A makon da ya gabata ne aka fara buga gasar Firimiya ta kasar Ingila inda tuni kungiyoyi 20 din da za su buga gasar kowacce ta buga wasanta na farko yayin da a gobe ne za a fara buga wasa na sati na biyu a gasar wadda Arsenal ke neman sake lashewa.
A gasar Premier League ta 2026 zuwa 2027 da aka fara, akwai wasu matasan ’yan wasan Nijeriya, inda kusan ’yan Super Eagles tara ke wakiltar kungiyoyi biyar daban-daban.
Cikin jerin akwai fitattun ’yan wasa irin su Aled Iwobi, Calbin Bassey da Ola Aina, yayin da matasan ’yan wasa Benjamin Fredrick da Zadok Yohanna da ke wakiktar kungiyiyinsu a babbar gasar ta kwallon kafa a Ingila. Haka kuma, akwai wadanda suka koma sababbin kungiyoyi kamar Taiwo Awoniyi da Frank Onyeka, wadanda yanzu suke buga wasa a Cobentry City, yayin da Semi Ajayi da Dabid Akintola ke cikin tawagar Hull City, wadda ta dawo gasar Premier League kuma ta doke Manchester United a wasan farko.
Wasu daga cikin ‘yanwasan Nigeriya da suke buga gasar Firimiyar Ingila sun hada da:
Benjamin Fredrick — Brentford
Benjamin Fredrick na daga cikin matasan ’yan wasan Nijeriya da za su buga Premier League, kuma yana cikin wadanda ake sa ran za su ja hankali. An haifi Fredrick a Kaduna, inda ya fara buga wasa a kungiyar Simoiben Football Academy da ke Kaduna, kafin ya koma buga wa ABS, sannan Nasarawa United wasa a Nijeriya. Fredrick ya koma Ingila a 2023, inda ya fara buga wasa a kungiyar matasan Brentford, Brentford B, a matsayin aro.
Kokarinsa ya sa Brentford ta dauke shi na dindindin a 2024. Daga bisani ya zama muhimmin dan wasa a kungiyar, inda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Brentford B a 2025. Ya kuma taimaka wa kungiyar ta lashe gasar Under-21 Professional Debelopment League.
Bayan ya koma Belgium a matsayin aro domin buga wa FCB Dender wasa, rauni ya katse zamansa, inda ya koma Brentford. A kakar wasa ta 2026 zuwa 2027, an daga shi zuwa tawagar farko ta Brentford, inda ya kuma sanya hannu kan sabon kwantiragi na shekaru hudu. Fredrick ya fara bugawa Nijeriya wasa a matakin manya a 2025, kuma yanzu yana fatan nuna kansa a matsayin fitaccen dan wasan Premier League.
Zadok Yohanna — Brighton & Hobe Albion
Tafiyar matashin danwasa Zadok Yohanna zuwa matakin Premier League ta kasance cikin sauri sosai. Matashin ya fara harkar kwallon kafa ne a Ikon Allah Football Academy da ke Kaduna a Nijeriya, kafin ya koma Sweden a 2025 domin komawa kungiyar AIK.
A kungiyar AIK, Yohanna ya yi saurin dagawa daga matakin matasa zuwa tawagar farko. Ya buga wasa 18 a gasar lig da sauran kofuna a lokacin da ya fara samun damar bugawa babbar tawaga, inda ya ci kwallo biyar sannan ya taimaka aka ci wasu hudu. Hakan ya ja hankalin Brighton, wadda ta dauke shi kan kwantiragin shekara biyar da zai ci gaba har zuwa 2031.
Wannan komawa Brighton babbar dama ce ga matashin dan wasan, wanda zai iya buga wasa a matsayin lamba 10 ko kuma dan wasan gefe mai shigowa tsakiyar fili.
Brighton na kallon sa a matsayin dan wasa mai kuzari, saurin gudu da iya fuskantar abokan hamayya kai tsaye. Yohanna na daga cikin sabbin ’yan wasan Nijeriya da ya kamata a sa ido sosai a kansu a wannan kakar.
Ola Aina — Nottingham Forest
Ola Aina na daga cikin ’yan wasan Nijeriya mafi kwarewa a wannan jerin. An haife shi a Landan, inda ya fara samun horo a makarantar koyon kwallon kafa ta Chelsea. Ya samu nasarori da dama a matakin matasa kafin ya fara bugawa babbar tawagar Chelsea wasa.
