ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Ayyukan 2025

by Muhammad Bashir
5 months ago

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan Dokar Kasafin Kuɗi ta shekarar 2026, wadda ta tanadi jimillar kashe kuɗi na Naira tiriliyan 68.32.Haka kuma, ya amince da ƙudurin da ya tsawaita lokacin aiwatar da kasafin kuɗin 2025 daga ranar 31 ga Maris 2026, zuwa 30 ga Yunin 2026.

A cewar sanarwar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, kasafin kuɗin na Naira tiriliyan 68.32 ya ware Naira tiriliyan 4.799 domin wasu ayyukan da suka jibanci al’amuran doka, sannan Naira tiriliyan 15.8 domin biyan bashin gwamnati.

  • Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
  • Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna
  • Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Haka kuma, an ware Naira tiriliyan 15.4 domin kuɗaɗen gudanarwa inda Naira tiriliyan 32.2 kuma aka keɓe wa Asusun Ci Gaba domin ayyukan ci gaba.Bugu da ƙari, Shugaban Ƙasar ya sanya hannu kan dokar gyaran kasafin kuɗi ta 2026, wadda ta tsawaita lokacin aiwatar da ɓangaren ayyukan ci gaba na kasafin 2025 daga 31 ga Maris 2026, zuwa 30 ga Yuni, 2026.

ADVERTISEMENT

Onanuga ya ce tsawaita aiwatar da kasafin zai tabbatar da cikakken amfani da kuɗaɗen da aka ware, musamman ga manyan ayyukan more rayuwa da ci gaba da suka kusa kammaluwa a faɗin ƙasarnanYa ƙara da cewa hakan zai bai wa Ma’aikatu da Hukumomi damar kammala ayyukan da suke yi da inganta yawan kammala ayyuka, tare da tabbatar da ingantaccen amfani da kuɗin jama’a.

Da zarar dokar kasafin kuɗin 2026 ta fara aiki daga ranar 1 ga Afrilu, Gwamnatin Tarayya za ta fara cikakken aiwatar da ita bisa tsarin shirin Renewed Hope.Shugaba Tinubu ya umarci ma’aikatu da hukumomi da su tabbatar da amfani da kuɗaɗe cikin tsari da gaskiya da inganci, tare da mai da hankali wajen kammala ayyuka a kan lokaci.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

Ya kuma yaba wa shugabanci da ‘yan Majalisar Tarayya bisa jajircewa da haɗin kai da kishin ƙasa wajen duba da amincewa da kasafin cikin gaggawa.A ƙarshe, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya aniyarsa ta zurfafa gyare-gyaren tattalin arziki da ƙara hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, da fifita zuba jari da za su bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da kuma ƙarfafa tsarin tallafin jin ƙai ga al’umma.

Muhammad Bashir
+ postsBio
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    ADC Na Zawarcin Gawuna Domin Ya Yi Wa Jam’iyyar Takarar Gwamnan Kano A 2027
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Gwamna Inuwa Yahaya Ya Tsaya Takarar Sanatan Gombe Ta Arewa
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Gwamna Yusuf Ya Amince Da Fitar Da Biliyan 21.2 Don Gyaran Manyan Matatun Ruwa Na Kano
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Tinubu Zai Kammala Shekaru Takwas A Mulki Kamar Yadda Buhari Ya Yi – Onanuga

MASU ALAKA

'Yan Bindiga
Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina
Labarai

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare
Labarai

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Next Post
Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Ayyukan 2025

Ku Kula Da Kyawawan Ɗabi’u, Su Ne Waɗanda Annabi SAW Ya Kira Duk Halitta A Kansu

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.