ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
3 weeks ago
Sakkwato

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan ƙaruwar ayyukan ta’addanci a Jihar Sakkwato tare da cewar wajibi ne gwamnati ta kawo ƙarshen kisan kiyashin da ake yi wa jama’a. 

Atiku, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya bayyana cewa abin takaici ne kisan gillar da ɓarayin daji suka yi wa mutane 32 a Sakkwato ba tare da sun aikata ko wane irin laifi ba.

A jawabin da ya fitar, Atiku ya ce kashe- kashen sun zama tamkar ruwan dare, lamarin da ke ban tsaro wanda bai kamata gwamnatin da ta kasa kare ƴan ƙasarta ba, babu alfanu fitar da sanarwar jaje bayan kowanne kisan gilla ba tare da ɗaukar ƙwaƙƙwaran matakin shawo kan matsalar ba.

ADVERTISEMENT

A makon jiya ne ɗaruruwan ɓarayin daji suka shiga garin Ungushi da ke ƙaramar hukumar Keɓɓe da ke Kudancin Sakkwato, suka ɗauki rayukan mutanen a yayin da suke Sallar Juma’a. 

Majiyoyi da dama sun bayyana cewar ɓarayin dajin sun fara kai hari ne a cikin garin Keɓɓe, inda suka fatattaki jami’an tsaro da al’ummar garin tare da fashe shaguna da awon gaba da dabbobi, daga bisani kuma suka kutsa kai a cikin ƙauyuka. 

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Wani shugaba a yankin wanda ya halarci jana’izar da aka gudanar ranar Lahadi, ya ce mazauna yankin sun gano tare da bizne gawarwakin mutane 32, ya kuma bayyana cewa mazauna yankin sun kashe mutane 13 daga cikin maharan a yayin artabun da aka shafe tsawon lokaci. 

Atiku ya jaddada cewar babban aikin gwamnati shi ne, kare rayukan al’umma, don haka ƴan Nijeriya ba za su ci gaba da bizne ƴan‘uwansu ba, yayin da waɗanda aka ɗora wa alhakin tsaron suke ta bayar da uzuri.

“Zuciyata na tare da iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma al’ummar Jihar Sakkwato, amma ta’aziyya kaɗai ba ta isa ba. Mutane nawa ne kuma za a kashe kafin gwamnati ta ɗauki kare rayukan ƴan ƙasa a matsayin abin gaggawa?” cewar Atiku. 

Sakkwato
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Mata Masu Yoyon Fitsari Ke Rayuwa Cikin Ƙunci A Arewa

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Sin Da Kasashen Afirka Na Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Fasahohin AI

Sin Da Kasashen Afirka Na Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Fasahohin AI

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.