ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Bukatar Kara Kaimin Ibada A Watan Ramadan

by Ibrahim Bala and Sulaiman
5 months ago
Ramadan

Assalamu Alaikum Wa Rahmatullahi Ta’ala Wa Barakatuhu.

Jama’a barkanmu da kasancewa tare da wannan fili mai albarka, wanda yake tattaunawa game da abin da yake ci wa al’umma tuwo a kwarya.

A wannan mako zan dan kara jan hankali a kan lokutan da ya kamata mu kara kusanci ga ubangiji, mu samu lada mu ji kai. A wannan wata da yake gabato mu na Ramadan, ya kamata mu daure, mu cije wajen ayyukan alkhairi.

ADVERTISEMENT

Allah subhanahu wata a’ala ya fifita watan Ramadana a cikin watanni da yawa, wata ne me falala da Allah yake bude kofofin rahmarsa. Amma sai a cije, masu kudi, ‘yan kasuwa sai su daura damara su kara kudin kaya.

Ba ma ga masu kudi ba, su kansu talakawa sai su hade rai, su wata ne na neman kudi, haka kawai sai an yi kudi a wannan watan, sai an takura sai an zafafa. Hatta kankara in kana siyan kankara naira dari za ta koma dari biyar har naira dubu daya, saboda kawai lokaci ne da za a yi amfani da ita.

LABARAI MASU NASABA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

Kwana ashirin da tara ne, amma wani shi sai ya zafafa abin da shekara guda ma bai zafafa ba. Ya ilahil’alamina lokaci ne da ya kamata mu yi amfani da shi mu samu lada, amma shi ne ya zama na tsawwalawa. Idan fa ka saukaka fa Allah zai saukaka maka.

A iya watannin nan Allah sai ya yi maka gafarar da shekara ashirin kana neman gafara bai yi maka ba, Allah sai ya yi maka arzikin da shekaru talatin kana neman arzikin bai yi maka ba, Allah sai ya yi maka budin da shekara arba’in kana nema bai yi maka ba, sai ya yi maka a wannan watan.

To, ka ga wata ne da ya kamata kai ma ka tausaya, kai ma Allah sai ya tausaya maka. Idan ka taimaki mutum daya ya ji dadi to, Allah zai yi maka budin da za ka ji dadi har abadan abidina. Dan haka ‘yan’uwa dan Allah duk abin da aka san dan’uwa musulmi ya na amfani da shi dan ya sha ruwa ya ji dadi a ransa dan Allah mu saukaka.

Na tabbatar akwai abubuwan da aka siye su da dadewa irinsu, barkono, kayan citta, kayan shayi, da su mai, akai ta bobboyewa su waken suya da waken kosai da ake yi. To, dan Allah ‘yan’uwa mu duba girman musulinci mu duba girman watan, mu duba ‘yan’uwantaka da zumuntaka, dan Allah kar mu zafafa, mu saukaka kayan amfani yadda kowa zai iya amfana. Hatta kankana sai ka ji ana dubu biyar, a yanzu dai kana iya siyen dubu daya, dari biyar, amma a wannan wata har dubu biyar, sai ka ce ta gwal.

To, dan Allah ‘yan’uwa musulmi ina mai bamu shawara, lokaci ne da za mu samu dama da za mu samu kusanci ga ubangiji. Abin da muka dade muna roko sai ka ga Allah ya ba mu saboda tausayawa da muka yi. Wanda kuma Allah ya basu iko da tausayawa na taimakawa marayu da makofta, akwai wadanda suna cikin wani hali, wani yakan adana abin da zai adana tun daga daya ga watan ramadan har izuwa ranar sallah.

Wani kuma kullum sai ya fita zai samu abin da ma zai kawo wa iyalinsa a ci, idan Allah ya sa kana da wannan damar to, ka taimaka, kai ma sai Allah ya baka, ka kuma tausaya. Ga marayu nan wasu sai sun yi bara za su samu, to irin wannan damar da ka samu Allah ya bude maka kofofi to, kai ma sai ka samar domin Allah ya tausaye ka.

Allah ya sa mu dace, ubangiji Allah ya sa mu shiga wannan watan cikin nasara da albarka, Allah ya sa albarka a cikin rayuwarmu baki daya.

Ramadan
Ibrahim Bala
+ posts Bio
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Hanyoyin Da Za A Bi A Rage Yawan Zawarawa
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Matsalar Ƙwacen Waya: Ina Mafita?
  • Ibrahim Bala
    https://hausa.leadership.ng/author/ibrahim-bala/
    Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 
Ramadan
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin
  • Sulaiman
    Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka
  • Sulaiman
    Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi
  • Sulaiman
    CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

MASU ALAKA

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki
Marurun Zuciya

A Duba Halin Da Masu Buƙata Ta Musamman Ke Ciki

June 20, 2026
Laifukan Intanet: Kotun Abuja Ta Karɓi Rahoton DSS, Ta Ba Da Belin Wani Ɗan Gwagwarmaya
Marurun Zuciya

Falalar Goman Farko Na Zul-hajji 

May 23, 2026
marayu
Marurun Zuciya

Bukatar Kulawa Da Marayu Da Masu Karamin Karfi

May 17, 2026
Next Post
Ministan Wajen Sin: Akwai Kyakkyawan Fata A Dangantakar Sin Da Amurka

Ministan Wajen Sin: Akwai Kyakkyawan Fata A Dangantakar Sin Da Amurka

LABARAI MASU NASABA

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

An Bankado Muguwar Aniyar Japan Ta Haifar Da Tashin Hankali A Tekun Kudancin Sin

July 14, 2026
Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

Layin Dogo Tsakanin Tanzaniya Da Zambiya Ya Zama Shaidar Abota Tsakanin Sin Da Afirka

July 14, 2026
Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

Nijeriya da Masar Sun Ƙulla Haɗin Gwiwa Domin Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi

July 14, 2026
CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

CMG Ya Gudanar Da Babban Taron Masu Kirkirar Manyan Shirye-Shirye Da Fina-Finai

July 14, 2026
Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

Tsohon Sanatan Gombe, Bayero Nafada, Ya Fice Daga PDP Bayan Ganawa da Shugabannin APC

July 14, 2026
ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

ADC Ta Nemi A Binciki Nafiu Bala Bayan INEC Ta Ƙaryata Iƙirarinsa

July 14, 2026
Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato

Sojoji Sun Daƙile Harin ISWAP A Borno

July 14, 2026
Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

Tsaka mai wuyar Infantino da Koma bayan mulkin yamma

July 14, 2026
“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

“Buhari Ya Taɓa tambaya Ta Mutane Nawa Na Kashe Saboda Yawan Azumin Dana Ke Yi”

July 14, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.