ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Yusuf Ya Amince Da Fitar Da Biliyan 21.2 Don Gyaran Manyan Matatun Ruwa Na Kano

by Muhammad Bashir and Sulaiman
4 months ago
Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kashe Naira biliyan 21.29 domin gyara da farfaɗo da manyan cibiyoyin samar da ruwa a faɗin jihar, a wani mataki na magance matsalar ƙarancin ruwa da ta daɗe tana addabar al’umma.

Ma’aikatar Albarkatun Ruwa ta jihar ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da Mukaddashin Kwamishina, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya fitar a ranar 30 ga Afrilu, 2026.A cewar sanarwar, aikin zai mayar da hankali ne kan manyan cibiyoyin Tamburawa, Challawa da kuma Goron Dutse, waɗanda tabarbarewar aikinsu ta janyo ƙarancin ruwa a sassa da dama na jihar.

Sanarwar ta ce daga cikin ayyukan da za a gudanar akwai gyaran matatar ruwan Tamburawa da kuma dawo da famfon tace ruwa kan kuɗin Naira biliyan 9.9. Haka kuma za a gyara famfon tace ruwa na Challawa da matatar ruwan, tare da farfaɗo da tankunan ruwan Goron Dutse kan kuɗin Naira biliyan 11.39.

ADVERTISEMENT

Dakta Hashim ya bayyana wannan mataki a matsayin ɗaya daga cikin manyan jarin da aka taɓa zuba a ɓangaren ruwa a ‘yan shekarun nan, yana mai cewa matakin ya zama dole cikin gaggawa.

Ya ce matatar ruwan Tamburawa, wadda aka gina domin samar da lita miliyan 150 na ruwa a rana, a halin yanzu tana aiki ne da kusan kashi 27 cikin ɗari kacal, sakamakon lalacewar da ambaliya ta haddasa tun daga shekarar 2022.Haka zalika, matatar Challawa wadda ke da ƙarfin samar da lita miliyan 220 a rana, tana aiki ne da ƙasa da kashi 30 cikin ɗari.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

A cewarsa, a haɗe, matatun biyu an gina su domin samar da lita miliyan 370 na ruwa a kullum, amma a yanzu suna samar da ƙasa da hakan, lamarin da ke haifar da ƙarancin ruwa a sassa da dama na jihar.

Bugu da ƙari, tankunan ruwan Goron Dutse, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen rarraba ruwa a yawancin yankunan birnin Kano, sun daina aiki gaba ɗaya sakamakon lalata muhimman kayan aikinsu.

“Waɗannan matsaloli ne da ke bayyana girman ƙalubalen da muke fuskanta. Amma kuma su ne ginshiƙin shirin da muka ɗauka domin magance matsalar gaba ɗaya,” in ji Dakta Hashim.

Ya tabbatar wa al’umma cewa ayyukan da aka amince da su za su ƙara yawan samar da ruwa, su inganta rarrabawa, tare da daidaita wadatar ruwa a faɗin Kano.Duk da sanin hali da wahalhalun da jama’a ke fuskanta, kwamishinan ya jaddada cewa gwamnan jihar na da ƙudurin warware matsalar ta zama tarihi.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf na da niyyar magance wannan matsala ta hanyar da za ta ɗore, kuma muna da yakinin cewa da waɗannan matakai, za a rage matsalar ƙarancin ruwa a Kano har ta kau gaba ɗaya,” in ji shi.

Haka kuma ya buƙaci haɗin kan jama’a wajen kare kayan aikin ruwa daga lalata su, yana mai cewa hakan na daga cikin abubuwan da ke haddasa yawaitar matsalolin samar da ruwa.

Gwamnatin Jihar Kano ta kuma sake jaddada aniyarta na samar da ingantaccen ruwan sha ga al’umma tare da inganta rayuwarsu ta hanyar ci gaba da zuba jari a muhimman ayyukan more rayuwa.

Yusuf
Muhammad Bashir
+ posts Bio
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    ADC Na Zawarcin Gawuna Domin Ya Yi Wa Jam’iyyar Takarar Gwamnan Kano A 2027
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Gwamna Inuwa Yahaya Ya Tsaya Takarar Sanatan Gombe Ta Arewa
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Na Naira Tiriliyan 68.32, Ya Tsawaita Ayyukan 2025
  • Muhammad Bashir
    https://hausa.leadership.ng/author/muhammad-bashir/
    Tinubu Zai Kammala Shekaru Takwas A Mulki Kamar Yadda Buhari Ya Yi – Onanuga
Yusuf
Sulaiman
+ posts Bio
  • Sulaiman
    Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara
  • Sulaiman
    Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
  • Sulaiman
    Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
  • Sulaiman
    ‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue
Manyan Labarai

Ɓata-gari Sun Kai Wa Ayarin Peter Obi Hari A Benue

September 8, 2026
Next Post
Kar Ku Tayar Da Hankulanku, Mun Samo Fetur Fiye Da Lita Biliyan 1.5 – NNPCL

Ɓatan Dabon Naira Tiriliyan 210 A NNPCL: Kyari, Ajia da Wunti Sun Shirya Bayar Da Shaida

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.