ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Tsaurara Tsaro A NIPSS Bayan Harin ’Yan Bindiga

by Sadiq
4 weeks ago

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya ba da umarnin ɗaukar matakan gaggawa domin ƙara tsaro a Cibiyar Nazarin Manufofi da Dabarun Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a Jihar Filato, bayan harin da ’yan bindiga suka kai inda suka kashe sojoji biyu da jami’in ɗansanda ɗaya.

Yayin wata ziyara da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai cibiyar a madadin shugaban ƙasa ranar Juma’a, ya miƙa sakon ta’aziyyar gwamnatin tarayya ga iyalan jami’an tsaron da suka rasa rayukansu, tare da tabbatar musu da cewa gwamnati za ta kula da su.

Shettima ya ce Shugaba Tinubu ya umarci mahukuntan NIPSS da su haɗa kai da rundunar sojoji, ’yansanda da DSS domin ƙara tsaro a cibiyar cikin gaggawa.

ADVERTISEMENT

Ya kuma ce dole ne a gabatar da cikakken shirin inganta tsaro, wanda ya haɗa da sa ido ta na’urori, ƙarin jami’an tsaro, kula da hanyoyin shiga da tsarin gaggawa cikin sa’o’i 72.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana NIPSS a matsayin muhimmiyar cibiyar ƙasa, yana mai cewa kare ta ya zama wajibi ga tsaron Nijeriya.

LABARAI MASU NASABA

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Ya tabbatar wa ma’aikata da mahalarta shirin cewa tsaronsu na da muhimmanci ga gwamnati, tare da alƙawarin cewa iyalan jami’an tsaron da suka mutu za su samu cikakken tallafi.

Shettima ya kuma yaba wa Darakta Janar na NIPSS, Ayo Omotayo, da sauran jami’an cibiyar bisa yadda suka ɗauki matakan gaggawa wanda ya taimaka wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan ma’aikata da mahalarta shirin.

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya amince da ɗaukar wasu matakan inganta tsaro a kewayen cibiyar, ciki har da samar da yankin kariya da kuma girka fitilun tsaro.

Haka kuma, mahukuntan NIPSS sun buƙaci ƙarin jami’an tsaro da na’urorin sa ido kamar kyamarorin CCTV domin ƙara kare cibiyar daga duk wani hari a nan gaba.

MASU ALAKA

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe
Manyan Labarai

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare
Manyan Labarai

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu
Manyan Labarai

Mutfwang Ya Buƙaci Sojoji Su Ƙara Ƙaimi A Aikinsu

July 16, 2026
Next Post
Sin Na Kira Da A Ingiza Matakan Siyasa A Kasar Libya

Sin Na Kira Da A Ingiza Matakan Siyasa A Kasar Libya

LABARAI MASU NASABA

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

July 17, 2026
NPA Ta Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 758.2 A 2024

Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026
Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

July 17, 2026
Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026
Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

Pew: Sin Ta fi Amurka Samun Amincewar Al’ummun Duniya

July 16, 2026
Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

Sin Ta Fitar Da Tsarin Sanya Ido Don Inganta Muhalli Da Muhallin Halittu Na Shekarar 2026 Zuwa 2030

July 16, 2026
Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

Nazari Game Da Damammakin Da Sin Ta Samar Cikin Rahoton Ci Gaban Tattalin Arzikinta Na Rabin Farkon Shekara

July 16, 2026
Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

Gwamna Bala Ya Rushe Kwamitin Gudanarwar Wikki Tourists Bayan Rashin Nasararta A Gasar NPFL

July 16, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.