hanya, tare da ƙarfafa su don su ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da ke sauya fasalin harkokin sufuri a Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Bayanan kwatancen shekarun 2025 da 2026 sun nuna cewa an samu raguwar kashi 56 cikin 100 na haɗurran da suka shafi manyan motocin Dangote Cement, tare da raguwar mace-mace da kashi 36 cikin 100 da kuma raguwar raunuka da kashi 52 cikin 100.

A cewar shugaban hukumar, waɗannan nasarori sun nuna yadda kamfanin ya yi nasarar aiwatar da tsarin nazarin giɓin tsaro da kuma ƙa’idojin cikin gida na kula da tsaron sufuri, waɗanda ya ce sun cancanci sauran masu harkokin sufuri da jigilar kaya a faɗin Afirka su yi koyi da su.

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

Ya ƙara da cewa nasarar Dangote Cement ta ƙara tabbatar da cewa idan manyan kamfanoni suka ba da muhimmanci ga tsaro, alfanun hakan zai amfani ƙasa baki ɗaya da ma nahiyar Afirka.

Tun da farko, shugaban sashen sufuri na Dangote Cement, Murilo Silɓa, ya bayyana irin ci gaba da zuba jari da kamfanin ke yi a sabbin tsarin kula da harkokin sufuri, ciki har da fasahohin bincike ta atomatik da hanyoyin amfani da basirar na’ura mai ƙwaƙwalwa (AI) domin ƙara inganta aiki da tsaron hanya.

Murilo Silɓa ya ce daɗaɗɗen haɗin gwiwar da kamfanin ke yi da Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa  wajen tsarawa da aiwatar da manufofin sufuri yanzu na fara haifar da sakamako mai kyau.

Ya ƙara da cewa baya ga manufofin tsaron sufuri na musamman da kamfanin ke da su, har yanzu suna bai wa sake tantance direbobi da ci gaba da horas da su muhimmanci sosai.

Shi ma Babban Jami’in Lafiya, Tsaro, Muhalli da Ɗorewar Cigaba (HSSE) na Masa’antun, Dr. James Adenuga, ya bayyana cewa waɗannan nasarori sun samo asali ne daga jajircewar shugabanci da cikakken goyon bayan manyan jami’an gudanarwa wajen rungumar sabbin dabaru.

Dr. Adenuga ya jaddada cewa Dangote Cement na ci gaba da mai da hankali wajen inganta ayyukanta ta hanyar gyare-gyare masu ɗorewa, ƙarfafa matakan tsaro da kuma amfani da sabbin fasahohi domin ƙara inganci, bin ƙa’idojin duniya da samar da amfani mai ɗorewa ga masu ruwa da tsaki da al’ummomin da kamfanin ke aiki a cikinsu.

Haka kuma, jami’in kula da tsaron manyan motocin kamfanin a Nijeriya, Ozoɓehe Abraham, ya bayyana cewa kamfanin ya ƙaddamar da sabbin fasahohi domin sanya ido kan yadda direbobi ke tafiya a ainihin lokaci.

Ya ce waɗannan tsarin suna taimakawa wajen tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro, gano direbobin da ke yin haɗari da wuri, da kuma ci gaba da inganta ƙwarewar direbobi.

Ozoɓehe Abraham ya ƙara da cewa a halin yanzu kamfanin na sake tsara da ƙarfafa dokar iyaka gudu a matsayin wani ɓangare na matakan tsaron aiki domin ƙara rage haɗurran hanya da tabbatar da bin doka da aminci wajen jigilar kaya.

Tawagar Dangote Cement da ta kai ziyara hedikwatar Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa sun haɗa da Daraktan Sashen Sufuri, Obajana Hemant Rana (Col. mai ritaya); shugaban binciken ababen hawa kafin tafiya, Charles Theophilus; da Dr. Jibrin Abubakar daga sashen hulɗa da jama’a da yaɗa labarai na kamfanin.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto
Labarai

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja
Labarai

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Next Post
A Yayin Da Babban Bankin Ƙasa (CBN) Ke Yaƙi Da Laifukan Intanet

A Yayin Da Babban Bankin Ƙasa (CBN) Ke Yaƙi Da Laifukan Intanet

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.