ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, September 8, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Rikici Ya Tsananta Tsakanin Dan Daba Da Malaman Addini A Sakkwato

by Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
1 week ago
Rikici

Takaddamar ikirarin kisan fitaccin Malaman Addini biyu a Sakkwato, Sheikh Musa Ayuba Lukuwa da Malam Murtala Bello Assada da rikakken dan daba Dahiru Mai- Barewa ya yi ta tayar da kura tare da daukar hankalin al’ummar ciki da wajen Birnin Shehu.

Tuni barazanar halaka Malaman ta haifar da ce-ce- ku-ce musamman kan girman matsalar, yunkurin daukar doka a hannu, kalubalen tsaro, rashin jin amon manyan malamai da kuma matsayin hukumomi kan wanzar da zaman lafiya da kare rayukan al’umma a Cibiyar Daular Usmaniyya.

A bidiyoyi daban – daban da suka bazu a kwanakin nan sun hasko Mai- Barewa yana barazanar kashe Sheikh Musa Lukuwa da Mallam Murtala Assada kan batun makomar iyayen manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, kalaman da suka harzuka al’ummar Musulmi da tayar da jijiyar wuya.

ADVERTISEMENT

A mabambantan bidiyo Mai- Barewa wanda da farko ya fara da kalubalantar Lukuwa da ya fito su yi mukabala daga baya kuma ya bayyana cewar jinin Lukuwa da Assada sun halasta saboda suna batanci ga iyayen manzon Allah amma kuma a wani bidiyo dan ta’addan ya bayyana cewar dalilin da yasa yake kokarin halaka Malaman shine saboda suna sukar Majalisar Sarkin Musulmi da gwamnatin Sakkwato.

Hazo ya tashi a sararin samaniya ne musamman ganin Mai- Barewa kan sara ko babu gaba, hasalima bai jiima da fitowa daga gidan gyaran hali ba a dalilin kisan kai tare da kwashe shekaru shida a gidan maza gabanin samun afuwa daga gwamnati.

LABARAI MASU NASABA

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

Haka ma dimbin matasa sun yi ikirarin daukar mataki irin na Mai- Barewa a kan Lukuwa domin a cewar su ba za su zuba idanu suna kallon a na taba daraja da mutuncin fiyayyen halitta ba.

Sheikh Lukuwa wanda ke da dubban mabiya shine Malamin Assada wanda ake ganin yana goyon malaminsa kuma akwai takun saka tsakaninsa da Majalisar Sarkin Musulmi musamman kan abin da ya shafi rashin biyayya ga umurnin Sarkin Musulmi a sha’anin ganin watan azumin Ramadan, lamarin da Malamin ke gudanar da Sallar Idi ba tare da mafi yawan al’ummar Musulmi ba. Bugu da kari yadda ya jagoranci cin neman doki a Sakkwato a shakarun baya ya tayar da kura sosai.

Al’ummar Musulmi sun dade suna bayyana damuwa kan akida da koyarwar Sheikh Lukuwa, musamman yadda ake ganin wasu daga cikin kalamansa da matsayarsa kan al’amuran addini ke haddasa ce-ce-ku-ce da rarrabuwar kai a tsakanin al’umma, maimakon su taimaka wajen samar da fahimtar juna, maslaha da hadin kan Musulmi.

Sheikh Assada kuwa ya yi fice wajen yaki da zalunci ta hanyar tsage gaskiya ga masu rike da madafun iko musamman kan abubuwan da suka shafi wajibcin gwamnatii wajen sauke hakkin al’umma da kare rayukan su a wa’azozin da yake yi na yaki da azzuman shugabanni da barayin daji da ke cin karen su ba babbaka.

A gwamnatocin jiya da yau duka Assada bai taba kasa a guiwa wajen suka da caccakar su ba kan rashin daukar kwararan matakan da suka kamata domin kawo karshen ayyukan ta’addanci wadanda ya ce idan har da gaske ake yi to da tuni matsalar ta zama tarihi.

A bisa ga yadda Assada ya jajirce wajen suka da caccakar ayyukan ta’addanci; a lokuta da dama an ji hatsabibin jagoran barayin daji, Bello Turji yana aika sako kai tsaye ga Malamin a kan ya shiga taitayinsa ko su kawo karshen sa. Hasalima a baya an yi yunkurin halaka Malamin a wani farmaki da aka kai a gidansa wanda ya bayyana cewar ‘yan ta’addan birni ne wadanda yake kira da Turazzan birni.

