ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

NSCDC Ta Cafke Mutum 10 Da Ake Zargi Da Satar Kayan Gwamnati Da Kuma Fashi A Kano

by Rabi'u Ali Indabawa
3 months ago

Jami’an Hukumar Tsaron ta Nijeriya ta (NSCDC) reshen Jihar Kano sun kama wasu mutum 10 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da lalata kayayyakin gwamnati, sata, haɗa baki wajen aikata laifi, shiga haramtacciyar hanya da kuma karɓar kayan sata.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, SC Ibrahim Abdullahi, ne ya fitar ranar Laraba, ya ce an kama waɗanda ake zargin a wurare daban-daban a Jihar.

Sanarwar ta ce wuraren da aka kama su sun haɗa da Gwarmai a Ƙaramar Hukumar Ghari, yankin masana’antu na Challawa, Unguwar Rimi da Waratallawa duk a Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Rundunar NSCDC ta Jihar Kano ta samu nasarar cafke wasu gungun masu aikata laifuka 10 da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati, sata, haɗa baki wajen aikata laifi, shiga ba bisa ƙa’ida ba da kuma karɓar kayan sata.”

An kuma bayyana cewa kwamandan hukumar na Jihar, Commandant Mohammed Hassan Agalama IION, ya gabatar da waɗanda ake zargin a hedikwatar rundunar ranar Talata.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

Kayayyakin da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da mita 200 na wayoyin aluminium, wayoyin hannu, wayoyin copper, power bank da kuma muggan makamai kamar wuƙaƙe, adda, takobi da almakashi da sauransu.

Sanarwar ta ce an kammala bincike kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu domin fuskantar hukunci.

Kwamandan ya sake jaddada ƙudirin hukumar wajen kare muhimman kadarorin ƙasa da kayayyakin more rayuwa, tare da nuna rashin amincewa da duk wani nau’in aikata laifi. Ya kuma roƙi al’ummar Jihar Kano da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai domin magance matsalolin tsaro.

A wani labarin kuma, rundunar NSCDC ta Jihar Kwara ta kama wasu mutane uku bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da kuma safarar ma’adanai a birnin Ilorin.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Musa Abdullahi mai shekara 45, Aliyu Ibrahim mai shekara 20 da Ishaƙ Ibrahim mai shekara 51. An ce an kama su ne a wani samame na sirri da jami’an sashen ma’adanai da ƙarafa na rundunar suka gudanar da daddare.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Yankin Hong Kong Na Kasar Sin Ya Zama Cibiyar Kula Da Jarin Ketare Mafi Girma A Duniya

Yankin Hong Kong Na Kasar Sin Ya Zama Cibiyar Kula Da Jarin Ketare Mafi Girma A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.