Hadurran kwale-kwale sun zama babbar barazana ga rayukan al’ummomin da ke zaune a yankunan da koguna suka ratsa, lamarin da ke haddasa asarar dimbin rayuka da dukiyoyi, musamman a wannan lokaci da har yanzu jama’a ke dogaro da kwale-kwale a matsayin muhimmiyar hanyar sufuri.
A yankin Sakkwato daga Shagari zuwa Goronyo zuwa wasu kananan hukumomin da ke makwabtaka da kogin Rima a baya- bayan nan an sha samun rahotannin nutsewar kwale-kwale dauke da al’umma da dama musamman manoma, ’yan kasuwa da sauran matafiya.
Galibi ‘yan kasuwa da manoma a kauyuka da dama kan dogara kacokam wajen amfani da hanyoyin sufurin jiragen ruwa wajen zuwa kasuwanni da gonaki lamarin da ke jefa rayukan su a cikin hadari.
A kan wannan jama’a na ci- gaba da nuna damuwa yadda ake samun yawaitar hadurran kwale-kwale a yankin Sakkwato da ke cin rayukan dimbin al’umma ba tare da shawo kan matsalar ba.
Kasawar gwamnatoci wajen samar da hanyoyin mota da hada kauyuka da gadoji ne dalilin da yasa garuruwa da dama ba su da zabi face amfani da jiragen ruwa musamman na katako wajen sufurin da ke jefa rayukan su a cikin hatsari.
A kowace shekara a kan samu hadurran jiragen kwale- kwale da dama wadanda galibi daruruwan al’umma kan rasa rayukan su bisa ga sakaci da yi wa jirgi lodin da ya wuce kima.
A shekarar 2024 kadai an samu asarar rayuka sama da 400 a tsakanin watan Yuli da Disamba 2024 wadanda suka faru a dalilin rashin kwarewa da rashin amfani da matakan kariyar sufurin ruwa
Jihohi 28 ne ke da manyan kogunan da ke da alaka da juna a fadin kasar nan wadanda ke da tsawon sama da kilimita dubu 10, kuma suna karuwa da tsawon kilomita dubu 3, 800 a kowace shekara kamar yadda Hukumar kula da Hanyoyin Ruwa ta Kasa ta bayyana.
Kididdiga daga hukumar bincike da kiyaye hadurra (NSIB) ta bayyana cewar fiye da kashi biyu bisa uku na hadurran da ake samu a jiragen ruwa kan faru ne a dalilin nutsewa da mutane ke yi saboda rashin amfani da rigar kariya.
Mummunan hadarin kwale-kwale da ya faru a kogin Goronyo da ke jihar Sakkwato a kwanan nan ya girgiza al’umma musamman yadda rayuka 65 suka salwanta, lamarin da ya jefa iyalai cikin alhini tare da jefa tambaya kan dalilin yawaitar hadurran jiragen ruwa a yankin.
Fasinjojin jirgin sun hadu da hadarin ne a ranar Alhamis din makon jiya a lokacin da kwale-kwalen ya kife da su, sai dai matukin jirgin da hakimin kauyen na daga cikin wadanda suka tsira da rai.
Kafin dakatar da aikin ceton a ranar Alhamis saboda duhu, an riga an gano gawarwaki 53 amma bayan an ci-gaba da aikin neman mutanen ranar Juma’a, an sake gano wasu gawarwaki, lamarin da ya sa adadin wadanda suka mutu ya kai 65.
Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin kwale-kwalen, akwai ’yan gida guda har 11, lamarin da ya kara bayyana girman musibar da ta fadawa al’ummar yankin wadda ta shiga cikin kundin tarihin lamurra mafi muni.
Hukumar kula da hanyoyin ruwa ta tabbatar da cewar mutane 11 ne suka tsira, ciki har da Hakimin Gorau, Alhaji Na- Batsami Gorau, kuma tuni an yi jana’izar wadanda suka rasa rayukan su bisa tsarin addinin Musulunci.
