A jiya Juma’a 31 ga watan Yuli, tawagar zaunannun wakilan Sin dake MDD, ta gudanar da taron manema labaru game da taron fasahar AI na duniya na shekarar 2026, kuma taron koli na shugabancin harkokin fasahar AI na duniya a zauren MDD.
Zaunannen wakilin Sin dake MDD Fu Cong, a yayin bikin bude taron, ya bayyana cewa shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin kasar Sin game da tsarin shugabancin harkokin fasahar AI na duniya, da tunanin samun ci gaba tare da yin la’akari da bukatun jama’a, da taimakawa kasashe masu tasowa wajen rage gibin fasahar AI, da nuna goyon baya ga MDD wajen shugabancin harkokin fasahar AI na duniya da sauransu, batun ya samar da muhimmiyar gudunmawa wajen shugabancin harkokin fasahar AI na duniya.
Fu Cong, ya ce kasar Sin za ta ci gaba da bin tunanin bude kofa, da hadin gwiwa, da samar da moriyar juna da more fasahohi, da yin kokari tare da bangarori daban daban bisa tsarin MDD, don tattauna manyan batutuwan dake shafar yadda za a shugabanci harkokin fasahar AI na duniya a nan gaba.Manzon musamman na MDD mai kula da fasahohin sadarwa, da sabbin fasahohi Amandeep Singh Gill, ya bayyana cewa taron fasahar AI na duniya yana da babbar ma’ana, ya kuma yi fatan kungiyar hadin gwiwa ta fasahar AI ta duniya za ta yi hadin gwiwa tare da MDD. (Zainab Zhang)














