ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sarki Sanusi Ya Nemi Tinubu Ya Sauya Salon Tafiyar Da Mulkin Kasar Nan

by Sani Anwar
4 months ago
Sanusi

Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya ce; Nijeriya na bukatar a gaggauta samar da dabaru da tsare-tsare na kasa, domin amfani da fasahohin da ke bullowa, musamman fasahar kere-kere,  don samun ci gaba mai dorewa.

Sanusi ya bayyana haka ne, a wajen taron shekara 8 na kwamitin shugabannin jami’o’i mallakar jihohi a Nijeriya da aka gudanar a Kano.

“Wannan kasa tana bukatar dabaru da sabbin tsarin siyasa tare da bukatar kyakkyawan shiri, musamman a wannan karnin da muke ciki,” in ji shi.

ADVERTISEMENT

Sarkin ya bukaci jami’o’in Nijeriya da su samar da taswirar fasahar zamani ta ‘AI’ na kasa, yana mai jaddada cewa; dole ne cibiyoyin su kasance kan gaba wajen koyarwa da bincike, domin tsara manufofin da ke kawo ci gaban kasa.

Har ila yau, ya yi gargadin cewa; Nijeriya na fuskantar barazanar samun koma baya, kamar sauran kasashe, ciki har da Ghana, da ta riga ta kirkiro tare da fara aiwatar da ingantattun dabarun AI da nufin horar da matasa, bunkasa bayanai da kuma sauyin tattalin arziki.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Sanusi II ya jaddada matsayin jami’o’i a matsayin ginshikan kungiyoyin farar hula, inda ya ce; dole ne cibiyoyin ilimi su ba da gudummawarsu wajen gabatar da jawaban kasa kan harkokin mulki, tattalin arziki, kimiyya da fasaha.

Ya kuma yaba wa gwamnatocin jihohi, bisa yadda suka fahimci muhimmancin shugabannin jami’o’in, wajen tsara alkiblar manufofi da kuma karfafa shugabanci a jami’o’i.

Tun da farko, Shugaban COPSUN, Ayodeji Omole, ya ce; taron ya nuna bukatar ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakanin masu ruwa da tsaki, domin magance kalubalen da jami’o’in gwamnati ke fuskanta.

Haka zalika, ya yi nuni da cewa; tare da irin wadannan cibiyoyi sama da 60 a fadin kasar nan, yin aiki akai-akai, na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da daidaiton manufofi da hada kan hukumomi da kuma inganta harkokin mulki.

Omole ya kara da cewa, dole ne jami’o’i su dace da abubuwan da suke faruwa a duniya, ciki har da ci gaban fasaha da kuma sauya bukatun tattalin arziki, ta hanyar kirkire-kirkire da tsare-tsare.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Suleiman Wali Sani, ya ce; gwamnatin jihar ta bai wa ilimi fifiko a matsayin babban ginshikin ci gaba.

Gwamnan ya ce, taron ya bayar da dama ga masu ruwa da tsaki, wajen samar da hanyoyin da za a bi domin inganta tsarin tafiyar da jami’o’i, kudade, kirkire-kirkire da kuma matakan ilimi.

Sanusi
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Kasar Sin Ta Amince Da Kaya Na Farko Da Aka Shigo Da Su A Karkashin Manufar Soke Haraji Ga Kayayyakin Afirka

Kasar Sin Ta Amince Da Kaya Na Farko Da Aka Shigo Da Su A Karkashin Manufar Soke Haraji Ga Kayayyakin Afirka

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.