Hatsarin ya sake jawo hankalin jama’a kan matsalar tsaron hanyoyin ruwa a Nijeriya, musamman a yankunan da ke kusa da koguna, inda mutane ke amfani da kwale-kwale a matsayin hanyar sufuri zuwa gona da wajen kasuwanci.
Duk da jami’an da ke aikin ceton gaggawa sun ci- gaba da bincike a hanyoyin ruwan domin neman mutanen da ka iya kasancewa a cikin ruwan, sai dai a bisa ga yadda lokaci ke ke tafiya, babu tabbacin sake samun wasu mutanen da suka tsira.
Da yake tsokaci kan hatsarin, Shugaban Hukumar Gudanarwar Hanyoyin Ruwa ta Kasa, kuma tsohon Ministan Ruwa, Mukhtar Shehu Shagari, ya bayyana hatsarin a matsayin babban abin jimami maras iyaka.
Shagari ya yi kira ga masu tuka jiragen kwale-kwale da fasinjoji da su rika bin dokokin tuki da shiga ruwa yadda ya kamata. Ya ce bai kamata irin wannan mummunan hatsari ya zama abin da ake yawan samu a harkar sufurin ruwa a Nijeriya ba.
A shekaru biyu da suka gabata, gwamnatin jihar Sakkwato ta bayyana cewar za ta siyo jiragen ruwa na zamani da rigunan kariya na naira bilyan 1 da miliyan 100 domin rabawa ga kananan hukumomi 22 cikin 23 da suka fuskanci ambaliyar ruwa,.
Sai dai har zuwa yau ba a sake jin batun labarin kwangilar ba wadda Kwamishinan Kananan Hukumomi, Dadi Adare ya bayyanawa manema labarai a sakamakon zaman majalisar zartaswar gwamnatin jiha da Gwamna Ahmed Aliyu ya jagoranta.
A tattaunawarsa da manema labarai, dan majalisar da ke wakiltar mazabar tarayya ta Gada/Goronyo, Hon. Bashir Usman Gorau, ya bayyana cewar akwai babbar matsala da ta shafi kogin Goronyo da hanyoyin ruwansa da ke bukatar Gwamnatin Tarayya ta gaggauta daukar mataki domin hana sake faruwar irin wannan musibar.
Gorau ya ce laka da tarkacen da suka taru a cikin kogin Goronyo da hanyoyin ruwansa babbar matsala ce da ke haddasa kifewar kwale-kwale wanda ya kamata gwamnatin tarayya ta kwashe su. Ya ce laka da tarkace da suka taru tsawon shekaru sun rage yawan ruwan da kogin zai iya dauka, kuma hakan na iya kara haifar da ambaliyar ruwa da sauran matsalolin ruwa a yankunan da ke kewaye.
A cewar dan majalisar, Gwamnatin Tarayya ce ta gina Dam din Goronyo sama da shekaru 50 da suka gabata don haka a tsawon shekaru, laka da tarkace masu yawa sun taru a cikin dam din, abin da ya rage karfinsa da kuma jefa al’ummomin da ke dogaro da shi cikin hadari.
Dan majalisar ya kuma nuna damuwa da cewar ci- gaba da gurbacewar kogin da hanyoyin ruwansa na iya kara jefa al’ummomin cikin hadari a lokacin damina wanda hakan na iya haifar da ambaliya, lalata dukiyoyi, tilasta mutane barin gidajensu da kuma sake rasa rayuka.
Haka ma bincike ya nuna cewar rashin kulawa da jiragen kwale- kwalen da rashin kiyaye dokoki, da rashin saka rigunan kariya na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen haddasa hadurran jiragen ruwa a yankin.
A ire- iren hadurran kwale-kwalen jama’a da dama kan ji raunuka, wasu kan fita hayyacin su, bacewar wasu a yayin da wasu kan yi bankwana da duniya bakidaya ba tare da ceton rayukan su ba.
