Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
An fara ganawar da yammacin ranar Alhamis, 27 ga watan Agusta, 2026, bayan gwamnonin sun halarci taron Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa (NEC), wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta.
Har yanzu ba a bayyana dalilin ganawar ba tukuna.
Ganawar na zuwa ne kwanaki takwas bayan fara kamfen ɗin zaɓen 2027 a hukumance, kamar yadda jadawalin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ya tanada.
Haka kuma, ganawar ta zo kwanaki biyar bayan APC ta fitar da sunayen mambobin Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa.
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari ne, zai jagoranci kwamitin a matsayin Darakta-Janar.














