ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, September 10, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

‘Yan Ta’adda Sun Kashe Sojoji 7 A Harin Kwantan Ɓauna A Sakkwato

by Rabi'u Ali Indabawa
4 months ago

Wasu da ake zargin ƴan ta’addan Lakurawa ne sun kashe sojoji bakwai a wani kwanton ɓauna da suka yi a ƙauyen Runji, mai tazarar kusan kilomita 10 daga garin Illela a Ƙaramar Hukumar Illela ta Jihar Sakkwato.

Majiyoyin yankin sun ce lamarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar da ta gabata yayin da dakarun ke dawowa daga wani samame da suka kai maɓoyar Lakurawa.

Mazauna yankin sun bayyana cewa sojojin sun kai hari sansanin ƴan ta’addan ne da motocin soja guda uku, wani farmaki da ake kyautata zaton ya jawo wa ƴan bindigar asara mai yawa.

ADVERTISEMENT

Wata majiya da ta san yadda lamarin ya faru ta ce ɗaya daga cikin motocin sojojin ta samu matsalar inji yayin da suke komawa sansaninsu da ke Illela, lamarin da ya sa wasu daga cikin sojojin suka tsaya a gefen hanya domin gyara ta.

Da alama ƴan ta’addan sun tattaru tare da bibiyar sojojin domin ɗaukar fansa kan harin da aka kai musu a sansaninsu,” in ji majiyar.

LABARAI MASU NASABA

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

Ta ƙara da cewa maharan sun iso yankin ne a kan babura kusan 30, inda kowane babur ke ɗauke da mayaƙa uku masu ɗauke da muggan makamai.

“Sun tarar da sojojin a wajen da ake gyaran motar, sannan aka yi musayar wuta mai tsanani na wani lokaci,” in ji majiyar.

Sai dai wani rahoto ya ce sojoji bakwai da farar hula ɗaya ne suka rasa rayukansu a harin kwanton ɓaunar.

“Bayan sojojin sun bar motar da ta lalace, suna tafiya zuwa sansaninsu tare da taimakon wani farar hula da ya san yankin sosai, sai Lakurawa suka yi musu kwanton ɓauna suka kashe sojojin bakwai da jagoransu na farar hula,” in ji majiyar.

Wani mazaunin Illela, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce an fara tabbatar da mutuwar sojoji shida a wurin da lamarin ya faru, sannan daga baya aka gano gawar wani soja a cikin wani daji da ke kusa da wurin, wanda ya sa adadin ya kai bakwai.

“Mun ga gawarwaki bakwai a wurin, sannan aka sake gano wata gawar washegari,” in ji shi.

Majiyoyin tsaro ma sun tabbatar da harin, inda suka ce an kwashe gawarwakin sojojin da aka kashe zuwa Sakkwato.

Wani jami’in gwamnati a yankin ya kuma bayyana cewa wani babban jami’in soja mai muƙamin Laftanar a rundunar sojin Nijeriya na cikin waɗanda aka kashe a harin.

Kakakin rundunar ƴansandan Jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman, sun ƙi yin tsokaci kan lamarin.

Sai dai wani babban jami’in soja da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa sojoji shida ne suka mutu a harin.

“Eh, mun yi rashin jami’ai abin takaici a ƙarshen mako a yankin Illela. Sai dai an tura ƙarin dakarun soja cikin gaggawa zuwa yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan leƙen asiri domin gano da kuma kawar da ƴan ta’addan da suka aikata hakan.

“Kamar yadda al’adar soja ta tanada, ba za mu bayyana sunayen jarumanmu da suka rasu ba har sai an sanar da iyalansu.

“Saboda haka muna roƙon kafofin yaɗa labarai da su mutunta sirrin iyalan waɗanda abin ya shafa tare da kauce wa wallafa alƙaluman asara marasa tabbaci. Maimakon haka, ya kamata a mayar da hankali kan sadaukarwa da jajircewar dakarunmu,” in ji jami’in.

Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ƙungiya Ta Gudanar Da Zaɓen Sabbin Shugabanninta A Abuja
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Jihar Katsina Da UNICEF Sun Ceto Rayuwar Yara Ta Hanyar Samar Da Abinci Mai Gina Jiki
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Yadda Tinubu Ya Kashe Naira Biliyan 37.64 A Tafiye-tafiye
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Ta’addaci: Mutum 14,500 Sun Bace A Arewa Maso Gabas

MASU ALAKA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Tsaro

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’
Tsaro

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara
Tsaro

Sojoji Sun Kama Mai Kai Wa Ƴan Ta’adda Kayan Aiki A Zamfara

June 25, 2026
Next Post
Ƴan Takarar Gwamna A Gombe Sun Yi Watsi Da Yunƙurin Pantami Na PDP

Ƴan Takarar Gwamna A Gombe Sun Yi Watsi Da Yunƙurin Pantami Na PDP

LABARAI MASU NASABA

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

Sin Na Fatan Amurka Za Ta Dakatar Da Furta Karairayi Da Nufin Bata Mata Suna

September 9, 2026
An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

An Kashe Shahararren Mai Sharhin Siyasar Kano, Ibrahim Dan Shagamu

September 9, 2026
Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

Sin Ba Ta Taba Janyewa Wata Kasa Tsani Ba

September 9, 2026
Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

Xi Ya Aike Da Gaisuwa Albarkacin Ranar Malamai Yana Mai Kira Da A Samar Da Matasa Masu Hazaka Domin Kara Farfado Da Kasa

September 9, 2026
Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

Ku Daure Ku Sake Zaɓar Mijina A 2027 – Remi Tinubu

September 9, 2026
Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

Renon Matasa A Kan Kyakkyawar Turba Ginshiki Ne Na Gina KasaBy

September 9, 2026
Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

Bikin CIFTIS Zai Ingiza Bude Kofa A Kasar Sin

September 9, 2026
“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

“Ajin Tashar Sararin Samaniya Na Hong Kong Da Macau” Ya Kara Wa Matasa Sha’awar Kimiyya Da Karfafa Kishin Kasa

September 9, 2026
’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

’Yansanda Sun Cafke Matar Da Ta Kwara Wa Maƙociyarta Tafasasshen Ruwan Zafi A Abuja

September 9, 2026
Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

Taron Kolin Urumqi Ya Mayar Da Hankali Kan Kwarewar Shugabanci A Xinjiang Da Muhimmancinta Ga Duniya

September 9, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.