Musabbabin rikicin ya faru ne kan wani hadisi da Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya ambata game da iyayen Annabi Muhammad (S.A.W) da yake a matsayin batanci wanda ya rikide zuwa ce-ce-ku-ce tsakanin malaman addini da al’umma a Sakkwato, lamarin da daga bisani ya kai ga barazanar kisa daga gawurtaccen dan daba Dahiru Ma-i Barewa.

Wasu daga cikin al’ummar Musulmi, sun dauki yadda Malamin ya gabatar da kalaman a matsayin abin da ya sabawa martabar Shugaban Halitta, lamarin da ya haifar da muhawara da suka daga wasu bangarorin malamai da matasa.

Sai dai Sheik Lukuwa ya dage kan cewa batun na ilimi ne, kuma ya kamata a tattauna shi da hujjojin ilimi maimakon a mayar da shi wata takaddama ta daban don haka ya bukaci zama na musamman  a kai.

A bisa ga wannan matsayar, Lukuwa ya nemi a yi mukabala domin a tattauna batun cikin hujjoji da dalilai na ilimi, yana mai jaddada cewa harkar ilimi ya kamata a warware ta da ilimi.

A kan wannan, kungiyar matasan dalibai ta aika da takarda dauke da kwanan wata 19 ga Agusta wadda ta aika ga hukumomin tsaro a jihar ta na cewar ta karbi gayyatar Lukuwa domin warware matsalar tare da fatar zaman zai kasance wata dama ta musayar ilimi, bayyana hujjoji da fahimtar da juna a tsakanin bangarorin da lamarin ya shafa.

Gamayyar kungiyar ta bayyana cewar ba manufar su ba ce haifar da rikici ko kiyayya da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar jihar ba, illa dai suna da burin ganin an gudanar da tattaunawar a cikin kwanciyar hankali, adalci da mutunta juna tare da bin ka’idojin tattaunawar Ilimi.

Sai dai duk da cewar Malamin ya karbi takardar amma kuma daga baya ya ce ba zai yi mukabalar da kungiyar ba saboda ba su kai matsayin da zai yi mukabala da su ba. Wadanda suka kai masa takardar sun bayyana mamakin dalilin da yasa Malamin zai ce bai karanta takardar da ya sawa hannu ba tare da canza ra’ayinsa ga bukatar da ya nema da kan sa.

Batun dai ya fara wuce iyakar muhawarar ilimi, inda wasu daga cikin masu goyon bayan bangarorin suka shiga kafafen sada zumunta da mabambantan ra’ayoyin su, lamarin da ya kara tayar da kura.

A nasa bangaren, Malam Murtala Assada, wanda dalibin Lukuwa ne, kuma wannan alaka ta dalibi da malami ta sa wasu ke ganin cewa matsayar malaman biyu kan batutuwan da suka shafi addini ta na da kusanci don haka wasu ke ganin duka matsayin su daya.

Sai dai Assada ya bayyana cewar ko kadan babu kamshin gaskiya a abin da ake alakanta shi da shi domin ya bayyana cewar bai yi kalaman ba kuma yana kalubalantar a gabatar masa da hujjar kalaman da ake cewa ya yi, amma kuma ya ce za a iya zama da Lukuwa domin tattaunawar ilimi kan batun.

Malamin ya bayyana cewar babu kamshin gaskiya a zancen kamar yadda ya bayyana da cewar “Duk mai hankali ya san karya ce, idan Lukuwa ya yi maganar, to me ya kawo sunan Assada cikin wadanda za a kashe? don haka karya ce kawai.

A wata hira da RFI Hausa da aka yada kwanan nan, Malam Murtala Asada ya yi magana kan barazanar da yake fuskanta a inda ya zargi mahukunta a jihar da yin biris da lamarin duk da korafin da suka kai a hukuman ce.

A tattaunawar, Assada ya bayyana cewar Ma-  Barewa ya yi ikirarin kashe su a cikin bidiyo 14 don haka suka kai korafi ga hukumomin tsaro amma Kwamishinan ‘Yan Sanda ya hana su gan shi, ya ce su kai korafi ga Ma’aikatar Lamurran Addini ita kuma ta gabatar da korafin ga rundunarsa amma ya ce hukumar tsaron farin kaya ta saurare su kuma ta mutunta su.

