Dakarun rundunar hadin gwuiwa ta kasa da kasa (MNJTF) sun kashe ‘yan ta’adda sama da 70 tare da lalata wasu bama-bamai da aka hada da motoci 8 a wani sumame na baya-bayan nan a yankin tafkin Chadi.
Babban jami’in yada labarai na rundunar ta MNJTF, Laftanar Kanar Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa, wadannan hare-haren da aka samu nasara, wani bangare ne na aikin soji mai lakabin “Operation Lake Sanity 2”, wanda ya hada da kai harehare ta sama da kasa kan sansanonin ‘yan ta’adda a fadin yankunan Kamaru da Nijeriya.
- Huldar Abotar Dindindin Tsakanin Sin Da Kazakhstan Na Samun Ci Gaba Zuwa Sabon Mataki
- Jimillar Cinikayyar Ba Da Hidimomi Tsakanin Sin Da Sauran Sassan Kasa Da Kasa Ta Karu Cikin Sauri
A yayin farmakin, dakarun MNJTF tare da goyon bayan rundunar sojojin kasar Chadi cikin gaggawa sun tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda guda biyar tare da kashe ‘yan ta’adda 70. Sojojin sun kuma lalata wasu manyan makamai guda biyu a arewa maso gabashin Malam Fatori.
Laftanar Kanar Abubakar ya mika godiyarsa ga dukkan Sojojin da suka halarci aikin, wadanda suka hada da na ‘Operation Emergence 4 Kamaru’, da ‘Operation Hadin Kai Nigeria’, da ‘Sector 4 Nijar’, wadanda gudunmawarsu ta taka rawa wajen samun nasarar aikin.
Ya kuma jaddada aniyar MNJTF na kawar da ta’addanci da kuma maido da zaman lafiya a yankin tafkin Chadi, inda ya sha alwashin ci gaba da yin aiki tukuru da abokan hulda domin cimmawa da kuma dorewar wannan muhimmin manufa.