ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shettima Ya Nemi Hadin Kan Kafafen Yada Labaru Domin Samar Da Ci Gaba

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
5 months ago
Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya nemi hadin kan kafafen yada labaran Nijeriya domin samar da ci gaba tare da gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da manhajojinsu wajen karfafa dimokuradiyyar kasa ta hanyar aikin jarida mai amfani da tunani mai zurfi.

Ya ce al’umma ba ta lalacewa saboda rashin ra’ayoyi, amma saboda rashin maza da mata masu kwarin gwiwa don bincikan ra’ayoyi da gwada su da hankali da kuma tambayoyi masu wuya wadanda ke ceto mutane daga bin ra’ayoyinsu na hankali.

  • Ba Za A Iya Daidaita Batun Mashigin Hormuz Ba Har Sai An Kawo Karshen Yaki
  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da ‘Yan Nijeriya 1,231 Daga Jamhuriyar Nijar A Mako Daya

A cewar wata sanarwa daga mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, Sanata Shettima ya yi jawabi a jiya a Abuja yayin kaddamar da wani littafi da bikin shekaru 60 na haihuwar kwararren dan jarida, Mista Babajide Kolade-Otitoju.

ADVERTISEMENT

Ya yaba wa gudunmawar Babajide ga aikin jarida da tunanin mai zurfi, yana mai cewa shirin talabijin dinsa da aka fi sani da “Journalists Hangout,” ya samu damar habaka bincike a Nijeriya.

Dangane da rawar da kafofin watsa labarai ke takawa wajen karfafa dimokuradiyya, mataimakin shugaban kasa ya ce, “Ma’aunin kowace dimokuradiyya shi ne, ba wai gudanar da zabe ba ne kawai, akwai wayar da kan da jan hankai na kafofin watsa labarai. Dimokuradiyya na dogara ne ga kafofin watsa labarai da ke sanin lokacin tambayoyi, lokacin gargadi, lokacin bayar da misalai da lokacin kauce wa rikice-rikice abokan hulda.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

“Komai yana lalacewa ne idan ba a yin tambayoyi a kansa. Matsayi yana lalacewa. Hukumomi na lalacewa. Tattaunawar kasa tana lalacewa. Ko gaskiya da kanta na iya yin shiru idan aka bar karya tare da kalubalantarta ba. Kafofin watsa labarai ba wurin hayaniya ba ne. Sun kasance wajen fadakar da al’umma.”

Mataimakin shugaban kasa Shettima ya yi wa Babajide yabo mai girma a ranar haihuwarsa ta shekara 60, yana bayyana shi a matsayin mutum wanda ya mayar da bincikan abubuwan da suke amfanan rayuwar al’umma domin su samu mafita daga abubuwan da suka shige musu duhu.

Ya ce Babajide cikakken misali na irin wadannan maza da mata da ya kamata a samu, har ma da bayyana shi a matsayin mai inganta dimokuradiyya wanda ya cancanci a yi bikin zagayowar haihuwarsa.

“A yau, yayin da muke bikin zagayowar ranar haihuwarka ta shekara 60 da gabatar da littafinka, muna girmama abubuwan da ka gabatar a cikin wadancan shekarun.

“Muna girmama sana’ar da kuka daraja, wata kafa da kuka daga darajarta, da tattaunawa mai zurfi da kuka taimaka wajen raya ta a kasarmu. Haka kuma muna girmama shawararku ta rubutu, don tuna abubuwa, da barin wani tarihi na rayuwa da aka sadaukar don tunani,”.

Ya kara yabawa Kolade-Otitoju saboda sadaukar da rayuwarsa ga aiki mai wahala domin al’umma su amfana. Ya jaddada cewa ba karamin aiki ba ne yin aiki a matsayin dan jarida tsawon shekaru tare da kare mutuncinsa har yanzu.

“Wannan ba karamin nasara ba ce. Yin shekaru da dama a aikin jarida tare da kiyaye gaskiya ba karamin namijin kokari ya yi ba, kuma har yanzu yana nan a kan turbarsa ta asali, wata gagarumar nasara ce,” ya kara da cewa.

A nasa bangaren, shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya kuma Gwamnan Jihar Kwara, Alhaji Abdulrahman AbdulRazak, yayin da yake yaba halayen wanda ake taya shi murnar zagayowar shakarar haihuwa, ya yi kirari da kafafen yada labarai saboda gudummawar da suke bai wa dimokuradiyya da ci gaban Nijeriya.

A nasa bangaren, Farfesa Kyari Mohammed, ya ce littafin mai babi tara yana dauke da aikin kwarewar Babajide-Otitoju da aikinsa a matsayin dan jarida da ya yi fice a duniyar wajen buguwa da watsa shirye-shirye, yana nuna zurfin kwarewarsa da tasirin gudummawarsa ga ilimi da aikin jarida a Nijeriya da ma duniya baki daya.

Ya ce littafin yana bayar da labari ne na musamman game da ra’ayin marubucin kan siyasa da mulki, aikin jarida kuma ya ba da shawara ga masu tsara manufofi, ‘yan jarida masu aiki da kuma masu gudanarwa a bangarorin gwamnati da na masu zaman kansu.

Tun da farko a jawabinsa, tsohon daraktan janar na hukumar kula da kafofin yada labarai ta kasa (NBC), Malam Danladi Bako, ya yaba wa halayen Mista Babajide-Otitoju, yana bayyana shi a matsayin jarumi.

Ya gode tare da yaba wa mataimakin shugaban kasa saboda girmama mai bikin da daukacin ‘yan jarida da aikin jarida.

A cikin wasu bayanai daban-daban, mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Sunday Dare da mai gabatar da shirin AIT, Mista Gbenga Aruleba, da shugaban hukumar kula da ‘yan Nijeriya a kasashen waje (NiDCOM), Hon. Abike Dabiri, wanda ya yi jawabi a madadin tsoffin abokan aiki na wanda ake murnar ranar haihuwarsa, sun yi masa yabo da kuma godiya ga gudunmawarsa ga aikin jarida da ci gaban dimokuradiyya a Nijeriya.

Haka kuma a wurin taron akwai jagoran majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele da Gwamnonin Umo Eno na Akwa Ibom da Babajide Sanwo-Olu na Legas da Kefas Agbu na Taraba da Usman Ahmed Ododo na Kogi da Babagana Zulum na Borno da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, mashawarci na musamman ga shugaban kasa kan yada labarai, Mista Bayo Onanuga, da tsohon babban lauyan tarayya, Malam Mohammed Adoke, da sauran su.

Shettima
Yusuf Shuaibu
+ posts Bio
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027: APC Na Fuskantar Matsin Lamba Kan Sake Fasalin Tawagar Yakin Neman Zabe
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    Cacar Baki Ta Kaure Tsakanin APC Da ‘Yan Adawa Kan Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Magidanta
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    INEC Ta Zayyano Kalubalen Da Ke Iya Shafar Sahihancin Zaben 2027
  • Yusuf Shuaibu
    https://hausa.leadership.ng/author/yusuf-shuaibu/
    2027:Kamun Ludayin Yakin Neman Zaben Manyan ‘Yan Takarar Shugaban Kasa
Shettima
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Tsaurara Matakan Fatattakar Haramtattun Harkoki A Sashen Kudi

Sin Ta Tsaurara Matakan Fatattakar Haramtattun Harkoki A Sashen Kudi

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.