ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matan APC A Kaduna Sun Gargadi Masu Shirin Zanga-zanga

by Shehu Yahaya and Sulaiman
5 months ago

Kungiyar wayar da kan matan jam’iyyar APC ta shiyyar Kaduna ta Tsakiya dake jihar Kaduna wato (Kaduna Central APC Women Mobilization Forum), ta bayyana cikakken goyon bayanta ga duk wani mataki da gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, zai dauka dangane da tsayar da ‘yan takara a shiyyar gabanin babban zaben shekarar 2027.

Kungiyar ta bayyana wannan matsaya ne yayin wani taro da ta gudanar a dakin taro na otel din Hamdala da ke birnin Kaduna, inda ta jaddada cewa hadin kai da biyayya ga shugabancin jam’iyya su ne ginshikin samun nasara a kowane zabe.

Jagorar kungiyar Madam Vera Oladotun, ta ce tana da yakinin cewa matakan da gwamnan zai dauka za su taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC daga sama har kasa a zaben 2027.

ADVERTISEMENT

Har ila yau, kungiyar ta nesanta kanta daga duk wata zanga-zanga da wasu mata ke shirin gudanarwa a jihar Kaduna, inda aka danganta zanga-zangar da goyon bayan wani dan takara.

Kungiyar ta bayyana irin wadannan yunkuri a matsayin abubuwan da ka iya haddasa rikici da rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

Madam Vera Oladotun, ta bayyana cewa kungiyar ba za ta shiga ko goyon bayan kowace irin zanga-zanga ba da sunan nuna rashin amincewa da wani dan takara.“Mu a matsayinmu na mata masu kishin jam’iyya, mun yanke shawarar nisanta kanmu daga duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kai.

Muna kira ga daukacin matan APC da su ci gaba da mara wa gwamnatin Sanata Uba Sani baya domin ci gaban jihar da kuma tabbatar da nasarar jam’iyyar a zabe mai zuwa,” in ji ta.

Madam Oladotun ta kuma bayyana cewa idan har akwai wani dan takara da kungiyar za ta goyawa baya a matakin majalisar dattawa, to sun fi karkata ga Sanata Shehu Sani, wanda ta ce yana da kwarewa da gogewar wakiltar al’umma.

A cewarta, “Sanata Shehu Sani yana nuna kwarewa da jajircewa wajen kare muradun al’umma, kuma muna ganin ya cancanci sake wakiltar mu a majalisar dattawa.

”Kungiyar ta kuma yi kira ga sauran bangarorin jam’iyyar APC da su guji duk wani abu da zai kawo rabuwar kai, tare da jaddada muhimmancin hadin kai domin fuskantar kalubalen siyasa da ke tafe.

Mahalarta taron sun hada da shugabannin mata daga kananan hukumomi daban-daban na shiyyar Kaduna ta tsakiya, wadanda suka bayyana aniyarsu ta ci gaba da wayar da kan mata a kan muhimmancin shiga harkokin siyasa da kuma zabe.

A karshe, kungiyar ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryen fadakarwa da gangamin wayar da kai domin karfafa gwiwar mata su taka rawar gani wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a dukkan matakai a zaben shekarar 2027.

Shehu Yahaya
+ posts Bio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Uba Sani Ya Yi Jimamin Rasuwar Dan Jarida Jafaru Yakubu Maitama
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamnatin Kaduna Ta Fara Rabon Takin Zamani Kyauta Ga Manoma 150,000
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Zaka Iya Sayar da Takin Gwamnati Ka Sayawa Iyalinka Kaji — Imam Nuradden
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Rashin Tsaro: ACI Zata Kira Taron Gaggawa Na Masu Ruwa Da Tsaki A Kaduna
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Sulaiman
    Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

MASU ALAKA

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi
Manyan Labarai

2027: Atiku Na Amfani Da Tallafin Mai A Matsayin Dabarun Siyasa – Fayemi

September 8, 2026
Siyasa

Muna Da Yan Takarar Gwamna A Jihohi 28 Don Shiga Zaben 2027

September 6, 2026
Next Post
Sin Ta Bai Wa Iran Agajin Gaggawa Na Jin Kai

Sin Ta Bai Wa Iran Agajin Gaggawa Na Jin Kai

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.