Gwamnatin Chadi ta yanke shawarar ficewa daga Kotun Manyan Laifuka ta Duniya ICC, bayan ta bayyana cewa kotun ba ta da amfani, ba ta adalci, kuma tana da burin takura wa ƙasashen Afirka ne kadai.
Wannan mataki ya biyo bayan bincike na tsanaki da kasar ta gudanar kan ayyukan kotun tun kafuwarta a shekarar 2002.
Chadi ta bayyana cewa cikin bincike 13 da kotun ta ƙaddamar, guda 9 duka sun shafi Afirka ne, yayin da sauran 4 da aka buɗe a wasu yankunan duniya ba su samu wani ci gaba ba.
Haka nan, ta bayyana cewa mutane 7 kacal kotun ke tsare da su, kuma 6 daga cikinsu duka sun fito ne daga ƙasashen Afirka.Wannan babban mataki na Chadi ya zo ne a daidai lokacin da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ke zarginta da hannu a rikicin basasa da ke faruwa a maƙobciyarta, wato Sudan, abin da ke ci gaba da ɗaukar hankali musamman a fagen siyasar duniya.
Ƙasar Chadi ta bi sahu ne bayan ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar waɗanda gwamnatocin soja ke mulka, a watan Satumba suka sanar da ficewar su.
Wannan mataki zai rage ƙarfin ikon da ƙasashen Yamma kamar Amurka da Tarayyar Turai ke da shi a kan manufoyin siyasar Afirka, yayin da ƙasashen nahiyar ke nuna cewa ba za su ƙara amincewa da tsarin shari’ar ƙasa da ƙasa wanda suke gani a matsayin aikin danniya na mulkin mallaka ba.
Ficewar daga ICC za ta ba wa shugabannin siyasa da na soji a Afirka kariya daga fuskantar shari’a a kotun Hague idan aka zarge su da keta haƙƙin bil’adama. Ga kasar Chadi musamman, wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake zarginta da hannu a rikicin Sudan. Don haka, ficewar za ta rage fargabar cewa za a iya bincikar jami’an gwamnatin Chadi ko na soji kan laifukan yaƙi a nan gaba.














