Wata girgizar kasa mai karfin maki 7.4 ta auku a Colombia a ranar Litinin, wadda ya zuwa yanzu ta yi sanadin mutuwar sama da mutane dari, tare da jikkata sama da mutane dubu.
Game da haka, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yayin ba da amsa a gun taron manema labaru da aka saba yi a yau Laraba cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya riga ya aike da sakon ta’aziyya ga takwaransa na kasar Colombia Abelardo de la Espriella.
Kasar Sin kuma na cike da imanin cewa, a karkashin jagorancin gwamnatin kasar Colombia da shugaba Abelardo de la Espriella ke shugabanta, al’ummar kasar za su hada kai, don shawo kan wannan ibtila’i da wuri, da kuma sake gina kasarsu.
Kazalika, kasar Sin a shirye take, ta ba da taimakon da za ta iya ta hanyar da ta dace bisa bukatun Colombia. (Bilkisu Xin)














