ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

A Yayin Da Babban Bankin Ƙasa (CBN) Ke Yaƙi Da Laifukan Intanet

by Darlington Uzodinma and Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
3 months ago

Akwai ƙaruwar damuwa game da tusshen hanyoyin samun kuɗaɗen ƴan ta’adda da sauran ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba. Hasalima damuwar ta zama babban batun da ya shafi ƙasa a yayin da ya bayyana ƙarara cewa wasu marasa kishin ƙasa da kuma masu aikata ɓarna na ba da gudummawa ga ayyukan ta’addanci ta hanyar zama hanyar samar da kuɗaɗen da ake amfani da su wajen aiwatar da miyagun laifuka a bisa ga wata manufar siyasa da ta da zaune tsaye.

Babban abin da ya ƙara ɗaukar hankalin jama’a shi ne yadda tsarin hada-hadar kuɗi na duniya ya ɗauki lamarin da muhimmanci, kuma Nijeriya ba za ta zauna abaya ba, musamman ganin yadda ƙasar ke ƙara zama ɗaya daga cikin cibiyoyin ayyukan ta’addanci.

Ko shakka babu ta’addanci da nau’o’insa kama daga kan fashi da makami da garkuwa da mutane sun sun zama ruwan dare a ƙasar nan a yau suna kuma haifar da tsananin damuwa ga jama’a da iyalansu.

ADVERTISEMENT

Ba sai mutum ya fuskanci irin wannan lamari kai tsaye ba sa’annan zai fahimci irin ƙunchi da illar da hakan ke haifarwa, haka ma ba tare da la’akari da asarar kuɗi ba waɗanda ko da an biya kuɗin fansa babu tabbacin wanda aka sace zai koma gida da ran sa.

A yayin da wannan matsalar ta kai ƙololuwa, an fara zargin cibiyoyin hada-hadar kuɗi wato bankuna da masu harkokin  canjin kuɗi a matsayin waɗanda ake zargin suna taka rawa a lamarin.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

A bisa ga tsananin wannan matsalar, musamman yadda take da matuƙar illa ga tsaron ƙasa, ya sanya hukumomin kula da harkokin kudlɗi da na tattalin arziki cikin matsin lamba domin ɗaukar matakan yaƙi da samar da kuɗaɗen ta’addanci tare da tabbatar da ɗaukar matakan inganta tsaron yanar gizo.

A kan wannan Babban Bankin Ƙasa ya tashi tsaye wajen tunkarar wannan ƙalubale ta hanyar aiwatar da sababbin manufofi da matakai domin tabbatar da tsarin aikinsu da hanyoyin gudanar da harkokinsu ba su gurɓace ba ko fadawa hannun ayyukan da ke barazana ga muradun tsaron ƙasa ba.

Domin cimma wannan buri na tabbatar da ganin ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba, ba su yi anfani da tsarin banki da harkokin kuɗi ba, babban bankin ƙasar ya ƙara tsaurara sa ido kan bankunan ajiya da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi.

Haka kuma Babban Bankin ya gudanar da binciken ba- zata a kan bankunan Nijeriya da rassansu na ƙasashen waje domin hanzarta cire Nijeriya daga jerin ƙasashen da ake sanyawa ido a yadda suke tafiyar da harkokin kuɗaɗe.

Babban Bankin Nijeriya ya ɗauki wannan mataki ne domin samar da ingantaccen yanayin zuba jari, jawo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma ƙarfafa martabar tsarin kuɗi na Nijeriya a idon duniya.

Bugu da ƙari, bankin ya ci- gaba da dagewa wajen ƙarfafa tsaron yanar gizo ta hanyar kafa ingantaccen tsarin sa ido a dukkanin ɓangarorin hada-hadar kuɗi a inda ya umurci bankuna da sauran cibiyoyin da yake kula da su da su gudanar da cikakken nazarin kan su domin auna ƙarfin su na jure hare-haren yanar gizo.

Wannan mataki ya tabbatar da cewa bankunan ajiya, bankunan sabis na biyan kuɗi, ƙananan cibiyoyin ba da rance , kamfanonin turawa da karɓar kuɗi da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi sun bi wannan doka a inda a cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala amfani da sabon tsarin da aka ƙaddamar na kayan aikin tantance ƙarfin tsaron yanar gizo.

Wannan ya haɗa da tsari mai inganci da aka tsara domin tantance yadda cibiyoyin ke fuskantar barazanar hare-haren yanar gizo da kuma ƙarfin su na ɗaukar matakan kariya tare da mayar da martani.