Daga baya ya koma Torino ta Italiya, inda ya fara buga wasa a matsayin aro kafin daga bisani kungiyar ta dauke shi na dindindin. Aina ya koma Ingila tare da Fulham a kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 a matsayin aro, inda ya buga wasa 31 na Premier League.
Bayan wasanninsa a Italiya da Ingila, ya koma Nottingham Forest a 2023. Tun daga lokacin ya zama muhimmin dan wasa a kungiyar. A kakar wasa ta 2024 zuwa 2025, ya buga wasa 35 na Premier League, sannan ya tsawaita kwantiraginsa da Forest har zuwa 2028. Aina ya shiga sabuwar kakar a matsayin daya daga cikin ’yan wasan baya mafi kwarewa na Nijeriya.
Calbin Bassey — Fulham
Gogaggen dan wasa Calbin Bassey ya bi wata hanya mai ban sha’awa kafin ya kai ga Premier League. An haife shi a Italiya ga iyayen Nijeriya, amma ya girma a Landan. Ya taso ne a makarantar koyon kwallon kafa ta Leicester City, ko da yake bai samu damar buga wa babbar tawagar kungiyar wasa ba. A shekarar 2020 ya koma Rangers ta Scotland, inda ya yi suna cikin kankanin lokaci.
Bassey ya lashe gasar Scotland da Scottish Cup, sannan ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da Rangers ta kai wasan karshe na Europa League a 2022. A wannan shekarar ne Ajad ta Netherlands ta dauke shi, kafin Fulham ta saye shi a shekarar 2023. A Fulham, Bassey ya zama daya daga cikin ’yan wasan baya na kungiyar, kuma yana iya buga wasa a matsayin mai tsaron baya na tsakiya ko kuma na gefen hagu. Ya kuma zama daya daga cikin fitattun ’yan wasan Super Eagles.
Aled Iwobi – Fulham
Kwararren dan wasa Aled Iwobi na daga cikin ’yan wasan da suka fi kwarewa a Premier League a wannan jerin. Shi ne dan uwan shahararren tsohon dan wasan Nijeriya Jay-Jay Okocha. Iwobi ya taso ne a makarantar koyon kwallon kafa ta Arsenal, inda ya samu damar shiga babbar tawagar kungiyar kafin ya koma Eberton a 2019.
Daga baya ya koma Fulham a 2023, inda ya zama muhimmin dan wasan tsakiya da kuma wajen kai hari. A watan Yunin 2026, Iwobi ya cimma wani babban tarihi bayan ya buga wasansa na 100 da Super Eagles, inda ya shiga cikin rukunin ’yan Nijeriya kalilan da suka kai wannan adadi. Ya buga daruruwan wasanni a Premier League kuma har yanzu yana daga cikin ’yan wasan Nijeriya da suka fi iya kirkirar damar cin kwallo. A Fulham, iya buga wasa a wurare daban-daban shi ne ya sa yake da matukar amfani ga kungiyar.
Taiwo Awoniyi — Cobentry City
Taiwo Awoniyi, a watan Agustan shekarar 2026 ya koma Cobentry City daga Nottingham Forest, a yarjejeniyar da aka ruwaito ta kai kusan fam miliyan tara.
Tafiyarsa zuwa Premier League ta fara ne daga Imperial Soccer Academy a Nijeriya, kafin Liberpool ta dauke shi tun yana matashi.
Saboda matsalolin samun izinin aiki a Ingila, ya shafe shekaru yana zuwa kungiyoyi daban-daban a matsayin aro, ciki har da kungiyoyi a Jamus, Belgium, Netherlands da Ingila.
Lokacin da ya fi yin fice shi ne a Union Berlin ta Jamus, inda ya zama dan wasan gaba mai yawan cin kwallaye. Kungiyar Nottingham Forest ce ta zauke shi a 2022, kuma ya yi tasiri sosai a kakarsa ta farko a Premier League, inda ya ci kwallaye 10 a gasar a kakar 2022 zuwa 2023.
Yanzu da yake Cobentry, Awoniyi zai yi fatan dawo da mafi kyawun salon wasansa tare da taimaka wa kungiyar da kwallaye yayin da take dawowa Premier League bayan shafe shekara 25.
