ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabannin Sin Da Koriya Ta Arewa Sun Sha Alwashin Wanzar Da Gagarumin Kawancen Gargajiya Tsakanin Kasashen Biyu

by Sulaiman and CGTN Hausa
3 months ago
Sin

Babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping, da babban sakataren jam’iyyar ‘yan kwadago ta Koriya ta Arewa, kuma shugaban kasar Kim Jong-un, sun amince da kudurin wanzar da gagarumin kawancen gargajiya daga zuri’a zuwa zuri’a tsakanin kasashen biyu.

Shugabannin biyu su amince da wannan matsaya ne a yau Talata, yayin da shugaba Xi ke ci gaba da ziyara a Koriya ta Arewa. A kuma yau din, shugaba Xi da mai dakinsa Peng Liyuan, sun kaiwa hasumiyar kawancen Sin da Koriya ta Arewa ziyarar girmamawa, bisa rakiyar shugaba Kim da uwargidansa Ri Sol Ju.Xi da Kim, sun kuma amince cewa shekarun 1950, lokacin da Sin da Koriya ta Arewa suka yi yaki kafada da kafada, muhimman shekaru ne dake da tasiri a tarihin su. Kuma a wannan rana da safe, Xi Jinping, basa rakiyar Kim Jong-un, ya ziyarci makarantar horar da shugabannin kwamitin tsakiyar jam’iyyar KWP dake birnin Pyongyang.

Xi Jinping da Kim Jong-un sun dasa wata bishiyar fir tare. Bishiyar fir tana kasancewa koriya a duk tsawon shekara, wanda hakan ke alamta dorewar abotar Sin da Koriya ta Arewa. Bayan haka, a gaban manyan shugabannin jam’iyyu da kasashen biyu, Cai Qi da memban dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar KWP, kuma sakataren tsakiyar jam’iyyar Kim Jae Ryong, sun gabatar da dutsen tunawa da dasa bishiyar. A gaban dutsen, an sassaka manyan kalmomi da harsunan Sinanci da Koriya ta Arewa cewa, “Abota tsakanin Sin da Koriya ta Arewa za ta dauwama har abada”.

ADVERTISEMENT

Dadin dadawa, Xi tare da uwargidansa Peng Liyuan sun kalli wasan kwaikwayo na musamman a filin wasanni na Pyongyang a wadannan rana bisa rakiyar Kim Jong-un da uwargidansa Ri Sol-ju, tare da jama’ar Koriya ta Arewa. ‘Yan wasan kwaikwayon sun gabatar da wakoki, da raye-raye da sauran nau’o’in fasaha, don maraba da ziyarar da Xi ke yi a Koriya ta Arewa bayan shekaru 7, tare da bayyana begen su na karfafawa, da kuma bunkasa abota da hadin gwiwar gargajiya tsakanin Sin da Koriya ta Arewa.

An kammala wasan kwaikwayon da waka mai jigon “Abota tsakanin Sin da Koriya ta Arewa tana dawwama har abada.” Wakilan bangarorin Sin da Koriya ta Arewa, sun gabatar da furanni da aka aika da sunan manyan shugabannin jam’iyyun kasashen biyu, da kuma masu dakinsu ga ‘yan wasan kwaikwayon, don taya su murnar nasarar gabatar da wasan. (Saminu Alhassan、Amina Xu)

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Sin
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
Sin
CGTN Hausa
+ posts Bio
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/

    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
  • CGTN Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cgtn-hausa/
    Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje 14,940 A Sokoto

'Yan Bindiga Sun Kashe Jami’in Tsaro, Sun Yi Garkuwa Da Mutane Da Dama A Sokoto

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.