Mahukunta kan sha alwashin daukar kwararan matakai domin shawo kan aukuwar hadurran ko magance mace- macen amma alwashin a fatar baki ne kawa domin bai tabbata ba.
A mafi yawan garuruwan da koguna da hanyoyin ruwa suke, jiragen ruwa ne hanyar sufurin su amma kuma zirga- zirgar su na zama cikin hadari kamar yadda ake gani a bisa ga yawaitar hadurra da asarar rayuka.
Kadan daga cikin hadurran jiragen ruwa na baya- bayan nan sun hada da a Yuni 2025, wani hatsarin kwale-kwale ya faru a Kambama da ke karamar hukumar Shagari, inda kwale-kwalen ya kife a kusa da Rinaye kuma ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai, lamarin da ya kara jefa al’ummar yankin cikin fargabar tafiya a ruwa.
Bugu da kari a Agusta 2024, wani kwale-kwale ya kife a yankin Dundaye da ke karamar hukumar Wamakko yayin da yake dauke da manoma da ke tafiya zuwa gonakinsu a Kogin Rima dauke da fiye da mutane 35, inda cunkoso ne daya daga cikin abubuwan da aka alakanta da hatsarin wanda akalla mutane 10 suka rasa rayukansu.
A Agusta 2025 an samu gagarumin hadarin kwale-kwale a kogin Goronyo a yayin da jirgin na katako ya nutse da mutane 50 wanda ya girgiza al’umma wanda aka ceto mutane 41, sai dai shekara daya bayan hadarin al’umma ba su dauki da darasin kiyaye ka’idojin ba musamman lodin da bai wuce kima ba.
Haka ma an samu wani hatsarin a karamar hukumar Sabon- Birni inda rahotanni suka tabbatar da mutuwar mutane shida, aka ceto 21, yayin da wasu uku ruwa ya tafi da su.
Hukumar kula da hanyoyin jiragen ruwa wadda ke da alhakin kiyaye koguna da hanyoyin ruwa a Nijeriya ta bayyana matakan da ya kamata a dauka domin kiyaye hadurra wadanda suka hada da zirga-zirga a tsakanin shida na safe zuwa shida na yamma a kowace rana, haka ma wajibi ne matukan jiragen ka da su yi lodi ya wuce kima.
Hukumar ta ce matukan jirgin su guji amfani da tsofaffin jirage musamman wadanda suka wuce shekaru biyar, bugu da kari matukan jirgin su guji shan barasa ko kwaya kafin da yayin tuka jirgi haka ma wajibi ne fasinjoji su saka rigar kariya kafin shiga jirgi.
Sauran hanyoyin kariyar da hukumar ta bayyana sun hada da wajibi ne dukkanin jirage da matuka jiragen suna da rajista da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa, masu tuka jirgin su rika duba lafiyar jiragen akai- akai haka ma matuka jirgin su rika sanar da fasinjoji matakan kariya.
A kan yawaitar samun wannan matsalar, Shugaban Kasa Tinubu ya bayyana cewar gwamnati ba za ta sa idanu ta ci- gaba da ganin rayukan al’umma na tafiya haka kawai ba a bisa ga sakaci ko rashin sani, a cewarsa bin ka’idojijn kiyayewa ba zabi ba ne wajibi ne.
Tinubu ya ce abin damuwa ne yadda hadurran ke ci-gaba da faruwa duk da ilmantarwarwa a kodayaushe da ma’aikatar muhalli, ma’aikatar tattalin arzikin teku da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa ke yi.
A kan wannan ya bukaci sarakuna, shugabannin addini da kananan hukumomi da su kara wayar da kan al’umma kan bin ka’idojijn kiyayewa musamman a hanyoyin ruwa, ya ce yana da kyau jama’a su fahimci cewar a na iya kiyaye hasarar rayukan da ake yi.














