A yanzu haka fannin kere-kere na kasar Sin yana kara samun sabbin nasarori a idon duniya, bisa jigon nan na sabbin “Ci gaba Uku” ko the New New Three” a Turance, inda kasar ta sauya daga mai karbar kwangilolin sarrafa tufafi, da kayayyakin kawata gina na katako, da sauran abubuwan amfani a gidaje, zuwa mai haifar da sauyi a fannin makamashi da ake iya sabuntawa, inda Sin ta shige sahun gaba a bangarorin kera ababen hawa masu aiki da lantarki, da baturan lithium, da kayayyakin sola.
A yanzu kuma, kasar Sin na cimma sabbin nasarori a fannin kere-keren AI, da na mutum-mutumin inji, da kayayyakin fasahar kiwon lafiya, matakin da ya shaida irin gagarumin ci gaban da kasar ke samu, a fannin masana’antun kere-kerenta masu matukar inganci.Wani binciken jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ya nuna yadda kaso 93.1% na masu bayyana ra’ayoyin suka amince cewa, the New New Three” da Sin ta cimma, sun tabbatar da nasarar kasar a fannin kere-kere na asali na masana’antun gida, da tsarin sarrafa hajoji masu basira, da samar da dabarun warware matsaloli ga kasuwannin kasa da kasa.
Kazalika, suna fatan Sin din za ta samar da karin gajiya, karkashin ci gaban kirkire-kirkire a nan gaba.Har ila yau, kaso 87.7% na masu bayyana ra’ayoyin sun amince cewa, wadannan masana’antu na shaida karfin ikon sarrafa hajoji da kirkire-kirkire na Sin, yayin da kaso 87.2 bisa dari ke ganin karfin masana’antun Sin ya wuce batun sarrafa hajoji kadai, maimakon hakan ya shafi ikonsu na tsara kayayyaki da mizanin ingancinsu, da dunkule albarkatun sassan kasa da kasa, da ci gaba da ingiza kirkire-kirkire da daga martabar masana’antu. (Saminu Alhassan)














