ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

El-Rufai Ya Maka ICPC Kotu Kan Hana Shi Ganin Iyalansa, Ya Nemi Naira Biliyan 10

by Abubakar Sulaiman
3 weeks ago

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar da ƙarar neman diyya ta Naira biliyan 10 a kan Hukumar ICPC, bisa zargin hana shi ganin matarsa, Aichatou Asabe, da ɗansa, Abba El-Rufai, yayin da yake tsare a hannun hukumar. Lauyansa, Ubong Akpan, ne ya shigar da ƙarar, inda aka kuma haɗa Shugaban ICPC da Babban Lauyan Tarayya (AGF) a matsayin waɗanda ake ƙara.

A ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1852/2026, wadda aka shigar a ranar 13 ga Agusta, El-Rufai ya roƙi Babbar Kotun Tarayya ta Abuja da ta tabbatar da cewa haƙƙoƙinsa na asali da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanada ba su tafi a banza ba saboda tsare shi. Ya kuma ce hana shi damar ganin iyalansa, musamman domin su kai masa abinci, da magunguna da sauran buƙatu, ba tare da sahalewar doka ko umarnin kotu ba, ya saɓa wa haƙƙinsa.

Tsohon gwamnan ya kuma zargi jami’an ICPC da amfani da ƙarfi, da tsoratarwa da kuma tsoma baki cikin dangantakarsa da iyalansa yayin da matarsa da ɗansa suka yi ƙoƙarin ganinsa a ranar 7 ga Yuli. Ya ce hakan ya haifar masa da wulakanci, da damuwa da matsananciyar matsalar tunani, tare da neman kotu ta umurci ICPC da ta ba shi damar ganin iyalansa da lauyoyinsa cikin sauƙi a duk lokacin da yake tsare.

ADVERTISEMENT

A cikin rantsuwar da aka gabatar wa kotu, Babban Sakataren El-Rufai, Mohammed Shaba, ya ce matarsa ta kasance tana kai masa abinci, da tufafi, da magunguna da sauran abubuwan da yake buƙata tun bayan tsare shi. Ya kuma bayyana cewa a ranar 1 ga Afrilu, Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna ta bayar da umarnin bai wa waɗanda ake tsare damar ganin lauyoyinsu da likitocinsu. A cewarsa, wannan umarni ya nuna cewa bai kamata a tsare mutum ba tare da ya samu damar sadarwa da mutanensa ba.

Shaba ya ƙara da cewa kafin ranar 7 ga Yuli, Asabe tana ziyartar mijinta akai-akai tare da kai masa abinci da sauran abubuwa ba tare da cikas ba. Sai dai daga baya aka hana ta yin hakan, lamarin da ya sa El-Rufai ya garzaya kotu domin neman a tabbatar da haƙƙinsa na ganin iyalansa da samun kulawar da yake buƙata yayin da yake tsare.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Iyalin El-Rufai Sun Bai Ministan Tsaro Wa’adin Kwana 7 Kan Zargin Rikicin Kudancin Kaduna
  • Abubakar Sulaiman
    Atiku Ya Zargi Gwamnatin Tarayya Da Cin Bashi Kamar Mashayin Da Kuɗi Ya Ƙarewa
  • Abubakar Sulaiman
    Boko Haram Ta Kai Hari Adamawa, Ana Fargabar Mutuwar Mutane 11
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Kashe Mutane 7, Sun Yi Garkuwa Da 12

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Ta Amfani Da Rokar Long March-12

Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabon Rukunin Taurarin Dan Adam Ta Amfani Da Rokar Long March-12

LABARAI MASU NASABA

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.