Domin kara saukaka tafiye-tafiyen kan iyakokin kasa, kasar Sin ta yanke shawarar cewa daga ranar 17 ga watan Fabrairun 2026, za ta fadada manufar shiga kasarta ba tare da biza ba ga masu fasfo na gama-gari daga kasashen Kanada da Birtaniya, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi.
A cewar mai magana da yawun, masu fasfo na gama-gari na kasashen biyu za a iya tsame su daga masu bukatar biza wajen shiga kasar Sin da zama a kasar na tsawon kwanaki 30 domin kasuwanci, yawon bude ido, ziyarar dangi da abokai, musaya da kuma yada zango.
Manufar za ta fara aiki har zuwa ranar 31 ga Disambar 2026, kamar yadda mai magana da yawun ya bayyana. (Abdulrazaq Yahuza Jere)















Discussion about this post