ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shirin Raya Kasar Sin Karo Na 15, Taswirar Ci Gaban Kasashen Duniya

by CGTN Hausa and Sulaiman
4 months ago
Sin

Mataimakin daraktan ofishin kula da harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin kolin JKS Han Wenxiu ya bayyana yayin taro kan ci gaban kasar Sin na 2026 da aka yi jiya cewa, kasar za ta ci gaba da kara wa tattalin arzikin duniya tabbaci da daidaito da kuzari. Ko ta yaya za ta yi hakan?

A baya bayan nan, ana samun kafafen yada labarai na yammacin duniya da ke hasashen kasar Sin ba za ta cimma burinta na habakar tattalin arziki ba, suna ganin yanayin Gabas ta Tsakiya zai rage karfinta na fitar da kayayyaki. Abun lura shi ne, dogaron da tattalin arzikin Sin ke yi kan gudunmawar bangaren fitar da kayyayaki zuwa ketare, ya ragu daga kaso 59.2 a shekarar 2008, zuwa kaso 32.7 a bara. A yanzu kasar Sin ta fi mayar da hankali ne kan habaka kasuwar cikin gida, maimakon dogaro da fitar da kayayyaki waje kawai, inda wannan bangare ya bayar da gudunmawar da ta kai kaso 63.7 ga tattalin arzikin kasar a bara.

  • Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Tarwatsa Gada A Neja Domin Daƙile Harin Sojoji
  • Benin Ta Gudanar Da Bikin Ranar Taijiquan Ta Duniya A Karon Farko 

Irin wadannan alkaluma suna kara nuna kaifin basira da hangen nesa na kasar Sin, Shi ya sa shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 15 da aka fara a bana, ke zaman wata sabuwar hanya da sassan duniya za su ci gajiya. A ganina, shirin bai tsaya kan raya kasar Sin kadai ba, shiri ne na Sin na tafiya tare da kasa da kasa kan tafarkin ci gaba.

ADVERTISEMENT

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki, kwanciyar hankali da daidaton tattalin arzikinta na da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya. Kuma cikin shirin, kasar Sin mai bayar da gudunmawar kaso 30 ga tattalin arzikin duniya, na da burin ci gaba da rike kambunta, ta hanyoyin bunkasa bukatu na cikin gida da habaka bude kasuwarta ga kasashen waje da tunkarar kalubale. Mun ga yadda tasirin COVID-19 ya lalata tattalin arzikin kasashen duniya, amma kuma saboda tubala masu kwari na tattalin arzikin kasar, ba ta yi fama da tasirin kamar sauran kasashe ba.

Maimakon rufe kofofi ko takaita cinikayya da kasashen duniya, kasar Sin za ta kara fadada bude kofofinta da ma rage shingayen dake tarnaki ga cinikayya tsakaninta da kasashen duniya, domin ba su damar cin gajiyar babbar kasuwarta. Wannan wata manufa ce ta Sin ta nuna cewa, ba ta neman rarar cinikayya, sai dai daidaito da adalci da cin moriyar juna, wadanda su ne muhimman abubuwan da duniya ke bukata yanzu.

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sai kuma uwa uba, soke bukatar biyan haraji da za ta fara aiwatarwa kan kasashen Afrika da ke da huldar diplomasiyya da ita. Kusan zan ce kasashen Afrika su ne kan gaba wajen cin moriyar wannan shirin na shekaru biyar-biyar domin sun samu damar shigar da karin kayayyakinsu kasuwar duniya da kara bazar kayayyakinsu zuwa sassan duniya, lamarin da zai bunkasa samar da ayyukan yi da habaka ayyukan gona da kara karfin masana’antu da kanana da matsakaitan harkokin kasuwanci da sana’o’i, lamarin da sakamakonsa zai kai ga kyautata rayuwar jama’ar nahiyar da bunkasa ci gaba.

Kamar yadda nake fada a kullum, ci gaban kasar Sin ci gaba ne ga sassan duniya ba wai barazana ba. A duk lokacin da take tsara manufofin raya kasa da inganta walwalar al’ummarta, ba ta nuna son zuciya ko neman cin nasara daga musgunawa ko matsa wa wata kasa, ta kan mayar da hankali ne wajen samar da dabaru da hanyoyin da sauran kasashe za su ci gajiya domin a gudu tare a tsira tare. Wannan ita ce ma’anar babbar kasa mai sanin ya kamata. (Fa’iza Mustapha)

Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Ci Gaban Fasaha Na Hidimtawa Jama’a Cikin Kowane Yanayi A Kasar Sin
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sakamakon Binciken Masana Na Kasar Da Ake Fitarwa Kyauta Yana Kara Jan Hankalin Duniya
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Cinikin Waje Ta Kasar Sin Na Bunkasa Cikin Sauri Da Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Shekara Ta 2026
Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo
  • Sulaiman
    Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta
  • Sulaiman
    Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
  • Sulaiman
    Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

MASU ALAKA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026

Next Post
Xi Ya Yi Rangadi A Sabon Yankin Xiong’an Na Lardin Hebei Dake Arewacin Kasar Sin

Xi Ya Yi Rangadi A Sabon Yankin Xiong'an Na Lardin Hebei Dake Arewacin Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.