Babban ginshiƙin tsarin waɗannan manufofin shi ne ƙoƙarin samar da ƙwaƙƙwaran sa- ido bisa la’akari da haɗurra daga ɓangaren hukumomin sa- ido.

Babbar manufar wannan tsari ita ce samar da saurin bunƙasar bankin zamani da biyan kuɗi ta hanyar na’ura domin ƙara amincewar masu amfani da ayyukan tare da rage guraben da masu aikata laifukan yanar gizo za su iya kai hari da kuma taƙaita sauran ɓangarori masu rauni a tsarin da ke iya haddasa matsaloli.

Wannan umarni ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan barazanar hare-haren yanar gizo da ke kai hari ga cibiyoyin hada-hadar kuɗi a faɗin duniya, yayin da ƙaruwar dogaro da harkokin kuɗaɗe na zamani, masu samar da ayyuka na waje da kuma tsarin ajiya na gajimare ke ƙara fallasa bankuna ga haɗurra masu rikitarwa da ke ci- gaba da sauyawa.

Ga ɓangaren bankunan Nijeriya, a na sa ran wannan manufa za ta ƙara tsaurara buƙatun bin ƙa’idoji tare da hanzarta zuba jari a fannin kayan aikin tsaron yanar gizo, tsarin shugabanci da kuma hanyoyin kaucewa haɗurra.

Ƙananan cibiyoyi, ciki har da ƙananan bankuna da kamfanonin turawa da karɓar kuɗi na iya fuskantar ƙarin tsadar daidaitawa yayin da suke ƙokarin bin sabbin sharuɗɗan da aka gindaya.

Kamar yadda Babban Bankin Ƙasa ya bayyana, wannan ƙoƙarin hadin guiwar zai tattara cikakkun bayanai kan tsarin shugabanci na tsaron yanar gizo, hanyoyin kiyaye haɗurra, yadda ake mu’amala da masu ba da sabis na waje, ƙarfin mayar da martani ga hare-hare da kuma jimillar ƙarfin jure matsaloli na tsarin aiki baki ɗaya.

A na sa ran sakamakon da za a samu daga wannan aikin zai jagoranci matakan sa- ido na hukumomi tare da ƙarfafa kulawa da dokoki kan haɗurran fasahar zamani a faɗin ɓangaren hada-hadar kuɗi baki ɗaya.

A yayin da babban bankin ƙasa ya ƙaddamar da wannan yunƙuri na yaƙi da haramtacciyar hanyar samar da kuɗaɗen ta’addanci ta hanyar ƙarfafa amincewa da tsarin tsaron yanar gizo, ya dogara kan haɗin kai da gaskiyar cibiyoyin da ke ƙarkashin ikon sa inda bankin ya bayyana matsayinsa a fili cewa za a ɗauki mataki kan duk wani rahoto da aka gano ba daidai ba a ƙoƙarin ɓoye gaskiya.

Masana sun bayyana cewa matakin da Babban Bankin Ƙasa ya ɗauka na iya ƙara ƙarfafa amincewa da tsarin hada- hadar kuɗi ta hanyar tabbatar da cewa cibiyoyin kuɗi sun rungumi matakan kariya masu inganci da tsauri domin daƙile aukuwar hare-haren yanar gizo da ka iya kawo cikas ga ayyuka ko rage amincewar kwastomomi.

Amfani da tsarin gamsuwar abokan ciniki, ya sanya Nijeriya a layi ɗaya da sabbin matakan da duniya ke bi, inda manyan bankuna ke kara mayar da hankali kan ƙarfafa tsaro a tsarin harkokin kuɗi domin tabbatar da kwanciyar hankali a fannin hada-hadar kuɗi, musamman yayin da harkokin kuɗi na zamani ke ƙara faɗaɗa a ƙasashe masu tasowa

A kan wannan a bayyane yake Babban Bankin Ƙasa bai yi ƙasa a guiwa ba domin ya ƙara ƙaimi wajen aiwatar da matakan yaƙi da safarar kuɗaɗen haram da kuma tabbatar da tsaron yanar gizo.

Haka kuma Babban Bankin ya ƙara tsaurara sa- ido tare da gudanar da binciken ba- zata a kan bankunan Nijeriya da rassansu a ƙasashen waje domin hanzarta fitar da Nijeriya daga jerin ƙasashen da aka sa wa idanu. Waɗannan matakai na da manufar samar da ingantaccen yanayin zuba jari, jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje, da kuma ƙara ɗaukaka martabar tsarin kuɗi na Nijeriya a idon duniya.

Darlington Uzodinma
+ posts Bio
    This author does not have any more posts.
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ posts Bio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22

Yadda Arsenal Ta Lashe Gasar Firimiya Bayan Shekara 22

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.