Dabid Akintola — Hull City
Shi ma dan wasa Dabid Akintola ya bi kungiyoyi da dama a kasashe daban-daban kafin ya kai ga Premier League. Dan wasan dan asalin Oyo ya fara sana’ar kwallon kafa a FC Ebedei, kafin ya koma kungiyar Midtjylland ta Denmark.
Daga nan ya yi zaman aro a kungiyoyi da dama ciki har da Thisted, Jerb, Haugesund, Rosenborg, Omonia da Hatayspor. Daga bisani ya buga wa Adana Demirspor da Çaykur Rizespor wasa a Turkiyya. Hull City ta dauke shi a watan Agustan 2025 kan kwantiragin shekaru biyu. A kakar 2025 zuwa 2026 ya buga wasanni 20 na Championship da Hull, inda ya ci kwallo daya sannan ya taimaka aka ci wasa biyu.
Yanzu da Hull ta koma Premier League, dan wasan mai shekaru 30 ya samu damar gwada kansa a matakin mafi girma na kwallon kafa a Ingila.
Semi Ajayi — Hull City
Dan wasa Semi Ajayi ya koma kungiyar Hull City da kwarewar gasar Premier League sosai. Domin an haife shi a Landan, inda ya taso a makarantar koyon kwallon kafa ta Charlton Athletic, kafin ya yi wasa a kungiyoyi kamar Cardiff City da Rotherham United.
Ya kafa kansa sosai a West Bromwich Albion, inda ya shafe shekaru shida tare da kungiyar kuma ya buga wasanni sama da 200 a dukkan gasa. Hull City ta dauke shi a 2025. Komawarsa Premier League ta samu kyakkyawan faraway inda a wasan farko na Hull Ajayi ya ci kwallon farko ta Hull a wasan da ta doke Manchester United da ci 2-0. Ga dan wasan bayan, wannan wata babbar hanya ce ta sanar da dawowarsa gasar Premier League. Ajayi ya kuma kasance cikin tawagar Super Eagles na tsawon lokaci, inda ya buga wasanni sama da 50 wa Nijeriya.
Frank Onyeka — Cobentry City
Frank Onyeka shi ne na karshe cikin ’yan wasan Nijeriya tara. Onyeka ya fara sana’ar kwallon kafa ne da FC Midtjylland ta Denmark bayan ya taso daga FC Ebedei a Nijeriya.
Ya zama muhimmin dan wasa a Denmark, inda ya lashe gasar Lig da kofuna, sannan ya samu damar buga gasar Champions League. Brentford ta dauke shi a 2021, inda ya zama dan wasan farko da kungiyar ta saya tun bayan da ta shiga Premier League.
Bayan shekara hudu a Brentford, ciki har da zaman aro a kungiyar Augsburg ta Bundesliga, Onyeka ya koma Cobentry City na dindindin a watan Yunin 2026. Ya taimaka wa Cobentry wajen lashe Championship da samun gurbin zuwa Premier League.
Yanzu zai sake haduwa da dan uwansa na Super Eagles, Taiwo Awoniyi, a Cobentry, wanda shi ma ya koma kungiyar a kwanakin baya daga Nottingham Forest. Kuzarinsa da karfinsa da iya taka rawar tsaron tsakiyar fili na iya zama muhimmin abu yayin da Cobentry ke kokarin kafa sansani a Premier League.
Duk da cewa har yanzu ba a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa ba a Ingila, hakan yana nufin watakila za a iya samun wasu ‘yan Nijeriya da za su iya komawa gasar firimiya da buga wasa daga nan zuwa daya ga watan Satumba. Daga gogaggun ’yan wasan kasa irin su Iwobi, Aina, Bassey, Ajayi da Onyeka, zuwa matasa masu tasowa kamar Fredrick da Yohanna, Nijeriya na da dimbin wakilci a Premier League ta 2026 zuwa 2027.
Abin da ya kara sanya kakar ta bana ta zama ta musamman shi ne kasancewar Cobentry City da Hull City sun dawo Premier League, wanda ke nufin ’yan Nijeriya hudu daga cikin tara suna buga wa kungiyoyin da suka samu karin girma daga Championship wasa.
Ga Super Eagles, wannan kakar za ta kasance wata dama ta bibiyar haduwar kwarewar tsofaffin ’yan wasa, wadanda suka riga suka kafa kansu a Premier League, da kuma sabbin ’yan wasa masu tasowa wadanda ke neman kafa tarihi a nan gaba.














