ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tsohon Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Olawepo-Hashim Ya Nemi A Gaggauta Ceto ‘Yan Makarantar Da Aka Sace A Borno Da Ogbomosho

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi Allah-wadai da sace ɗaliban makarantar firamare da ƙaramar sakandare ta Mussa da ke Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno, tare da hare-haren da aka kai makarantu da dama a Ƙaramar Hukumar Oriire ta Jihar Oyo da ke yankin Ogbomosho, yana mai bayyana lamarin a matsayin “mummunan hari kan makomar Nijeriya.”

Ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa da ƙarfi, yana mai cewa ceto yaran cikin gaggawa da tabbatar da lafiyarsu dole ne ya zama babban abin fifiko ga ƙasa baki ɗaya.

Makarantun da harin ya shafa a Jihar Oyo sun haɗa da Baptist Nursery and Primary School da ke Yawota, Community Grammar School da ke Esiele, da kuma L.A. Primary School da ke Esiele.

ADVERTISEMENT

A cikin wata sanarwa, Olawepo-Hashim ya ce kai hari ga yara masu makaranta na nuna wani sabon salo mai haɗari na ta’addanci da kuma kai hari kai tsaye ga ilimi, zaman lafiya da makomar ƙasa.

“Makarantu bai kamata su zama wuraren tsoro ba,” in ji shi, yana mai gargaɗin cewa yawaitar hare-hare kan cibiyoyin ilimi na iya ƙara yaɗa rashin tsaro har zuwa ga tsararraki masu zuwa.

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

Ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda abin ya shafa, sannan ya sake kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su ɗauki mataki cikin gaggawa domin ceto yaran lafiya.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce abubuwan da suka faru sun nuna gazawar tsarin tsaron yankunan karkara na Nijeriya, inda ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ke anfani da wuraren da gwamnati ba ta da cikakken iko, talauci da ƙarancin kasancewar gwamnati.

Da yake magana kan kashe wani kwamandan ISIS ta haɗin gwiwar jami’an Nijeriya da Amurka, Olawepo-Hashim ya yaba da nasarar soji, amma ya yi gargaɗin cewa bai kamata a dogara da irin waɗannan nasarori kaɗai ba.

“Wannan mummunan al’amari na tuna mana cewa nasarorin yaƙi kaɗai ba za su iya tabbatar da tsaron ƙasa ba,” in ji shi.

Ya yi kira da a samar da cikakken tsarin tsaron ƙasa wanda zai haɗa da ci gaba da matsin lamba ta fuskar soja, haɗin gwiwar leƙen asiri, tsaron iyakoki, faɗaɗa tsaron karkara da kuma shirye-shiryen tattalin arziki da zamantakewa.

Olawepo-Hashim ya kuma buƙaci ƙasashen duniya da su mai da hankali sosai kan tabarbarewar tsaro a Arewacin Nijeriya, yana mai cewa matsalar na da tasiri har zuwa yankunan Yammaci da Tsakiyar Afirka.

Ya soki rashin nuna damuwa mai ɗorewa daga ƙasashen duniya, musamman kan yawaitar sace yaran Afirka, yana mai gargaɗin kada duniya ta saba da irin waɗannan munanan abubuwa.

“Kada duniya ta zama mai ɗaukar irin waɗannan abubuwa a matsayin ruwan dare,” in ji shi.

Ya kuma yi gargaɗin cewa Nijeriya ba za ta iya gina makoma mai ɗorewa ba idan ana rayuwa cikin inuwa ta tsoro.

“Babu wata ƙasa da za ta bunƙasa yayin da ake farautar yaranta kuma makarantu ke cikin hari,” in ji shi.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi
Manyan Labarai

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa
Labarai

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila
Manyan Labarai

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
Next Post
‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji 7 A Harin Kwantan Ɓauna A Sakkwato

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji 7 A Harin Kwantan Ɓauna A Sakkwato

LABARAI MASU NASABA

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

Rashin Mulki Ke Firgita Atiku – Kakakin APC Na Kaduna

September 9, 2026
Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

Yaya Toure Na Dab Da Kafa Tarihi A Gasar Zakarun Turai

September 9, 2026
Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

Xi Jinping Ya Taya Kim Jong-Un Murnar Cika Shekaru 78 Da Kafuwar Koriya Ta Arewa

September 9, 2026
’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.