Wasu bayanai daga hukumar kula da hada-hadar kudaden waje ta kasar Sin, sun ce a rabin karshe na wannan shekara, hukumomin kula da hada-hadar kudaden waje sannu a hankali za su ci gaba da fadada bude kofa ga ketare, bisa ka’idojin kasa da kasa a fannin hada-hadar kudaden waje.
Yayin taron hukumar game da musayar ra’ayi kan ayyukan kula da kudaden waje a rabin karshe na shekarar nan ta 2026, wanda aka gudanar a kwanan nan, an bayyana cewa za a ingiza gyare-gyare don samar da yanayin cinikayya mai sauki, da fitar da jerin matakan saukake sarrafa kudaden waje na yau da kullum, ta yadda za a aiwatar da manufofin saukake shige da ficen kudaden waje, karkashin ingantaccen tsarin cinikin shige da fice.
Kazalika, za a aiwatar da matakan goyon bayan bunkasa sabbin nau’ikan cinikayya, kamar kasuwancin yanar gizo na ketare, da inganta sarrafa kudaden waje na cinikin bayar da hidimomi, da kuma goyon bayan bunkasa cinikayyar kayayyakin da ake iya kara sarrafawa. (Amina Xu)