Ya ce bayan ganin barazanar ya yi sanarwar lokacin karatunsa kuma ya aika goron gayyata ga Mai- Barewa amma da sharadin idan ya je wajen wa’azin sai dai uwarsa ta haifi wani cewar Malamin wanda ya fitar da wani bidiyo yana atisaye da bindiga.

Malamin ya ce a bayyane yake yana takun saka da gwamnatin jihar Sakkwato shi kuma Lukuwa yana takun saka da Majalisar Sarkin Musulmi don haka idan ma an kashe su babu wani mataki da za a dauka.

Da yake tsokaci kan lamarin, Alkalin Malaman Sakkwato, Malam Ahmad Umar Helele ya bayyana cewar hayagagar ta haifar da cece-kuce da tayar da hankalin al’umma wanda ko kadan bai kamata ba.

Ya ce jama’a ba su da wata hujja kan abin da suke fada domin matsalar Ilimi a bar ta a hannun Malamai yana cewar ko a baki Lukuwa ya yi magana ba zai karyata shi ba ballantana ya kawo hadisi amma kuma ya ce kuskure ne bayyana abin da zai tunzura jama’a tare da haddasa cece-kuce don haka bai kamata Lukuwa ya yi magana kan abin da babu wanda ya tambaye shi ba.

A yayin da yake tofa albarkacin bakin sa kan takaddamar, daya daga cikin mlamam addinin Musulunci a Sakkwato, Malam Murtala Bello Da’a ya bayyana cewar kalaman Lukuwa sun yi matukar muni wadanda furta su ke da matukar hadari.

Ya ce maslaha daya shine gwamnatin jihar Sakkwato ta shirya mukabala domin malamai su zauna su kalubalance shi. Ya ce shirya mukabala kan kare martaba da mutuncin manzon Allah (SAW) ya fi gwamnatin jihar Sakkwato ta kashe naira biliyan 100 wajen gyaran masallacin Shehu Dan-Fodiyo da na Sarkin Musulmi Muhammadu Bello.

A wannan makon ne hukumomin tsaro suka gurfanar da Mai- Barewa a gaban kotu kan wannan takaddamar kuma kotun ta bayar da umarnin a tura shi gidan maza domin ci- gaba da tsare shi yayin da ake ci- gaba da bincike da kuma bin matakan shari’a. Haka ma dimbin matasa sun gudanar da zanga- zangar neman a saki dan dabar tare da Allah -wadai da Malaman suna cewar babu hujjar kama matashin alhali ba a dauki matakin kan wadanda suka tayar da zaune tsaye ba.

A zahiri, rashin daukar kwakkwaran matakin magance matsalar daga gwamnatin jihar Sakkwato, kungiyoyin addini da kuma Majalisar Sarkin Musulmi, na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen tsawaita wannan ce-ce-ku-ce, lamarin da ya ba da damar ruruta wutar rikicin da sabanin fahimta su ci- gaba da yaduwa ba tare da an samar da mafita mai dorewa ba kamar yadda jama’a ke bayyanawa.

Rikici
Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
+ postsBio
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    2027:Cece-kuce Ta Barke Tsakanin Tinubu Da Atiku
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Dalilin Yawaitar Haduran Kwale-kwale A Yankin Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Atiku Ya Koka Kan Ƙaruwar Ta’addanci A Sakkwato
  • Sharfaddeen Sidi Umar, Sokoto
    https://hausa.leadership.ng/author/sharfaddeen-sidi-umar-sokoto/
    Yadda Mata Masu Yoyon Fitsari Ke Rayuwa Cikin Ƙunci A Arewa

MASU ALAKA

Gwamnatin Neja Ta Bayar Da Umarnin Kawo Karshen Matsalar Tsaro
Rahotonni

Karuwar Farin Jinin Gwamna Umaru Bago A Siyasar Jihar Neja

September 5, 2026
Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed
Rahotonni

Kyakkyawan Tsarin Laken Asiri Zai Dakile Shirin Magudin Zabe A Nijeriya —Mohammed

September 5, 2026
Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
Rahotonni

Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki

September 5, 2026
Next Post
Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026
Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

Xi Ya Zanta Ta Wayar Tarho Da Firaministan Birtaniya

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.