A baya-bayan nan, shugabannin kasashe da na jam’iyyun siyasa daga kasashe da dama sun aika sakonnin taya murna ga kwamitin kolin JKS da sakatare janar Xi Jinping, bisa cikar jam’iyyar shekaru 105 da kafuwa.Cikin sakonsa, shugaban jam’iyyar United Democratic Alliance ta kasar Kenya kuma shugaban kasar William Ruto, ya ce karkashin shugabancin sakatare janar Xi Jinping, Sinawa kusan miliyan 100 ne suka fita daga kangin talauci, haka kuma kasar ta gina tattalin arziki mai karfi tsakanin kasashen duniya, sannan ana kyautata rayuwar jama’a ainun.
Ya ce nasarorin da JKS ta samu, sun sa kasashe masu tasowa tunani mai zurfi kan dabarun raya kasa da na shugabanci, haka kuma sun kara karfafa kudurin Kenya na bin hanyar sauyi domin samun ci gaba.
Game da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka yi a yau Laraba cewa, jam’iyyu da manyan ’yan siyasa na kasashe da dama sun taya JKS murna dangane da cikarta shekaru 105 da kafuwa ta hanyoyi daban-daban. Ya ce kwararan shaidu sun tabbatar da cewa, ana ganin kasar Sin mai tsarin mulkin gurguzu da jam’iyyar JKS ke jagoranta a matsayin mai wanzar da zaman lafiya a duniya, kuma mai ba da gudummawa ga ci gaban duniya, kana mai kiyaye tsarin kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha/Bilkisu Xin)














